Yadda tsananin zafi ke naƙasa kananan sana'o'i a Indiya

A daidai lokacin da ake ci gaba da zabga zafi a Indiya, talakawan ƙasar da dama na cikin wani hali. Wakiliyar BBC Ayushi Shah ta haɗa wa BBC rahoto daga Mumbai.

Sulachna Yevale mai sayar da kayan lambu, tana yawan zuba ruwa kan kayan lambunta da suka haɗa da lemon tsami da alayahu da take sawowa daga kasuwa domin guje wa bushewarsu.

Sai dai duka waɗannan abubuwan ba su taimakawa.

Tsananin zafin ya ja da dama daga cikin kayayyakin sun lalace wanda hakan ya sa ba za a iya sayar da su ba.

Duk da cewa ta shafe shekaru da dama tana sayar da kayan lambu a wuri ɗaya, Ms Yevale ta bayyana cewa wannan ne karo na farko da ta yi asarar kayayyakinta da yawa - na kusan rupee 70, kusan dala ɗaya kenan - wanda wannan kuɗi ne mai yawa ga mutumin da ke rayuwa wanda abin da yake samu a matsayin riba a duk rana bai wuce rupee 800 ba.

A daidai lokacin ribarta ke raguwa, ta damu matuƙa kan abin da zai faru a nan gaba. Ta dogara ne da sayar da kayan lambu domin ciyar da iyalinta, ciki har da matar ɗanta wanda ya rasu da kuma jikarta.

"Ina jin ba zan iya yin komai ba," in ji ta, a lokacin da take kuka.

Zafi mai tsanani a halin yanzu ya takura wa rayuwar jama'a da dama a India waɗanda ke ta ƙoƙarin rayuwa a cikin zafin - wanda shi ne zafi mafi tsanani da aka yi a shekara 100.

Bayan an shafe makonni ana irin wannan zafin, hukumar da ke kula da hasashen yanayi a arewa maso yammacin India ta bayyana cewa akwai alamun cewa za a samu sauƙi.

Amma saukin da ake tunanin za a samu ana sa ran ba za a daɗe ba inda ake sa ran watakila a koma gidan jiya.

Waɗanda ke shan wahala dai akasari talakawa ne - mutane kamar su Ms Yevale su ne irin wannan zafin ke wahalarwa sakamakon a halin yanzu suna neman yadda za su yi ne su rayu.

Prameela Walikar, wadda wata mai sayar da kifi ce, tana goge zufar da ke fuskarta kuma ta bayyana cewa da ƙyar take adana kifin da take sawowa a duk rana sakamakon tsananin zafi.

"Akasarin ribar da nake samu ina kashe ta ne ta hanyar sayen ƙanƙara wadda za ta sanyaya kifi," in ji ta. " Ban taɓa samun lalataccen kifi ba a tsawon shekarun da na ɗauka ina sayar da kifi. A yanzu wani lokacin ina asarar kimanin rupee 2,000 a rana.

Har farashin ƙanƙara ya ƙaru inda ya ruɓanya wanda hakan na bai wa masu sana'o'i wahala.

"Akwai buƙatar gwamnati ta samar da kayayyakin aiki da kuma ƙanƙara domin taimaka wa masu sayar da kifi sakamakon zafin da ake ciki," in ji ta.

Labarin waɗannan matan biyu yana haskaka rayuwar miliyoyin mutanen da ke rayuwa ko kuma cin abinci ta hanyar irin waɗannan sana'o'i.

Sai dai a daidai lokacin da ake wannan zafi akai-akai, masana na cewa ayyuka kamar gine-gine da kuma noma za su iya zama ayyuka masu haɗari a lokacin irin wannan zafi.

Wannan ba wai maganar lafiyar al'umma bace kawai, amma ga tattalin arziki sakamakon illar da zai yi wa ayyukan yi. A yanzu India na asarar dala biliyan 101 a duk shekara saboda zafi kamar yadda wani rahoto ya bayyana.