Zaben kasar Kenya: Matashiyar da ke jawo hankalin mutane su yi zabe - amma ita ba za ta kada kuri'a ba

    • Marubuci, Daga Dickens Olewe
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi

Diana Mwazi na daya daga cikin matasan Kenya da ke kallon zaben kasar a matsayin wata hanyar samun kudi, maimakon wata dama ta zabar mutanen da za su iya kawo sauyi a rayuwarta.

Matashiyar, 'yar shekara 20, tana da wani dan karamin tasiri a fannin siyasar Kenya da maza suka mamaye, a unguwar Kibera da ke babban birnin Nairobi, inda take zaune.

Tana neman marasa aikin yi su halarci gangamin siyasa domin a ba ta kudi - kuma tana farin cikin yin hidima ga kowace jam'iyyar siyasa.

"Ina farin-ciki game da zabukan da ke tafe saboda ina samun aiki daga 'yan siyasa da ke son nuna cewa sun samu goyon bayan jama'a," inji ta.

Tuni aka soma gudanar da yakin neman zabe gabanin zaben da za a yi a ranar 9 ga watan Agusta - an kuma lika hotunan 'yan takara a wuraren taruwar jama'a kuma an cika gari da kade-kade da ake watsawa daga manyan lasifika da aka dora a kan motocin yakin neman zabe.

Duk 'yan siyasa - tsofaffin-hannu da masu tasowa - suna kai gwauro su kai mari domin jan hankalin jama'a.

Ms Mwazi, wadda ba ta shirya yin zaɓe da kanta ba, ta ce: "Tara mutane don halartar wani taro ba aiki ba ne mai wahala domin samun matasa da ba su da aikin yi abu ne mai sauƙi."

"'Yan siyasa duk makaryata ne. A lokacin zabe suna tururuwa kamar tumaki, suna masu alkawari: 'Zan yi haka, zan ba matasa ayyukan yi.' Amma idan kuka zabe su ba su yi komai ba".

Hada taron mutane " wata hanyar cin abinci ce," in ji Ms Mwazi.

Tana saye da sayar da takalma a shafin sada zumunta na WhatsApp, kuma tana amfani a kudin don taimaka wa mahaifiyarta samun karin kudin shiga a matsayinta na ma'aikaciyar lafiya.

A lokacin yakin neman zabe, Ms Mwazi tana aiki tare da sauran masu wayar da kan jama'a kuma dangane da adadin mutanen da aka nema, za ta iya tara tsakanin mutane 40 zuwa 100.

Ms Mwazi ta ce "Ina samun shilin Kenya 500 ($ 5; £ 3) a kowane taron amma wasu 'yan siyasa suna da kyauta."

Masu halarta suna samun irin wannan adadin.

Ms Mwazi ta ce "'yan siyasa suna son abokan hamayyarsu su ga cewa suna da karin goyon baya, don haka suna daukar hotunan taron jama'a suna yada wa a shafukan sada zumunta," in ji Ms Mwazi.

Ta samu nasara wajen hada kan 'yan mata, amma ta fuskantar kalubale wurin samari.

"Maza ba abin dogaro ba ne, suna korafi a kan kudin da ake ba su," in ji ta, ta kuma kara da cewa, a wasu lokutan kungiyoyin matasa masu adawa da juna kan yi rikici idan suka hadu da juna a yakin neman zabe

A kasar da akalla kashi 70 cikin dari na al'ummar kasar masu shekaru kasa da 35 ne, tabbatar da cewa matasa sun kada kuri'a a rumfunan zabe abu ne mai matukar muhimmanci ga wadanda suka tsaya takara a zabukan shida da ake gudanarwa a lokaci guda, wadanda suka hada da na shugaban kasa, 'yan majalisa da kuma shugabannin kananan hukumomi.

'Yan takara suna kashe miliyoyin daloli a kan kayan yakin neman zabe, kayan aiki da kuma sadarwa, gami da daukar masu tasiri a kafafen sada zumunta don fitar da ingantattun mukamai.

Dole ne kuma su biya bukatun masu kada kuri'a wadanda ke cin gajiyar burin 'yan siyasa na yin nasara - 'yan siyasar Kenya na cikin 'yan siyasa da suka fi karbar albashi mai tsoka a duniya.

