Ko zamani zai bar sana'ar rini mai dumbin tarihi da rai a Kano?

    • Marubuci, Salihu Adamu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Sama da karnuka shida ke nan birnin Kano mai dumbin tarihi a arewacin Najeriya ke da wasu kebabbun wurare da ake sana'ar rini.

Kayatattun tufafi da ake rinawa cikin tukwanen baba ko kuma ramukan rini cikin ruwa mai launin shudi sun kasance masu farin-jini da ake sayar da su a sassan kasashen Nahiyar Afirka da kuma kasashen Larabawa.

Amma a yanzu mutane da yawa suna nuna damuwa kan yadda wannan sana'ar ta kaka-da-kakanni ke fuskantar barazanar bacewa.

Na tarar da Baba Muhammad zaune a bakin wata katuwar tukunyar baba cike da ruwan rini har baki, ruwan na dauke da launin shudi.

Dattijon, mai shekara 75, na tsomawa da kuma ciro tufafi cikin ramin ruwan rini hannayensa sanye da safar hannu ta roba.

Ya shafe shekaru aru-aru yana sana'ar rini sannan a yanzu yana fargabar kasancewa cikin mutane na karshe da za su yi sana'ar da ya gada daga kaka-da-kakanni

"Matasa suna nuna halin-ko-in-kula kan wannan sana'ar ta rini, sun fi son sana'o'i na zamani kamar dinka kayayyaki maimakon rina su," a cewarsa.

Alakar rini da tattalin arzikin Kano

Baba Muhammad na daga cikin mazan-jiya da ke sana'ar rini wacce ke fuskantar barazanar rushewa duk da kasancewarta sana'a mai dumbin tarihi a nahiyar Afirka.

An kafa Karofin Kofar Mata ne tun a karni na 16 kuma tun a lokacin suka ci gaba da kasancewa hanyar dogaro wajen samun kudin-shiga ga mutane da dama a arewacin Najeriya.

Kamar yadda ake mata kirari da "Kano ta Dabo tumbin Giwa ko da me ka zo an fi ka," birnin ya kasance cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya mai matukar muhimmanci wajen cinikayya tsakanin kasashen yankin Kudu da Sahara tun kafin mulkin-mallaka na Turawa.

Masana tarihi na ba da labarin yadda Buzaye da Larabawa ke ketarawa daga kasashen yankin Kudu da Sahara da kuma Asiya tare da rakuma dauke da dabino su sayar a kasar Hausa sannan su sayi rinannen tufafi su koma da shi kasashensu.

Tufafin yana kayatar da bakin ne saboda wasu sinadarai na gargajiya da ake amfani da su wajen rina wadannan kayayyaki.

Har ya zuwa zamanin yau, masu rini na cewa babu ruwansu da sinadaran rini na zamani sai na gargajiya da ke kayatar da tufafin da suke rinawa.

Sai dai a 'yan shekarun nan, sana'ar na fuskantar barazanar shudewa.

Matsalolin da sana'ar rini ke fuskanta?

Rikicin Boko Haram a arewacin Najeriya musamman Arewa Maso Gabas ya rage yawan kwastomomi da ke zuwa sayen kaya.

Baballiya Hamisu wani matashin mai rini ne a Kofar Mata.

"A da masu yawon bude-ido daga sassan duniya kamar kasashen Faransa da Jamus da Ingila da Amuraka da dai sauransu na zuwa Kofar Mata, to amma matsalar rashin tsaro ta kori duk wadannan baki sun daina zuwa," a cewarsa.

Baballiya, mai shekara 37 a duniya, na daya daga cikin matasa da ke rini a Kofar Mata. Ya ce ya shafe shekaru da dama yana sana'ar rini.

"Na fara rini tun ina dan shekara 10, yanzu na shafe shekara 25 ina aikinnan," in ji shi.

Har wa yau, ya ce abun takaici ne ganin harkar rini na fuskantar koma-baya a Kano.

"A lokacin da nake yaro, muna da tukwanen baba da yawa a nan amma guda 144 kadai suka rage sannan a haka ma ba dukkan su ne ke aiki ba."

Kano na daya daga cikin biranen da ke bunkasa ta fannin tattalin arziki da gine-gine a Afirka . A shekarun baya-bayannan birnin Kano ya fuskanci wani yanayi na rushe fitattun wurare masu dumbin tarihi, amma gwamnati na cewa matakin ya zama tilas domin mayar da Kanon birni na zamani.

Tijjani Muhammad Naniya, Malamin Tarihi a Jami'ar Bayero ta Kano, ya ce ba zamanantar da Kano ta hanyar rushe wuraren tarihi ne kawai barazana da wuraren rini ke fuskanta ba.

"Matsalar ta faro ne tun lokacin mulkin Turawa saboda sun kawo wani tsari da suka ce zai inganta tattalin arzikin Kano ta hanyar shigo da tufafi daga ketare kamar birnin Manchester".

Sauki da tufafin da ake shigar da su shi ya karya darajar wadanda ake rinawa a cikin gida. Ko da yake wasu lokuta farashin kayayyakin duka biyu ba shi da tazara tsakaninsa amma mutane sun fi amfani da na kasashen ketare saboda irin kawata su da ake yi.

Su ma mata da ke cikin gidaje ba a bar su a baya ba, domin kuwa su suke yin kananan kulli a jikin duk tufafi da ake rinawa domin samar da zane kala-kala a jikinsu sannan a sake mika su ga marina.

Akasarin wadanda ke rini a Kofar Mata jikoki ne da tattaba kunnen marina. Mutane kamarsu Haruna Baffa da ya gaji sana'ar daga kakansa na bakwai ya ce kakansa Muhammadu Dabosa ne ya kafa Karofin Kofar Mata.

Sakataren na katafaren filin rini na Kofar Mata ya kara da cewa babu wani tallafi a hukumance daga wajen gwamnati da marina suka samu domin habaka sana'ar tasu.

Mallam Hamisu yana ganin akwai abunda za a yi wajen ceto masana'antar ta rini da ta shafe shekaru aru-aru.

"Idan gwamnati za ta sayi tufafin da muke rinawa sannan su karfafawa mutane su ma su saya, to da sana'ar tamu za ta ci gaba da habaka," a cewar Baballiya Hamisu.

"Misali a yanzu idan shugaban kasa ko gwamna zai sanya irin tufafin da muke rinawa a nan Kofar Mata ai kun ga duk rashin kyansa dole ya yi daraja".