Babban Bankin Duniya: Yawan masu fama da talauci a Najeriya ya zarce miliyan 95

Babban Bankin Duniya ya yi hasashen cewa yawan talakawa a Najeriya zai ƙaru zuwa mutum miliyan 95 a bana.

Ya bayyana haka ne a cikin wani rahotonsa mai taken "ƙoƙarin samarwa 'yan Nijeriya makoma ta gari."

Ya ce rage radadin fatara ya fuskanci cikas tun shekarar 2015 inda 'yan Najeriya da dama suka fada cikin kangin talauci a tsawon shekaru.

A cewar Bankin an yi hasashen adadin talakawan da za su fada cikin kuncin rayuwa a Najeriya zai kai miliyan casa'in da biyar da dubu dari daya a shekarar 2022.

Ya ce rahoton wani kokari ne na neman hanyoyin fitar da 'yan kasar daga kangin rayuwa.

Wata kididdiga ta baya bayan nan ta nuna cewa yawan matalautan kasar ya kai kashi 42 da digo takwas cikin dari a shekara ta 2020 wanda yana kasa da kididdiga ta 2010 da kuma ta 2011 da ya kai kashi 43 da digo biyar cikin 100.

Bankin Duniyar ya ce mai yiwuwa cikakken adadin masu fadawa talauci ya haura idan aka yi la'akari da yadda yawan al'ummar Najeriya ke karuwa cikin sauri.

Alkaluman da aka zayanna a baya bayan nan sun ba da kiyasin cewa talauci ya fara raguwa a farkon shekarun 2010 sannan kuma ya dawo a shekarar 2015.

Sai dai wannan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da koma-bayan tattalin arziki a 2016 sakamakon faduwar farashin mai a kasuwanin duniya.

Rahoton na Bankin Duniya ya ce annobar korona ta jefa 'yan Najeriya sama da miliyan biyar cikin talauci har zuwa shekarar 2022.

Wasu 'yan Najeriya sun shaida wa BBC cewa a yanzu ba sa iya cin abinci sau uku a rana saboda tsadar kayan abinci.

Wani mazaunin birnin Lagos ya gaya wa BBC cewa 'yan Najeriya na "kara fadawa cikin talauci a koyaushe, kusan kashai 70 cikin 100 na 'yan Najeriay na jin jiki. Maganar gaskiya da wahala nake iya yin cin abinci sau biyu a rana".

Ita ma wata mata cewa ta yi: "Talauci ya yi yawa sosai kuma idan akwai talauci to dole barayi su yi yawa a kasa".

Sai dai gwamnatin Najerya ta bullo da manufofin rage radadin talauci - kama daga bayar da rance kudi ga manoma da samar da guraben ayyuka ga matasa ta hanyar Shirin Npower da sauransu.