APC: Abubuwa shida da suka kamata ku sani gabanin babban taron jam'iyyar na ƙasa

    • Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Bayan ɗage taro har sau biyu da kiki-kaka cikin yanayin da ya kusa rusa komai, jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shirya tsaf domin gudanar da babban taronta na kasa a gobe Asabar.

Jam'iyyar za ta yi wannan babban taro ne a Dandalin Eagle Square da ke babban birnin ƙasar, Abuja, inda shugabannin jam'iyyar da wakilai za su hadu domin zaɓen sabbin shugabanni da za su ci gaba da tafiyar da harkokin jam'iyyar na tsawon shekara hudu.

Dandalin, wanda aka sauyawa fasali saboda taron, na shirin karbar bakoncin mutane dubu 12 da ake sa rai za su je taron domin kada kuri'arsu a zaben shugabannin.

Mutane 66 za a zaba a mukamai daban-daban na jam'iyyar, da kuma mambobin kwamitin gudanar da harkokin jam'iyya mutum 21.

Sai dai kafin a kai ga wannan taro akwai abubuwa da dama da suka faru da kuma ke kan faruwa musamman batun haɗin-kan 'ya'yan jam'iyyar da kuma mutumin da zai karbi shugabancinta.

Masana harkokin siyasa na cewa babban taron yana da tasiri sosai a kan makomar jam`iyyar APC.

BBC ta yi nazari kan wasu daga cikin abubuwan da suka kamata ku sani gabanin babban taron na APC.

Musayar mukamai

Tun kafin a kai ga wannan lokaci cikin makwanni baya jam'iyyar APC ta ware wa yankin arewacin ƙasar muƙamin shugaban jam'iyyar na ƙasa.

Gwamnan Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai ya faɗa wa manema labarai, jim kaɗan bayan ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari cewa jam'iyyar ta amince ta rarraba muƙaman da babu kowa a kai a Kwamatin Ƙoli na jam'iyyar tsakanin Kudu da Arewa kafin babban taronta.

Hakan na nufin muƙamin shugabancin jam'iyyar, wanda John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole suka riƙe a baya, dukkansu 'yan Kudu, zai koma Arewa.

Ya kuma ce sun amince da tsarin karkasa muƙamai ga dukkan shiyyoyin siyasa, ma'ana shiyyoyin Arewa za su samu muƙaman da na Kudu suka riƙe a cikin shekara takwas da suka wuce, su ma (na Kudu) haka.

Taron sassantawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron tattaunawa daban-daban da gwamnonin APC da shugabannin jam'iyya da mambobin majalisar dokoki a wani kokarin daidaita kawunan 'ya'yanta gabanin taronsu na Asabar.

Wasu daga cikin mutanen da Shugaba Buhari ya gana da su sun hada da tsohon shugaban riko na jam'iyyar Bisi Akande; da jagoran jam'iyya Bola Tinubu, da Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbomnaya Onu; Sanata Rochas Okorocha, Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Aliyu Wamako.

Sauran gwamnonin da Buhari ya tattauna da su su ne Nasir El-Rufai na Kaduna; Aminu Masari na Katsina; Ministan Sufuri Rotimi Amaechi; da shugaban riko na jam'iyyar, Mai Mala Buni; da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

A yau Juma'a kuma ana saran shugaban zai kuma gana da wasu gwamnonni 23 a kokarin dinke duk wata baraka da daidaita kawunansu ta yadda `ya`yan jam'iyyar su yi babban taro cikin lumana.

Gaza cimma matsaya

Wasu rahotanni na cewa wasu daga cikin gwamnonin da masu neman takarar shugabancin jam'iyyar har yanzu ba su gamsu da mara wa tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu baya ba kamar yadda Shugaba Buhari ke so.

Shugaban kasa dai na kokarin ganin an kauce wa kada kuri'a wajen zaben shugabannin, a maimakon haka a sasanta tsakanin 'yan takara, yayin da gwamnonin jihohi ke cewa za su goyi bayan duk wanda shugaba Buhari ya ce a ba kujerar shugabancin jam'iyyar.

Haka kuma shi ma gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello wanda ke cikin mambobin kwamitin riko na APC, ya shaida wa kafar Talabijin ta Arise na kasar cewa shugaba Buhari ya bukaci gwamnonin APC 23 su tabbatar Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam'iyya.

Sai dai wasu kusoshin jam'iyyar sun bayyana cewa ba su yarda da wannan tsari ba. Alal misali, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya ce zai ci gaba da fafutikar neman kujerar shugaban jam'iyyar duk da cewa ba yankinsu ne aka kebe wa kujerar ba, kuma a ganin sa bai wa wani yanki ko wani mutum mukamin ba tare da zabe ba, rashin adalci ne.

