PDP na gudanar da babban taron fitar da dan takarar shugaban kasa a Najeriya

A ranar Asabar din nan babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya, PDP, za ta gudanar da babban taronta na kasa, a babban birnin tarayyar kasar, Abuja, don zaben wanda zai mata takarar shugaban kasa a 2023, yayin da APC mai mulki ta dage nata zaben.

Mutum 14 ne suke neman takarar, wadanda suka fito daga bangarori daban-daban na kasar wadda ita ce mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Jam`iyyar ta ce ta kammala shirin karbar wakilanta, wadanda aka fi sani da daliget, daga sassan kasar, wadanda za su zaba mata dantakarar shugaban kasa daga cikin masu neman a ba su tutar.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri wanda tsohon sakataren jam`iyyar ne na kasa, na cikin `yan kwamitin shirya zaben fidda gwanin, ya bayyana wa BBC irin shirin da suka yi.

''Tsare-tsare sun kankama, za mu yi zaben fid da shugaban kasa in Allah ya yarda. Masu jefa kuri'a wadnda ake ce ma daliget mutum 811. Wadanda su za su jefa kuri'a su zabi dan takarar shugaban kasa,'' in ji shi.

Ya ce idan har komai ya tafi yadda suka tsara, suna sa ran ranar Lahadi da safe za a san wanda zai ja ragamar jam'iyyar ta PDP idan an zo zaben shugaban kasa na 2023.

Da farko dai mutum goma sha bakwai ne suka nuna sha`awar neman takarar, amma kuma sai biyu daga ciki ba su tsallake tantancewa ba, yayin da na ukunsu, tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya janye, kana ya fice daga jm`iyyar, ya koma Labour Party.

`Yan takarar 14 sun hada da gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed, da na Rivers, Nyesom Wike da na Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da na Akwa-Ibom, Udom Emmanuel da tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da Mohammed Hayatu-Deen.

Sai tsoffin shugabannin majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da Sanata Pius AnyimPius da Dele Momodu, da Sam Ohabunwa da Charles Ugwu da Chikwendu Kalu, da kuma mace daya tilo Tariela Oliver.

Jam`iyyar PDP din ta bar takarar kujerar shugaban kasar a bude ga dukkan shiyyoyin kasar, wanda saboda haka ne masana siyasa ke cewa kallo ya koma kan yankin da zai samu takarar shugaban kasa da tutar tata.

Mallam Kabiru Sa'id Sufi na kwalejin share fagen shiga jami`a ta Jihar Kano, CAS, ya bayyana yadda yake kallon lamarin:

''Duk idanu yanzu za su koma kan jam'iyyar PDP a ga wane dan takara za ta fitar, kuma musamman ma a ga daga wane yanki ya fito, daga Kudu ne ko daga Arewa ne, shi ne yanzu abin da kowa yake jira ya gani.'' in ji shi.

''Wadanda suke jira din sun hadar da jam'iyyun da suke hamayya da it PDP din.''

Ya kara da cewa, ''Kowanne yanzu yana jira ya ga, wane bangare ne zai dauki wannan tikiti na jam'iyyar PDP. Idan Kudu ne suka dauka to kuma wnnan ne ai haska wa ita kuma jam'iyyar hamayya da sauran ma jam'iyyun da ba su fitar da 'yan takararsu ba, domin samun dama.''

Rahotanni dai sun nuna cewa jiga-jigan jam`iyyar PDPn sun kashe dare suna tattaunawa da masu neman takarar da nufin cimma maslaha don saukaka zaben, amma idan ta gagara, to ba makawa sai an kada kuri`a.

APC ta dage lokacin zaben dan takararta na shugaban kasa

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriyar ita kuwa ta sanar da dage lokacin gudanar da zaben fitar da gwanin da ai yi mata takarar shugaban kasar, wanda a da ta tsara za ta yi daga ranar Lahadi 29 ga watan Mayu zuwa Litinin 30 ga watan na 2022.

A wata sanarwa da Sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar Barista Felix Morka, ya fitar ranar Asabar da daddare, ya ce a yanzu za su gudanar da zaben ne a tsakanin ranakun shida d bakwai d kuma takwas ga watan Yuni na 2022.

Hukumar Zabe ta kara wa'adin zaben fid da gwani

A halin da ake ciki kuma hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta kara tsawon wa'adin lokacin da jam'iyyun siyasa za su gudanar da zabukan fid da gwani na 'yan takararsu, da kwana shida, daga ranar hudu zuwa tara ga watan Yuni mai zuwa.

Hakan dai ya biyo bayan bukatar da wasu jam'iyyun siyasar kasar suka gabatar wa hukumar zaben, ta neman kara wa'adin da kwana 37 zuwa 60, don su sami sukunin kammala zabukan fid da gwani, su kuma gabatar wa hukumar sunayen 'yan takaran da suka tsayar, abin da INEC din ta ki amincewa da shi a lokacin, sai kuma a ranar Juma'a ta fitar da sanarwar kara lokacin da kwana shida.