Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
ASUU: Yadda 'yan Najeriya suke tafka muhawara kan daina bai wa Malaman Jami'a albashi
'Yan Najeriya da dama na ci gaba da tafka muhawara game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na daina bai wa Malaman Jami'a albashi tsawon watanni shida da suka shafe suna yajin aiki.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce batun biyan Malaman Jami'o'i albashinsu na tsawon watannin da ba su yi aiki ba shi ne kaɗai abin da ya rage ba a cimma ba a yarjejeniyar ASUU da gwamnati.
Ya kara da cewa hakkin Malaman Jami'o'i ne su biya ɗalibai diyya saboda ɓata musu lokacin da suka yi tsawon wata shida.
Adamu Adamu ya ce ya kamata daliban da yajin aikin ya shafa su kai kungiyar kotu don neman fansa a kanzaman banzan da aka tilasta musu a gida.
Sai dai kungiyar ASUU ta ce matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na ƙin biyan su albashi zai ƙara dagula lamura ne kawai.
Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad, ya shaida wa BBC cewa "gwamnati ba da gaske take ba" a kokarin yin sulhu
Matakin dai ya ja hankalin 'yan kasar musamman dalibai wadanda suka kosa su koma makaranta.
Masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawa sun bayyana ra'ayoyi mabambanta game da matakin.
Abdulmanaf, wani dalibi da ya yi tsakani kan batun, ya ce matakin da gwamnati ta dauka ya yi daidai yana mai cewa amma ya kamata su ma a ba su diyyar taba musu lokaci.
Sai dai Zaharaddeen Kallah ya ce ministan ya kamata a dora wa alhakin yajin aiki domin kuwa shi da kansa ya kori kungiyar dalibai lokacin da ta je wurinsa domin neman sulhunta gwamnati da ASUU.
Shi ma Kabiru Farther ya ce yajin aikin ba karamin cutar da su yake yi ba a matsayinsu na 'ya'yan talakawa yana mai yin kira da bangarorin biyu su yi "hakuri" su sasanta.
Mu'azu Kabiru Ci-guminka ya bai wa dukkan bangarorin shawara inda ya ce su ciza su hura.