APC ta kawar da batun maslaha a tsayar da dan takarar shugaban kasa

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce ba za a yi maslaha ba a wajen zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Ta bayyana haka ne ranar Laraba a yayin taron majalisar zartarwarta, a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin jam`iyyar na kasa da jihohi da gwamnoni da sauran jiga-jiganta daga sassan Najeriya
Jam'iyyar APC ta sanar da sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100 a babban zaɓe na 2023 mai zuwa.
Wani jadawalin gudanar da zaɓukan fid da gwani da jam'iyyar ta fitar bayan taron Majalisar Zartarwarta ya nuna cewa masu son yin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin tutar APC za su biya kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30, sai kuma kuɗin fom naira miliyan 70.
Kazalika, masu son yin takarar gwamna za su lale naira miliyan 50, yayin da sanatoci za su biya miliyan 20.
Masu fatan zama 'yan majalisar wakilai za su biya naira miliyan 10. Su kuma 'yan majalisar jiha miliyan biyu.
Wannan shi ne karon farko da kwamitin zartarwar APC ya yi zama bayan babban taron jam`iyyar, inda aka zabi sabbin shugabanni na kasa.
Kazalika taron ya zo ne a lokacin da hukumar zabe ta bai wa jam`iyyun siyasa wa`adin nan da watan Yuni mai zuwa su mika mata sunayen wadanda za su yi takara da tutocinsu.
APC ta yi taron ne a yayin da wasu `yan jam`iyyar suke cikin fushi sakamakon zargin rashin adalci da suka cewa ana yi a jam`iyyar.
Tuni wasu jiga-jigan jam`iyyar suka sauya sheka ko kuma suka kama hanyar yin hijira daga jam`iyyar APC irin su tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa da ma wasu jiga-jigan jam'iyyar.
Sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa jam’iyyun siyasa da dama ne ke zawarcinsu, bayan zaluncin da yake zargin APC ta yi masu.
Sanatan ya shaida wa BBC cewa “Gaskiya jam’iyyu da yawa sun nemi mu suna son mu taka karagar motarsu domin kai wa ga biyan bukatu na siyasa.”
Barrister Soloman Dalong, tsohon Ministan Wasanni, kuma dan ga-ni-kashe-nin jam`iyyar APC, ya ce shi da APC haihata-haihata, har ma ya samu masuki a jam`iyyar SDP.












