Sheikh Khalifa bin Zayed: Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ya rasu

Sheikh Khalifa bin Zayed

Asalin hoton, Reuters

Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, Sheikh Khalifa bin Zayed ya rasu a ranar Juma'a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar WAM ya ruwaito.

WAM ya ce shugaban ya rasu ne yana da shekara 73 a duniya.

Tuni kasar ta sanar da makokin kwana 40 inda za a sassauta tutar kasar tun daga ranar Juma'ar 13 ga watan Mayun 2022.

Sannan ta dakatar da aiki a ma'aikatu da hukumomin ƙasar har tsawon kwana uku.

Sheikh Khalifa shi ne sarkin Masarautar Abu Dhabi kuma shugaban ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

A ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar, mataimakin shugaban ƙasa kuma firimiya Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum, Sarkin Dubai ne zai zama muƙaddashin shugaban ƙasa.

Amma majalisar tarayya, wadda ta ƙunshi shugabannin masarautun ƙasar bakwai za ta yi wani taro a cikin kwana 30 masu zuwa don zaɓar sabon shugaba.

An haifi Sheikh Khalifa a shekarar 1948, kuma ba a faye ganinsa a bainar jama'a ba tun shekarar 2014 da ya gamu da ciwon zuciya.

Tun a lokacin ƙaninsa da suke uba ɗaya kuma yarima mai jiran gadon masarautar Abu Dhabi Mohammed bin Zayed, da aka fi sani da MbZ, wanda babban abokin Amurka ne, shi ke tafiyar da al'amuran ƙasar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na tuwita MbZ ya yabi marigayin shugaban a matsayin mai kirki da hangen nesa.

Tuni aka fara miƙa saƙon ta'aziyya daga ƙasashen Larabawa da suka haɗa da Sarkin Bahrain da shugaban ƙasar Masar da Firai ministan Iraƙi.

Sheikh Khalifa ya zama shugaban ƙasar UAE mai ɗumbin arziki ne a shekarar 2004. Ana sa ran Yarima Sheikh Mohammed ne zai gaji sarautarsa ta Sarkin Abu Dhabi.

Tun a shekarar 1971 ne masarautar Abu Dhabi ke riƙe da mulkin shugabancin ƙasar, bayan da mahaifin Sheikh Khalifa wato Sheikh Zayed bin Sultan al-Nahyan ya ƙirƙiri ƙasar.