Ana murnar cikar 'yan-tara shekara daya da haihuwa a Mali

'Yan-tara da aka haifa a karon farko a duniya a lokaci guda suna cikin "koshin lafiya" a yayin da suka shekara guda a duniya, kamar yadda mahaifinsu ya shaida wa BBC.

"Dukkansu suna rarrafe yanzu. Wasu daga cikinsu suna mikewa tsaye kuma za su iya tafiya idan suka rike wani abu," a cewar Abdelkader Arby, wanda soja ne a rundunar sojin Mali.

Har yanzu suna karkashin kulawar wani asibit da ke Morocco inda aka haife su.

Ya ce mahaifiyarsu Halima Cissé, mai shekara 26, ita ma tana cikin koshin lafiya.

"Ba abu ne mai sauki ba amma abin sha'awa ne. Ko da yake za ka ji ka gaji a wasu lokutan, amma idan ka kalli dukkan jariran cikin koshin lafiya, za ka ji dadi. Mun manta dukkan abubuwan da suka faru," kamar yadda ya bayyana a hirarsa da BBC Afrique.

Bai dade da komawa Morocco ba a karon farko cikin wata shida, tare da 'yarsu, Souda, mai shekara uku.

"Na yi matukar jin dadin sake haduwa da iyalina - matata, 'ya'yana da ni."

Za su gudanar da wani karamin biki na kewayowar ranar haihuwarsu tare da likitocin asibiti da kuma mutanen da ke gidansu, in ji Mr Arby.

"Babu abin da ya fi dadi kamar yadda suka shekara guda. Za mu tuna da wannan yanayi da kuma abubuwan da suka faru a baya."

Jariran sun kafa wata bajinta ta littafin Guinness World Record a matsayin jariran da aka haifa mafiya yawa a lokaci guda kuma suka rayu.

Gabanin bikin zagayowar ranar haihuwarsu, gwamnatin Mali ta kai Mrs Cissé Morocco domin ba ta kulawa ta musamman.

Haihuwar yara da yawa lokaci guda tana da matukar hatsari kuma ana bai wa matan da ke da 'yan-tayi fiye da hudu a cikinsu a lokaci guda da a cire musu wasu a kasashen da aka amince da zubar da ciki.

Kazalika akwai hatsari game da yadda jariran za su iya fuskantar matsalolin rashin lafiya saboda an haife su lokacin haihuwarsu bai yi ba.