Nnamdi Kanu: Ziyarar da Soludu ya kai wa jagoron IPOB ta janyo ce-ce-ku-ce

Kanu

Asalin hoton, Charles Soludu Twitter

Bayanan hoto, Kanu yana kurkuku bisa zargins da hannu a ta'addanci amma ya musanta
Lokacin karatu: Minti 3

An samu mabambamtan ra'ayoyi a tsakanin 'yan Najeriya sakamakon ziyarar da gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya kai wa madugun kungiyar 'yan aware na IPOB, Nnamdi Kanu a ranar Juma'ar da ta gabata.

Gwamnan Anambra ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi cewa ya kai wa jagoran IPOB ziyara "a wani mataki na lalubo bakin zaren samar da zaman lafiya a yankin Kudu maso gabashin kasar".

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Batun ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan Najeriya, inda Soludu ya kasance cikin jerin batutuwan da aka fi tattaunawa a Twitter tun daga Asabar zuwa Lahadi.

A martanin da suka mayar wasu 'yan Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu game da ziyarar a yayin da wasu kuma suka ce mataki ne mai mahimmanci domin samar da zaman lafiya.

A shafin @XerxesEmperor ya ce "karamma Nnamdi Kanu babban kuskure ne, za ka yi dana sani a nan gaba. Duk da manufarka na da kyau amma matakin rashin tunani ne".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Ita kuwa mai shafin @Nkemchor_ cewa ta yi "Ka yi daidai ranka ya dade. Sauran gwamnoni kudu maso gabas ya kamata su yi koyi da kai game da yadda ake shugabanci. Sasantawa shi ne muhimmin matakin samar da zaman lafiya".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Sai dai mai shafin @DaveTorty ya saka ayar tambaya inda ya ce "Me ya sa gwamna mai ci zai ziyarci dan ta'adda? Wannan babu tunani a ciki. Mutumin nan (Kanu) na haddasa rashin tsaro a kudu maso gabas tare da korar masu zuba jari."

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Mai shafin @ayogu_johnson cewa ya yi " Soludu ka daina wahalar da kanka munsan dabararku".

Short presentational grey line

A cikin 'yan shekarunan yankin kudu maso gabashin Najeriya na fuskantar matsalar tsaro a yayin da ake zargin 'yan awaren ipob da kai hare-hare kan jami'an tsaro da kuma farar hula.

A karshen watan Yuni ne gwamnatin Najeriya ta sanar da kama jagoran na IPOB Mr Kanu, wanda ya tsere daga kasar.

Gwamnatin Najeriya na tuhumarsa da laifuka 11, ciki har da cin amanar ƙasa da ta'addanci, da mallakar haramtattun makamai, da kuma kokarin tunzura jama'a don haifar da yamutsi.

Tun a 2017 ne gwamnatin Najeriya ta ayyana IPOB matsayin ta 'yan ta'adda saboda kashe-kashen da hukumomi ke zargin ta da aikatawa a jihohin kudu maso gabashin ƙasar da suka haɗa da Anambra, da Abia, da Ebonyi, da Imo, da Enugu.

Lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin Najeriya ta ce IPOB ce ta kashe wasu sojojinta biyu mace da namiji da ke shirin yin aure a Jihar Imo da ke yankin na kudu maso gabas. Sai dai ƙungiyar ta musanta zargin.

Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da Nnamdi Kanu shugaban ƙungiyar, wanda ke da shaidar zama ɗan ƙasar Birtaniya a gaban kotu, tana mai zargin sa da haddasa tashin hankali da raba kan 'yan ƙasa.

A makon da ya gabata gwamnatin Birtaniya ta cire mambobin IPOB daga jerin waɗanda za a iya bai wa mafaka a ƙasar saboda zargin su da aikata ta'addanci a Najeriya.

Ofishin harkokin cikin gida na Birtaniya ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon gwamnatin Najeriya ta ayyana su a matsayin ƴan ta'addanci saboda hare-haren da mambobinta ke kai wa kan jami'an tsaro da fararen hula.

'Yan Ipob sun ce jihohin Anambra, da Abia, da Enugu, da Imo, da Ebonyi, za su iya kafa kasa mai cin gashin kan ta
Bayanan hoto, Kungiyar Ipobta yi kirarin jihohin da ke jikin taswirar nan sun isa kafa kasar Biafra

Yadda yankin Biafra yake:

  • A shekarar 1967 tsohon soja wato Odumegwu-Ojukwu ya ayyana kasar Biafra.
  • Ya kuma jagoranci yawancin sojoji 'yan kabilar Ibo a yakin da aka kwashe shekaru uku ana yi, da kuma ya zo karshe a shekarar 1970.
  • Fiye da mutane miliyan daya ne suka rasa rayukansu, yawancinsu saboda tsananin yunwa a lokacin.
  • Shekaru da dama, bayan juyin juya halin Biafra, wasu kungiyoyi sukai ta daukar hankalin matasa da nufin taimaka mu su cimma nasara.
  • Sun yi zargin cewa gwamnatin Najeriya ta wancan lokacin ba ta damu da zuba jari a yankinsu ba.
  • Sai dai gwamnati ta ce, korafin na su ai ba wai akan kudu maso gabashin kasar su ke yi ba.