Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban Jam'iyyar APC

..

Asalin hoton, FEMI ADESINA

Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru ne ya sanar da hakan a yayin babban taron jam'iyyar bayan duka waɗanda suke takarar sun janye wa Abdullahi Adamu.

Kafin sanar da shi a matsayin sabon shugaban, sai da Gwamna Badaru ya tambayi wakilan zaɓe ko kuma deliget kan cewa sun amince da Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban APC, sai suka ce sun amince.

Tun kafin a soma taron dama ana ta raɗe-raɗin cewa za a samu maslaha a ba Abdullahi Adamu shugabancin, inda a yayin taron ne masu takarar suka sanar da cewa duk sun janye.

Sanata Abdullahi Adamu wanda da farko ba ya cikin waɗanda suka nuna sha'awar takarar shugabancin APC, amma daga baya ya kutso kuma ya samu goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni.

Wannan goyon bayan ne ya tilasta wa sauran ƴan takarar shugabancin APC janye wa a ranar Asabar kafin shiga dandalin taron.

Ƴan takarar da suka janye sun da tsohon gwamnan Benue George Akume da tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura da tsohon gwamnan Zamfara Abdul'Aziz Yari Abubakar da Saliu Mustapha d kuma Etsu Muhammed

Sauran muƙaman da aka zaɓa

Abubakar Kyari daga jihar Borno aka zaɓa a matsayin mataimakin shugaban jam'iyya shiryar arewa, sai Emma Eneukwu daga Enugu a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar shiyar kudu.

Muhazu Rijau ne mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa shiryar arewa maso tsakiya da Mustapha Salihu a matsayin muƙamin mataimakin shugaban jam'iyya arewa maso gabashi.

Salihu Lukman ne mataimakin shugaban jam'iyyar shiyar arewa maso yammaci. Ijeoma Arodiogwu kuma mataimakiyar shugabar jam'iyya shiyar kudu maso gabashi.

Victor Giadom mataimakin shugaban jam'iyya shiyar kudu maso kudu da kuma Isaac Kekemeke a matsayin mataimaki shiyar kudu maso yamma.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun Iyiola Omisore, aka bayyana a matsayin sakataren jam'iyyar.

Beta Edu aka amince a matsayin shugabar mata ta APC, Abdullahi Israel kuma shugaban matasa na jam'iyyar.