Hakan ne ma ya sa gwamnan Jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, ya shaida wa BBC cewa za a gudanar da zabe idan aka gaza cimma matsaya domin kada ran wasu ya baci.

Su waye ke takararshugaban jam'iyyar?

Kusan ana iya cewa mutum takwas ne ke wannan takara, sai dai mutum bakwai da suka hada da Mallam Saliu Mustapha da Mallam Mohammed Etsu da Sanata Mohammed Sani Musa da Sanata Tanko Al-Makura da Sanata George Akume da Sanata Abdullahi Adamu duka sun fito ne daga shiyyar Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Sai na takwas, shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari daga shiyyar Arewa Maso Yamma.

Ko da yake akwai Sanata Ali Modu Shariff, wanda ya ce ya koma gefe saboda rahotanni na cewa akwai wani shiri da ake yi don daidaitawa a bar kujerar ga wani dan takara, kuma a cewar sa Shugaba Buhari na goyon bayan shirin maslaha ko daidaitawar.

Sai dai Sanata Ali Modu Sharif ya gicciya sharadin cewa idan maganar ta sauya, to fa yana nan kuma da shi za a yi zawarcin kujerar.

'Ya'yan jam'iyyar da suka nuna kwaɗayin gadar Buhari

Tun kafin a kai ga jajiberen taron APC na kasa akwai mutanen da tuni suka soma nuna kwadayinsu na neman kujerar shugabancin Najeriya, har sun kai ga sanar da Shugaba Buhari anniyarsu.

Ɗaya daga cikinsu ko na gaba-gaba shi ne jagoran jam'iyyar APC din kuma tsohon gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu.

Akwai kuma rahotani da ke cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shi ma ya fadawa Buhari yana son kejarar, da kuma Sanata Rochas Okorocha.

Ruɗani gabannin taro

Akwai lokacin da jam'iyyar ta faɗa cikin ruɗani bayan gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yi iƙirarin karɓar jagorancin jam`iyyar a matsayin muƙaddashin shugaba na riƙo.

Wasu rahotanni sun ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sauke shugaban riƙon jam`iyyar, wato Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai mala Buni daga shugabancin jam'iyyar.

Sai dai, wasu ƴan kwamitin riƙon jam'iyyar sun musanta hakan. Abin da ya kai ga masana siyasa dai na cewa irin wannan dambarwar shugabanci da APC ke ciki na iya rage ƙarfinta a Najeriya.

Amma daga bisani an samu sassanci musamman bayan ganawar shugaba Buhari da Mai Mala Buni a Landan da kuma umartar a bai wa gwamnan ya Yobe damar cigaba da rike jam'iyyar har zuwa lokacin taronta.

Warware rikicin jam'iyyar a matakin Jihohi

APC dai ta rabe gida biyu a wasu jihohi na Najeriya kan rikicin shugabanci a irinsu Sokoto da Kano.

An shafe kusan wata hudu da aiwatar da zaɓukan shugabanni a matakin jihohi amma a waɗannan jihohin biyu rabuwar kawuna ta sa ba a daidaita ko kai wa ga mika shaidar shugabanci ga kowane mutum ba, har sai da aka dangana da kotu.

Sanan sauran jihohin da ake fama da rikici akwai Kebbi da Zamfara da Bauchi da Kwara da Osun da Delta da Rivers.

A Kebbi abin ya kai ga ɓangaren tsohon gwamna kuma sanata mai-ci, Muhammadu Adamu Aleiro, ya buɗe wata sabuwar hedikwatar jam'iyyar.

Hakan kuwa na faruwa ne duk da ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarensa da na gwamnan jihar, Sanata Atiku Bagudu da kwamitin Abdullahi Adamu ya yi.

Sharhi

Masana dai na cewa jam'iyyar tana cikin rudani saboda akwai bangarori da dama da ke hamayya da juna.

Sai dai shugabannin jam`iyyar APC dai sukan ce duk jam`iyyar da ta cika ta batse ta gaji hayaniya, ballantana APC mai mulkin kasa kuma suna daukar matakan daidaita kan `ya`yan jam`iyyar ta yadda za su samu mafita ga kowane irin rintsin da za su shiga.

Shi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa ya yi kira ga ƴan jam'iyyarsa da su gujewa koƙarin tayar da zaune tsaye a APC domin samun wanzuwa.

Buhari ya ce rikicin jam'iyya ba sabon abu ba ne a sassan duniya. "Amma rabuwar jam'iyya saboda son rai ba zai haifar da ɗa mai ido ba ga makomar jam'iyyar,"

Yanzu abin jira a gani shi ne ko babban taronta na kasa na iya dinke duk wata baraka da shirin 'ya'yanta domin kalubalantar babban zaben kasar da ke tafe a 2023.