An rushe gidajen Musulmai a Indiya bayan zanga-zangar adawa da ɓatanci ga Annabi

Hukumomi a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya sun rushe gidajen wasu Musulmai da ake zarginsu da alaƙa da jerin zanga-zangar addini da aka yi wadanda suka rikiɗe zuwa tarzoma.

Kalaman da wasu manyan jami'an jam'iyya mai mulki ta BJP suka yi a kan Annabi Muhammad ne suka harzuƙa mutane tare da jawo zanga-zangar.

Sai dai zanga-zangar ta rikiɗe zuwa rikici a wasu jihohin inda mutane suka lalata kayayyaki.

An kama fiye da mutum 300 a jihar Uttar Pradesh.

Hukumomin jihar sun rushe gidajen wasu Musulmai uku a cikin ƙarshen mako, suna zarginsu da cewa ba bisa ƙa'ida aka gina gidajen ba - zargin da masu gidajen suka musanta.

Rushe gidajen ya jawo tofin Allah-tsine daga shugabannin jam'iyyar hamayya, wadanda suka zargin gwamnatin jihar - wacce babban minista Yogi Adityanath ke jagoranta - da ƙoƙarin kai wa al'ummar Musulmai da suke tsiraru hari.

Masu suka sun ce bambancin addini na ƙaruwa a Indiya tun shekarar 2014, a lokacin da jam'iyyar mabiya addinin Hindu ta BJP ta hau mulki.

Tun lokacin ake samun ƙaruwar kai wa Musulmai hare-hare a shekarun baya-bayan nan.

Wani saƙon Tuwita da mai bai wa Mr Adityanath shawara kan yaɗa labarail, Mrityunjay Kumar ya wallafa ya sake jawo tashin hankali.

Ya wallafa wani hoto da ke nuna buldoza tana rushe wani gini, yana mai cewa: "Mutane marasa kan gado, kowace Juma'a dai Asabar ke biyo bayanta."

Biyu daga cikin gidajen mallakin wasu mutane ne da ake zarginsu da yin jifa da duwatsu bayan Sallar Juma'a.

Gida na ukun kuma na wani ɗan siyasa ne mai suna Javed Ahmed, wanda ake zarginsa da kitsa zanga-zangar.

Ƴarsa Afreen Fatima fitacciyar Musulma ce mai rajin kare hakkin Musulmai da ta sha jagorantar zanga-zangar adawa da dokar zama ɗan ƙasa mai cike da ce-ce-ku-ce.

Wani tsohon alkalin alkalai na babbar kotun Allahabad ya shaida wa jaridar The Indian Express cewa rushe gidan Mr Ahmed ba ya bisa kan ƙa'ida.

"Ko da ma a ce kuna zaton an gina gidan ba bisa ƙa'ida ba, wanda mafi yawan gidaje a Indiya haka suke, ai bai kamata a rushe gidan mutane a ranar Lahadi ba lokacin da suke cikin suna hutawa," a cewar tsohon alkalin alkalan Govind Mathur.

Wani jami'i daga hukumar tsara birane - wacce ta rushe gidan Mista Ahmed - ya ce tun a watan Mayu aka aike masa da sanarwar yin hakan, inda hukumar ta nemi ya bayyana agabanta.

Amma Fatima ƴar Mista Ahmed ta ƙaryata hakan, inda ta ce ba su san komai kan zanven ba sai ranar Asabar aka sanar musu.

Wata ƙungiyar lauyoyi ma ta rubuta wasiƙa ga babbar kotu, tana mai cewa rushe gidan ba ya kan ƙa'ida.

Ba wannan ne karo na farko da ake zargin jihar Uttar Pradesh da sauran jihohin da jam'iyyar BJP ke mulki da rushe gidajen mutane ba, musamman bayan yin duk wata zanga-zanga ko rikicin ƙabilanci.

A halin yanzu dai, ce-ce-ku-cen da kalaman shugabannin BJP suka jawo har yanzu bai lafa ba kuma babu alamar lafawarsa.