Zaben 2023: Hadakar 'yan takarar shugaban kasa hudu na jam'iyyar PDP daga yankin arewa ta wargaje

Asalin hoton, PDP
Gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya ce sun kasa cimma matsaya kan ɗan takarar da za su mara wa baya a tsakanin wata haɗaka ta mutum hudu da suka kafa don daidaitawa wajen fitar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Gwamnan ya ce a yanzu babu batun maslaha ko kuma wani ya janye wa wani a tsakanin masu neman takarar.
Gwamnan ya ce kafin wannan lokaci an yi tunanin tsakaninsa da Sanata Bukola Saraki da gwamnan Bauchi Bala Mohammad da Muhammad Hayatudeen da duk ke neman tikitin takara a inuwar PDP na iya maslaha a tsakaninsu.
Sai dai lura da yadda abubuwa ke tafiya kowa kawai tashi ta fisshe shi.
Gwamnan na wannan kalamai ne bayan wata sanarwar da ya fitar a yammacin jiya Juma'a tare da jaddada cewa a shirye yake a fafata da shi a zaben 2023.
"Mun zauna mu hudu 'yan takara wadanda a kashin kanmu muka yi matsayar cewa za mu tattauna mu yi sulhu a tsakaninmu, muka duba muka tattauna muka yi matsayar cewa abunda mu ke yi ga dukan alamu ya ci- tura.
"Saboda haka ya kamata mu ba kanmu shawara da kuma yin matsaya a kan cewa mu je kowa ya ci gaba da nema, duk abin da Allah ya yi sai mu karba," in ji Tambuwal.
Gwamnan ya ce bayan da suka kasa daidaita kansu sai suka yanke shawara zuwa gidan tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da ke Minna kuma a zaman farko da suka yi sai ya nemi su yi zabe.
Tambuwal ya ce nan take ya fitar mu su da takardar kuri'a amma dukaninsu sun ki amincewa da haka saboda a ganin su wannan ba ita ce hanyar da za a sami maslaha ba.
Ya ce a nan ne kuma suka yanke shawarar sake neman lokaci da za a yi shawara da shugabanni domin a ga yadda za a samu maslaha.
Sai dai ya yi ikirarin cewa akwai wasu daga cikinsu da suke hanzari domin ganin kokarin da suke yi ya kawo karshe.
"Hadakarmu ta kawo karshe, wannan abin da aka yi a Minna bai kawo kaina ba, bai hau kan magoya bayana ba, don mun yi matsaya ranar Laraba cewa wannan abin ya ci tura kuma za mu ci gaba da takara" .
A kwanakin da suka gabata tsohon gwamnnan jihar Kwara Sanata Bukola Saraki da gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad da takwaran aikinsa na jihar Sokoto Aminu Waziri Tambawul da Muhammad Hayatudeen suka soma kokarin ganin cewa sun zabi mutum daya daga cikinsu da za su mara wa baya daga yankin arewa.
Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ba ya cikinsu.
Kafin wannan barakar ta kunno kai bayanai sun ce 'yan takarar hudu sun so su fadada yunkurin nasu zuwa kasa baki daya a maimakon yankin arewa.











