Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne ɗan Daudu, kuma me ake ɗaukar sa a ƙasar Hausa?
A wannan makon ne wani dan majalisar wakilan Najeriya ya gabatar da wani kuduri, da ya nemi a yi garambawul kan dokar da ta haramta auren jinsi a kasar.
Honarabul Muda Lawal Umar mai wakiltar karamar hukumar Toro da ke jihar Bauchi a arewacin Najeriya ne ya gabatar da kudurin, wanda yanzu haka ya wuce karatu na farko a zauren majalisar.
Kudurin ya nemi a haramta ayyukan 'yan daudu a fili ko a boye, kamar yadda aka haramta auren jinsi a Najeriya.
Wannan batu ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen intanet a kasar, inda wasu suka rika nuna goyon baya wasu kuma na kalubatantar hakan, a gefe daya kuma wasu ba ma su san me ake nufi da dan Daudu ba.
Wannan ya sanya BBC Hausa ta kawo wannan makala domin yin bayani a kan wanene dan Daudu, kuma wane irin kallo ake yi masa a kasar Hausa?
Asalin kalmar Daudu
Masana irin su Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Jihar Sokoto, sun bayyana ma'anar kalmar Daudu da dan sarki mai jiran gado.
"Ko wanne irin dan sarki da ke jiran karagar mulki, kama daga dan sarkin mai kasa, ko dan sarkin kira ko fawa ko saka, duka 'ya'yan sarautar da ke jiran sarautar ta fadi su dauka su ake kira Daudu," in ji Farfesa Aliyu Bunza.
Amma a fassarar zaure wato wajen malaman fikihu, Daudu na nufin wanda idan an zo rabon gado yake kwashe komai, kamar ɗa da mahaifi da 'yan uwa shakikai ko kuma wadanda ake uba daya da su dukkansu ana kiransu Daudu a wajen malaman zaure.
Domin haka a karan kanta kalmar Daudu a wajen masana harshe ko kuma malaman fikihu kalma ce mai kyau ba ta da wata illa.
Wanene ɗan Daudu?
Kalmar dan Daudu tana da ma'ana guda biyu, a mafi yawan lokaci a irin al'adar Bahaushe da ka ji an ce dan Daudu wato ana nufin jikan sarki ke nan.
Yaro ne da yake tashi cikin gata da shagwaba, babu mai kwabarsa sai ya zama sangartacce, a lokuta da yawa sunan sarki ake san ya masa don haka ake girmama shi da yawa.
Ma'ana ta biyu ita ce namiji da ke da al'ada irin ta mata, "sau da dama akan haifi wasu yaran da muryar mata ko kuwa jiki irin na mata, ta fuskar karairaya da sauransu.
"Wasu lokutan kuma a a saboda shi kadai ne namiji a tsakiyar 'yan uwansa mata zai rika magana motsi da sauran al'amura kamar mace.
"Akwai kuma mutumin da yake zama dan Daudu na kasuwa zai yi doya da kwai zai dafa tuwo, sana'o'in da yake duka na mata ne, kuma rayuwarsa ma a cikinsu yake yi dumu-dumu, to wannan shi ma ana kiransa dan Daudu," in ji Farfesa.
Amma a Hausa da an ce dan Daudu, ana nufin wannan wanda ba shi da wata nakasa ya dauki harkokin Daudu ya dora a kansa.
Ma'anar farko in ji Farfesa ma'ana ce mai kyau a asalin al'ada da tarihin Bahaushe.
Bambancin da Daudu da mata-maza da kuma masu sauya halittarsu zuwa mata
Farfesa ya ce babu abin da ya hada mata-maza da harkokin 'yan Daudu, shi kawai al'aura ce da shi iri biyu ta mace da ta namiji. Duk bangaren da bincike ya nuna ya fi rinjaya a nan za a yi wa mutum hukunci a kansa.
Ga al'ada irin ta Bahaushe ba a sanin mata-maza saboda ba ya magana irin ta mata, sai dai idan wata sura ta bayyana a jikinsa irin ta mata, kamar mama ya fito masa ko kuma manyan mazaunai.
Bahausahe bai san masu sauya halittarsu zuwa mata ba a kimiyance, yanzu ne wannan abu yake mamaye duniya in ji Farfesa.
"Amma mun san Daudu dan sarki mun san dan Daudu jikan sarki sannan kuma munsan dan Daudu na zamani mai karairaya da sauya dabi'arsa zuwa ta mat.
Duk dan sarauta yana son a kira shi dan Daudu, a duniyar Bahaushe babu wanda yake so a kira shi da dan Daudu wanda ya sanya kansa harkokin mata.
Sabuwar al'ada ce a wajen Bahaushe amma a kasashen duniya irin na su Asiya inji Farfesa Aliyu sun jima da 'yan daudu, amma ba irin wadanda muka sani ba.
"Mafi yawan 'yan Daudunsu mata-maza ne, mutanen da gaba daya ba su da mazakuta.
"Mu daudu a nan kasar Hausa ɗabi'a ce da ta shigo da muke zaton da makircin Turawan mulkin mallaka na mayar da mazajenmu masu girke-girke da suka yi," farfesa ya kara da cewa.
Dan Daudu a idon Bahaushe
Kai tsaye Bahaushe ba ya ganin dan Daudu mai kwaikwayon mata a matsayin mutumin kirki, amma hakan ba ya hana a yi mu'amala da su.
A sau da dama mukan sayan abinci hannusu mu ci, ko mu sha da wasu mu'amaloli na daban.
Ta yadda mutum zai san cewa Daudun kwaikwayon mata ba a abin da Bahaushe ke kallo ba ne a matsayin abin arziki babu mai fatan nasa ya kasance a wannan yanayi.