Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jam'iyyar PDP: APC da Buhari ba su damu da rayuwar 'yan Najeriya ba
Jam'iyyar PDP a Najeriya ta zargi jam'iyyar APC mai mulkin kasar da nuna halin ko-in-kula game da matsalar tsaro da ta addabi kasar, lamarin da ta ce shi ne ya janwo mummunan harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, abin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum takwas da jikkatar mutane da dama.
A wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, jami'iyar ta PDP ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira rikon-sakinar-kashin da gwamnatin APC ke yi wa harkar tsaro a kasar.
Babbar jam'iyyar adawar dai na shan zargin gwamnatin APC da gazawa, amma kuma galibi ta fi yin matsin lamba kan batun matsalar tsaron wacce ta bayyana ta rinjaye sauran matsalolin da ake fama da su a kasar.
Magana zarar bunu ce
A sanarwar ta jam'iyyar PDP din ta fi mayar da hankali ne kan ikirari da kalaman da wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar APC suka furta game da mummunan harin da aka kai kan jirgin kasa a ranar Litinin.
Ta ce kalaman da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da kuma gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai suka yi game da matsalolin tsaron da cewa hakan ya tabbatar da cewa akwai hadin-baki tsakanin 'yan ta'adda da gwamnatin APC.
"Ikirarin da gwamnan Kaduna Malam el-Rufai da kuma Ministan Sufuri Rotimi Amaechi suka yi game da batun hare-haren 'yan bindigar ya tabbatar da zargin da jam'iyar PDP ke yi cewa gwamnatin APC ta san inda 'yan ta'addar suke, kana ta san shirin da suke yi na tayar da zaune tsaye a kasar amma ta ki daukar matakai da gangan," in ji sanarwar.
''Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ce wasu ministocin APC mai mulki sun yi kafar-angulu wa bukatun da ya gabatar a taron majalisar ministoci cewa a kafa na'urorin bincike don kauce wa hare-haren ta'addanci a kan titin jiragen kasa na Kaduna zuwa Abuja, ya kara tabbatar da zargin cewa gwamnatin ta APC na bai wa 'yan ta'adda damar gudanar da ayyukan ta'addancinsu cikin sauki kasar," a cewar PDP.
A wani jawabi da Gwamna Nasiru El- Rufai ya yi a bainar jama'a a baya bayan nan ne in ji jam'iyar ta PDP, shi da kan ya yi wa gwamnatin ta APC bankada, wanda ta ce shi ma yana ciki - ya ce: "Mun san inda sansanoninsu suke, mun san inda suke, jami'an tsaron farin-kaya na SSS na da lambobin wayarsu, suna sauraronsu kuma suna ba ni rahoto.
Kazalika PDP ta jaddada ikirarin Ministan Sufuri Ameachi inda yake cewa: "Muna sane da matsalolin da za su faru. Mun san cewa muna bukatar na'urorin zamani …. Na yi gargadin cewa za a tafka asarar rayuka kuma ga shi yanzu an rasa rayuka…A lokacin da ka tunkari gwamnati da gaskiyar niyya amma abokan aikinka suka rika taka maka birki, abin bakin-ciki ne."
A kan irin wadannan kalamai da ikirari ne daga manyan jami'an gwamnati jam'iyar adawar da kafa hujjojinta cewa shugabannin APC na da alaka da 'yan ta'addar.
Don haka a sanarwata din ta kuma kara da cewa ba abin mamaki bane cewa shugaba Muhammadu Buhari ya dage a kan cigaba da barin Dakta Isa Ali Pantami a matsayin ministan sadarwa, wanda ta ce aka zarga da alaka da ayyukan ta'addanci.
Harin jirgin kasa ne ya kara kaifin zarge-zargen
Wannan dai ba shi ne karon farko da jam'iyar PDP ke zargin gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari ba wajen gaza shawokan matsalar tsaro da ta addabi kasar musamman a arewaci, wanda ake cigaba da tafka asarar dubban mutane.
Amma kuma na baya-bayan nan da ya faru a ranar Litinin wanda wasu 'yan bindiga suka kai mummunan har ikan jirgin kasa makare da fasinjoji kusan dubu daya da ke kan hanyarsu da zuwa Kaduna da Abuja ya kara harzukawa tare da jefa zullumi a zukatan 'yan kasar musamman masu bin wadannan hanyoyi.
Kana ya kara kaifin irin zarge-zargen da jam'iyar ta PDP ke yi wa gwamnatin Najeriyar game da matsalar tsaron.
Jama'ar kasar da dama ne dai suka ta'alaka da bin jiragen kasa zuwa Abuja da dawowa Kaduna saboda yawan kai hare-hare da sace sacen jama'a don neman kudin fansa da 'yan bindiga ke yi akai-akai a kan hanyar mota ta Abuja zuwa Kaduna.
Kuma wannan shi ne karo na biyu da 'yan bindigar ke kai har kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, kana mafi muni.
Mutane da dama ne suka jikkata, a yayin da wasu da har yanzu ba a tantance adadinsu ba suka rasa rayukansu a harin, bayan yin awon gaba da wasu fasinjojin da su ma har yanzu ba a san halin da suke ciki ba a hannun maharan.