Masu neman mafaka a Birtaniya sun yi yajin cin abinci saboda shirin kai su Rwanda

    • Marubuci, Mohamed Shalaby and Emir Nader
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic

Masu neman mafaka a wani wurin tsare 'yan ci-rani a Birtaniya sun ce sun shiga yajin aikin cin abinci bayan an faɗa musu cewa za a kai su Rwanda.

Masu neman mafaka 17 da ke sansanin tsare 'yan ci-rani a kusa da filin Jirgin Sama na Gatwick, Sussex sun shaida wa BBC irin halin matsi da ƙunci da tsararrun suka shiga.

A watan Afrilu ne gwamnati ta sanar da shirinta na tasa ƙeyar masu neman mafaka a Birtaniya zuwa Rwanda.

Amma Ma'aikatar Cikin Gida ta ce ta ɗauki walwalar mutanen da "matuƙar muhimmanci".

Wani kundin bayanai mai kwanan watan 1 ga Yuni ya bayyana wani mai neman mafaka a Brooke House da za a kai shi Kigali babban birnin Rwanda. Kundin ya ce ba shi da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Sakatariyar Harkokin Cikin Gida Priti Patel ta ce jirgin farko da zai kwashe mutanen da suka shiga Birtaniya ta ɓarauniyar hanya zuwa Kigali zai tashi a ranar 14 ga watan Yuni, ƙarin mako ɗaya kan abin da aka tsara tun farko.

Sakamakon ƙaddamar da Dokar Zama Ɗan Ƙasa da Iyakoki a watan Afrilu, gwamnati za ta kai mutane zuwa "matalauciyar ƙasa mai zaman lafiya" - Rwanda - bisa dalilan shiga Birtaniya ta hanyoyin da suka saɓa wa doka, kamar tsallakawa ta Kogin Ingila a jirgin ruwa daga Faransa.

Matakin kwashe masu neman mafakar zuwa tafiyar mil 4,500 a Rwanda wani ɓangare ne na yarjejeniyar dala miliyan 151 da Birtaniya ta ƙulla da ƙasar da ke tsakiyar nahiyar Afirka.

Da yake magana da BBC, ya ce yana cikin ayarin mutum 17 da suka gama yajin aikin cin abinci na kwana biyar a yammacin Laraba bayan masu gadi sun daina ba su sikari don su dinga haɗawa da ruwan sha saboda ba sa cin abinci.

Ali wanda ya ce yana da dangi a Birtaniya, ya faɗa wa BBC cewa haɗuwarsa ta ƙarshe da jami'an hukumar shige da fice shi ne game da dakatar da yajin aikin cin abinci. "Abin da suka ce min shi ne 'ci abinci saboda ka hau jirgi cikin ƙoshin lafiya'."

Wasu daga cikin masu yajin aikin sun ƙunshi 'yan ƙasar Masar, waɗanda aka tsara kaiwa Rwanda. Wani rukunin ya samu sanarwar za a kwashe su a ranar Laraba, 14 ga wata.

Waɗanda aka tsare sun ce masu gadi sun hana su amfani da wayoyinsu masu kyamara, inda suka ƙwace su kuma suka ba su marasa layukan intanet.

BBC ta yi nasarar samun sanarwar da ta ba da bayanan kwashe su. Wasiƙar mai shafi fiye da 40, an rubuta ta ne da Ingilishi kaɗai. Sai dai wani ɓangare ya ce an samar da tafinta da zai dinga yi wa masu neman mafaka bayani. Kundin ya yi ta maimaita kuskure a sunan mutumin da za a kora zuwa Rwanda.

Masu neman mafaka biyu daban-daban sun nemi wakilinmu ya yi musu ƙarin bayani game da kundin, wanda ke buƙatar su saka hannu, saboda sun kasa fahimtar turancin.

Ma'aikatar ba ta tabbatar da adadin mutanen da aka sanar wa kwashe su ba. Sai dai gidauniyar Care4Calais ta yi ƙiyasin an gargaɗi mutum kusan 100 da suka isa ƙasar a watan da ya gabata cewa za a fitar da su daga Birtaniya.

Care4Calais ta gano tare da ba wa 60 daga cikinsu taimako.

Wani ɗan Syria da ake neman sa ƙasarsu don ya gudanar da aikin soja, ya faɗa wa BBC cewa a shirye yake "ya mutu, amma ba zai je Rwanda ba".

Ya ce: "Lokacin da na samu labarin za a tasa ƙeyarmu zuwa Rwanda kuma za a ba mu izinin zama na shekara biyar a can sai na fara dukan kaina."

Game da yajin cin abinci a Brook House, wani kakakin ma'aikatar ya ce: "Lafiya da walwalar tsararru na da muhimmanci sosai.

"Muna ɗaukar dukkan matakai don hana mutane su zalinci kan su ko kuma kashe kan su, ciki har da samar da tawagar ma'aikatan lafiya a kowane sansanin tsare mutane."

Wani ɗan ƙasar Masar ya fada wa BBC cewa "dole ce ta sa ni barin ƙasa ta saboda faɗan da ake yi a cikin danginmu. Ina da matsalar ƙwaƙwalwa sakamakon abubuwan da na gani a Libya kafin na ƙaraso nan".

Game da fara kwashe mutanen a tsakiyar Yuni, Priti Patel ta ce: "Mun san cewa za a yi yunƙurin kawo ayyukan kwashe mutane tsaiko; ba zan yi ƙasa a gwiwa ba kuma zan ƙara ƙaimi wajen samar wa mutanen Birtaniya abin da suka nema."

Sai dai Steven Galliver-Andrew, wani lauya ƙwararre kan dokokin shige da fice, ya faɗa wa BBC cewa gwamnati ba za ta iya fara kwashe mutane daga 14 ga wata ba kamar yadda aka tsara.

"Da alama dokar da ta ba wa gwamnati damar yin hakan ba za ta fara aiki ba har sai 28 ga watan Yunin 2022," in ji shi.

"Za a iya kai ƙarar abubuwan da suke yi - sun kuma san hakan tare da tsammanin hakan."