Elon Musk ya sayi Twitter: Wanne sauyi za a samu a kamfanin?

Lokacin karatu: Minti 5

Elon Musk ya kulla yarjejeniyar sayen kamfanin Tuwita tare da yin alkawarin rage sa ido a kan shafin, wanda ya sa ake dasa ayar tambayar abin da wannan kudiri nasa ke nufi ga "masu mu'amala da fasahar sadarwar ta intanet."

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun nuna damuwa cewa rashin sa ido zai iya haifar da karuwar kalaman nuna kiyayya.

Su ma masu amfani da shafin Tuwita na tambayar ko hakan na nufin za a dawo da shafukan wasu da aka toshe.

Mutum mafi shahara da aka taba dakatar da shafinsa shi ne Donald Trump.

Bayan sanar da yarjejeniyar cinikin, kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun nuna matukar damuwa game da kalaman nuna kiyayya a shafin na Tuwita da kuma karfin da zai bai wa Mista Musk, wanda ke bayyana kansa a matsayin "mai tsananin goyon bayan 'yancin magana".

Ya kasance mai baki sosai a sukar da yake yi wa dokokin shafin na sa ido a kan abubuwan da ake wallafawa, yana mai cewa kamata ya yi Tuwita ya zama wani sahihin dandali na 'yancin magana.

A wata sanarwa bayan kammala yarjejeniyar cinikin, ya bayyana 'yancin fadar albarkacin baki a matsayin ''kashin-bayan ingantacciyar dimokuradiyya."

A wasu jerin kalamai a shafin Tuwita, kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce: "Mun damu da duk wasu matakai cewa Tuwita ka iya daukar matakin soke dokoki da manufofin da aka tsara don kare masu amfani da shafin.

"Abin da ba za mu so ba shi ne shafin Tuwita wanda runtse idonsa da gangan kan kalaman batanci ga masu amfani da shafin, musamman wadanda abin ya fi shafa da suka hada da mata, da mata-maza da dai sauransu."

Kamfanin Tuwita bai yi saurin mayar da martani kan bukatun da BBC ta mika masa game da maganganun ba.

Shin Trump zai sake dawowa?

An cire shafin Donald Trump baki daya a shekarar da ta gabata a daidai lokacin boren 6 ga watan Janairu a ginin majalisar dokoki a Washington.

Amma ko da an sake dawo masa da shafinsa na Tuwita da aka toshe, Mista Trump ya ce ba zai dawo ya cigaba da amfani da Tuwita ba, a maimakon haka zai koma amfani da na shi dandalin na Truth Social.

"Ba zan koma Tuwita ba, zan cigaba da amfani da Truth," Mista Trump ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News.

Ya kuma kara da cewa ya yi amanna Mista Musk, wanda ya kira a matsayin "mutumin kirki" zai "kawo cigaba" ga dandalin.

Wakilan Mista Trump basu mayar da martani ga bukatar da BBC ta mika musu ba.

Ming-Chi Kuo, wani mai sharhi kan al'amuran fasahar zamani a wani kamfanin TF International Securities, ya shaida wa BBC cewa Mista Trump zai iya yanke shawarar sake dawowa dandalin idan zai sake tsayawa takarar shugaban kasa ne shekarar 2024.

Har yanzu Twitter shi ne zafi mafi kyau a gare shi na yin maganganu, muddin Tuwita ta shirya sake dawo da shafinsa," Mista Kuo ya bayyana.

"Ba abu mai sauki bane ka kafa wani dandali mai yawan mabiya irin Tuwita kafin zaben shugaban kasa mai zuwa."

Shin mutane za su bar Tuwita?

Mista Musk ya ce yana fatan cewa manyan masu sukar lamirinsa za su cigaba da kasancewa a dandalin "saboda hakan shi ne ma'anar 'yancin magana."

Amma kuma wasu masu amfani da dandalin sun yi barazanar ficewa daga Tuwita, a yayin da tuni wasu suka fice.

Wata 'yar wasan kwaikwayo ta kasar Birtaniya Jameela Jamil, wacce aka fi sanin ta a rawar da ta ke takawa a wasan kwaikwayon talabijin mai dogon zango da ake kira The Good Place, ta bayyana cewa tana da yakinin cewa dandalin "zai kara zama wuri marar bin doka, da tsana, da nuna kiyayya ga wadanda ba 'yan kasa daya ba, da girman kai, da nuna kin jinin mata.

"Ina son wannan ya kasance rubutuna na karshe a Twitter," Mis Jamil da shaida wa miliyoyin mabiyanta.

Amma kuma, Caroline Orr Bueno, wata mai bincike a Jami'ar Maryland, ta bayyana cewa a halin yanzu za ta cigaba da kasnacewa a dandalin, inda ta ke da mabiya fiye da 450,000.

Mis Bueno ta ce "ba mu san yadda zai kasanace a karkashin shugabancin Elon Musk ba."

"Abinda muka sani shi ne muddin mutane masu mutunci suka fice, zai kara lalacewa cikin sauri," ta kara bayyanawa

Dan Ives, wani mai sharhi a kamfanin Wedbush Securities, ya shaida wa BBC cewa yana tsammanin akasarin masu amfani da dandalin "za su jira su ga kamun ludayinsa."

"Yanzu batu ne na zawarcin sabbin masu amfani da shafin da kuma dakatar da masu son su fice,'' Mista Ives ya ce.

Akwai rashin tabbas

Majalisar gudanarwar kamfanin Tuwita mai mutane 11 ta amince ba tare da wata-wata na gat ayin Mista Musk na dala biliyan 44 ko fan biliyan 34 da miliyan 5.

Jack Dorsey, wanda ya kafa kamfanin na Tuwita da kuma har yanzu ke cikin majalisar gudanarwar, ya bayyana cewa yana mai farin cikin cewa dandalin "zai cigaba tafiyar da ayyukan yada maganganun jama'a'', duk da cewa bai amince cewa ''kowa zai iya mallaka ko tafiyar da kamfainin Tuwita ba."

"Tana son zama dandalin jama'a a matakin bin tsarin doka, ba kamfani ba,'' Mista Dorsey ya wallafa a Tuwita ranar Talata.

"Shawo kan matsala kasancewarsa kamfani amma kuma, Elon shi ne mutum daya da zai yin a tabbata," Mista Dorsey ya kara bayyanawa.

Babban daraktan kamfanin na Tuwita Parag Agrawal shi ma ya yi wa ma'aikatan kamfanin jawabi a wata ganawa, inda ya ce akwai rashin sanin tabbas game da makomar kamfanin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

"Da zarar an kammala yarjejeniyar, ba mu san alkiblar da kamfanin zai karkata ba," Mista Agrawal ya bayyana.

'Yan siyasa sun mayar da martani

A ranar Litinin, mai magana da yawun fadar White House Jen Psaki ta shaida wa manema labari cewa shugaban Amurka Joe Biden "hya dade da nuna damuwa game da karfin shafukan sada zumunta masu dimbin mabiya'', ko wanene ya mallaka ko ke tafiyar da Tuwita.

'Yar majalisar dattawa daga jam'iyar Democrat Elizabeth Warren ta ce yarjejeniyar cinikayyar "na da hadari ga dimokaradiyya."

Amma kuma, 'yar majalisar dattawa daga jam'iyar Republican Marsha Blackburn ta yi lale marhabun da yarjejeniyar a matsayin "lokacin karfafa guiwa ga 'yancin magana."