An tsara tsarin siyasar kasar ne domin tabbatar da cewa wadanda suka fi kashe kudi su ne za a zaba, in ji fitaccen dan fafutuka, Boniface Mwangi, wanda bai yi nasara a zaben dan majalisa ta 2017 ba.

"Daya daga cikin yan takara ya kashe kusan dala miliyan biyu (£1.5m) don samun kujera a majalisar dokoki," in ji shi. "Yana da matukar wahala dan takara talaka ya yi nasara a zabe saboda talaka ba ya zaben talaka - talakawa na bukatar a karfafa musu gwiwa domin su zabe ka."

Mista Mwangi, wanda ke da mabiya sama da miliyan biyu a shafukansa na sada zumunta, yana samun korafe-korafe da dama daga matasan Kenya, ciki har da neman aiki.

Ya ce hakan ya nuna gazawar 'yan siyasa wajen samar da ayyukan yi, ya kuma kara da cewa masu kada kuri'a sun zama masu kwadayi- suna kada kuri'a ga duk wanda ya biya su.

"Wasu daga cikin manyan 'yan siyasa a kasar nan ba su da farin jini saboda su shugabanni ne nagari, suna da farin jini saboda suna ba da kudi sosai, masu kada kuri'a sun yanke shawarar cewa ' kuri'ar mu na sayarwa ne' don haka ya zama ciniki," Mr. Mwangi ya ce.

Ya kara da cewa "A tsarin dimokuradiyya mai aiki, mutanen da ka zaba suna yi maka aiki. A Kenya masu zabe suna yi wa 'yan siyasa aiki."

Kusa da gidan dutse mai daki ɗaya inda Ms Mwazi take zaune tare da mahaifiyarta da kannenta biyu, akwai jerin gidaje da aka gina da karfe. Wata ƙunƙunciyar hanyar ƙazanta ta raba su kuma wuri ne mai ɗimbin yawan jama'a.

A can, na hadu da James Mogaka ko "Jimmy Lawyer".

Yana gyran wani rami da ya toshe, da ledodi da kwalabe da sauran sharar gida.

Ana kiransa moniker nasa, saboda ya karanta aikin lauya. Amma ya kasa samun aiki, yana yin aikin hannu don samun kudin biyan bukatunsa na yau da kullum, da kuma gabatarwa a shirye-shiryen talabijin na gida.

Ba kamar Ms Mwazi ba, dan shekaru 30 na shirin kada kuri'a ga dan takarar da yake ganin zai kawo sauyi.

Sai dai ya ce da yawa daga cikin matasa suna da wuya su tsaya kan hukuncin da aka yanke musu, kuma ana tilasta musu sayar da kuri'unsu don samun "kudi da za su ci abinci ".

"Masu kada kuri'a sun san cewa ko da ba su karbi kudi daga hannun 'yan siyasa ba, wani zai yi, kuma matsalolin da suke fuskanta ba sauya ba " in ji shi.

Kasar Kenya na fama da matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa, a cewar Jacqueline Mugo, babbar darektar kungiyar masu daukan ma'aikata ta Kenya.

"Matasa da suka fusata da rashin haƙuri matsala ce ta ƙasa… Idan kuna da matasa waɗanda ba za su iya samun abin dogaro da kansu ba kuma iyayensu suna ƙara kasa ciyar da su, wannan babbar matsalace ," in ji ta.

Ms Mugo ta ce "Idan aka kalli shekarun da suka kai kimanin shekaru 16 zuwa 35, to adadin rashin aikin yi zai iya kai kashi 40%, don haka abubuwa sun yi muni amma ba na jin zai iya yin muni fiye da yadda yake," in ji Ms Mugo. ta kara da cewa ya kamata matasa su ci gaba da harkokin siyasa domin a samu sauyi.

Ms Mwazi, wacce ke fatan yin nazarin fasahar dafa abinci wata rana, ba ta gamsu ba.

Nan da makonni masu zuwa za ta ci gaba da yin hobbasa daga wani taro zuwa na gaba don samun abin dogaro da kai, ba ta tsammanin jin ta bakin 'yan siyasa da zarar an kammala zabe.

"Yawancinsu ba sa zama a nan," in ji ta.