Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
100m: Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan tsadar fom na takara a APC
Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan tsadar fom na takara a jam'iyyar APC mai mulki inda ta ke sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100.
A ranar Laraba ne majalisar zartarwar jam`iyyar APC ta tabbatar da jadawalin zabukan fitar da gwani na masu neman mukamai daban daban a jam`iyyar da kuma farashin fom na kujerun takara.
Majalisar zartarwar jam`iyyar APC ta yi zaman ne ƙarƙashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin jam`iyyar na kasa da jihohi da gwamnoni da sauran jiga-jiganta daga sassan Najeriya inda aka amince da farashin fom na neman takara da ranakun da jam`iyyar za ta gudanar da zabukan fid da gwani a matakai daban-daban.
A sanarwar da APC ta fitar ta ce masu son yin takarar shugaban ƙasa a APC za su biya kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30, sai kuma kuɗin fom naira miliyan 70.
Masu son yin takarar gwamna za su lale naira miliyan 50, yayin da sanatoci za su biya miliyan 20.
Masu fatan zama 'yan majalisar wakilai za su biya naira miliyan 10. Ƴan majalisar jiha miliyan biyu.
Tuni batun ya haifar da ce-ce-ku-ce inda ƴan Najeriya ke bayyana ra'ayoyinsu.
Har an ƙirƙiri maudu'in naira miliyan 100 a shafin Twitter, inda ƴan Najeriya ke tattauna tsadar fom din shugaban ƙasa.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Ra'ayin ƴan Najeriya ya fi karkata ne kan naira miliyan 100, farashin fom na takarar shugaban ƙasa.
Wasu na ganin kudin sun yi yawa, yayin da wasu ke ganin wannan ne ke sa dole ƴan siyasa su yi sata saboda maƙudan kuɗin da suka kashe kafin samun muƙamin siyasa.
Kabir Dakata a ra'ayinsa "APC ta halatta sata a gwamnati. Duka jimillar albashin gwamna na shekara hudu bai kai naira miliyan 50 ba, ina ake tsammanin zai dawo wa kansa da kuɗaɗen"
@OfficialWazobia bayan ya zayyano farashin fom da APC ta ƙayyade, a ra'ayinsa yana ganin wannan wata dama ce ta hana wasu da suka cancanta yin takara.
@AM_Ridwan_ a ra'ayinsa ya ce bayan sayen fom, abin da ɗan siyasa zai fara mayar da hankali akai shi ne yadda zai mayar da kuɗaɗen da ya kashe.
A ra'ayin @Adedeji yana ganin tsadar fom din zai iya zama babban dalilin da ƴan siyasa za su duk yadda za su yi domin su lashe zaɓe, kuma idan sun yi nasara abu na farko shi ne yadda za su dawo da kuɗaɗensu.
Wasu kuma na bayyana ra'ayin cewa tsadar fom ɗin hanya ce ta hana wa matasa yin takara.
@Patholo81067994 ya ce: Ko ina ake tunanin matashi zai samu waɗannan kuɗaɗen, yana mai cewa wannan karya masu ƙwarin guiwa ne a siyasa.
A na shi ra'ayin @SHOGBIYANJU1 tambaya ya yi cewa: "ta yaya ƙasar nan za ta gyaru? Duk wani matashi da ya nuna shawa'ar yin takara, kuma ya fitar da waɗannan kuɗin, na tabbatar EFCC za ta fara farautarsa."
Wasu kuma na bayyana ra'ayinsu ne kan wasu matsalolin Najeriya da aka kasa magancewa musamman yajin aikin ƙungiyar malaman Jami'o'i ta ASUU da har yanzu ake ja-in-ja da gwamnati.
@KefasKyenmann cewa yanzu dole sai ka mallaki miliyoyi kafin ka iya sayen fom ɗin takara, (kafin ma kamfen) a cibiyar talauci ta duniya. Idan kuma ba ka da su sai dai ka bi ta wasu hanyoyin ka samu kuɗin.
"Me zai hana ka yin sata domin mayar da kuɗaɗenka idan har ka yi nasara.?"