Zaɓen 2023: Jam'iyyun siyasar Najeriya sun ce sun kammala shiri

Jam'iyyun siyasar Najeriya kama daga jam'iyyar APC mai mulki da babbar jam'iyyar hammaya wato PDP sun ce sun kammala shiri domin fafatawa a zaɓen fid da gwani cikin wa'adin da hukumar zaɓen ƙasar ta ƙayyade.

Jadawalin zaɓen 2023 ya nuna cewa jam'iyyun ƙasar za su yi zaɓukan fitar da gwanayensu ne daga ranar 4 ga watan Afrilu har zuwa ranar 3 ga watan Yuni.

Zaɓukan fid da gwanin, wani mataki ne na tunkarar babban zaɓen na 2023.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ce jam'iyyun da ke son shiga zaben 2023 a hukumance za su iya gudanar da zaben fid da gwani tun daga ranar 4 ga watan da muke ciki har zuwa 3 ga watan Yuni.

Sai dai ta ce dole ne jam'iyyu su warware duk wata takadaama da kan iya tasowa sakamakon zabukan cikin wata biyun da ta kebe.

Farfesa Moustapha Osuji, daraktan shirye-shirye a helkwatar jam'iyyar APC mai mulki, ya ce a koyaushe jam'iyyarsu na aiki da abin da ya doka ta ce.

"Kowace jam'iyya na da tsari game da yadda take tafiyar da harkokinta kuma jam'iyyar APC kan duba tsare-tsaren da suka yi daidai da dokar zabe kuma za ta fitar da nata jadawali na takara tun daga Majalisun jiha zuwa Majalisun tarayya da zabukan gwamnonin jihohi da kuma na shugaban kasa," in ji shi.

Ita ma jam'iyyar Accord ta ce nan ba da jimawa za ta gudanar da zaben fid da gwani a matakai daban-daban. Shugaban jam'iyyar na kasa Hon Mohammed Lawal Na Lado ya ce: "A gaskiya muna cikin shiri sosai domin ya kamata mu jam'iyyu mu ba da goyon baya kuma mu zage dantse mu ga cewa mun yi abubuwan da suka kamata domin a guje wa abubuwan da ita INEC ta ke gudun kar su faru a gaba".

Ita kuma babbar jam'iyya hamayya ta PDP ta ce za ta yi biyaya ga umarnin INEC kuma za su yi amfani da masalaha wajen fitar da 'yan takararsu a dukkan matakai.

Sai dai mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ya ce za su yi zabe a wuraren da aka kasa cimma maslaha.

A cewarsa " PDP jam'iyya ce mai biyayya ga umarni musamman na hukumar zabe wadda ita ce ta fida da wannan jadawali, ina son na tabbatar maka da cewa ba mu da wata matsala, kusan jihohin da ake da matsala na mukamai muna nan muna kokarin mu yi sulhu ga 'yan takara mu ga mun fitar da yarjejeniyar akan mutum daya. Idan haka bai samu ba toh za mu ba da dama a yi zaben fid da gwani."

Hukumar zabe mai zaman kanta ta debarwa jam'iyyun suyasra wa'adin watanni biyu don gudanar da zaben fid da gwani domin warware duk wani rikici da kan iya biyo baya.

A baya 'yan takarar da ba su amince da sakamakon zaben fid da gwani na jam'iyyarsu kan garzaya kotu domin kalubalantar zaben.