Yakin Ukraine: Bala'in da 'yan Afirka ke ciki a garin Kherson da Rasha ta mamaye

A demonstrator gestures as others, displaying Ukrainian flags, chant "go home" and walk towards Russian military vehicles at a pro-Ukraine rally amid Russia"s invasion, in Kherson, Ukraine March 20, 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An rika gudanar da zanga-zanga a Kherson tun bayan da dakarun Rasha suka mamaye garin ranar 3 ga watan Maris
    • Marubuci, Daga Nomsa Maseko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos

Kusan dalibai 'yan Afirka 100 suna roko a taimaka musu su fice daga Kherson, birnin da ke kusa da tasoshin jiragen ruwa a Ukraine, fiye da mako biyu bayan da dakarun Rasha suka kwace shi.

Sun kwashe kwana da kwanaki suna zaune a gidajen karkashin kasa da ke makarantunsu a wani yanayi na tsananin sanyi, ba tare da na'urorin dimama jiki ko kuma magunguna ba. Sun ce suna cikin dimuwa kuma sun matsu su bar birnin da ke kudancin kasar.

Daya daga cikin daliban ya shaida wa BBC cewa har yanzu suna jin karar bindigogi da fashewar bama-bama da jiragen soja masu tayar da hankali.

Hakan zai iya zama karar fafatawa a yayin da dakarun Rasha suke matsawa arewa maso yamma zuwa Mykolaiv. Kazalika dakarun Rasha sun bude wuta a kan mutanen da ke zanga-zangar kyamar mamayar da ake yi musu. .

Daliban Najeriya sun yi kira ga gwamnatin kasarsu ta taimaka ta kwashe su daga Ukraine kafin lamura su dagule baki daya. Sun shaida wa BBC cewa suna cikin 'yan kasashen waje na karshe da suka rage a birnin.

" Muna roko cewa muna matukar bukaar barin wannan wuri, abubuwa sun rincabe," a cewar daya daga cikin daliban da ya yi magana da BBC ta wayar tarho. Ba za mu ambaci sunan sa ba saboda dalilai na tsaron lafiyarsa.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana aiki tukuru domin ganin ta taimaka musu. A makon jiya, jami'ai a Moscow sun shaida wa jakadan kasar cewa suna shirin fitar da daliban daga Ukraine inda za a bi da su ta Rasha.

Sai dai hakan bai faru ba kuma daliban sun ce sun dari-darin bi ta Rasha.

Dalibai da dama, ciki har da 'yan kasashen Kamaru, Ghana, Masar, Tunisia da Morocco, sun ce har yanzu akwai sauran abinci a jami'o'insu sai dai galibin kayan masarufi sun kare a kantunan sayar da su.

Wadanda kuma suke da kayan suna sayar da su a farashin da ya ninka ko kuma rubanya.

Temporary beds in a shelter
Bayanan hoto, Daliban suna kwana a gidajen karkashin kasa cikin yanayin tsananin sanyi

"Wasu daga cikin mu da ke zaune a makaranta mun yi sa'a saboda har yanzu akwai abinci da ake kawowa daga gidan sayar da abinci," in ji wani dalibi.

Wani dalibin kuma ya ce dakarun Rasha da ke iko da birnin suna wurga musu abinci da suka hada da kayan marmari da shinkafa da taliya da ruwan sha. Sai dai ana gaya musu kada su karba domin kada a rika yi musu kallon wadanda ake hada baki da su domin yakar Ukraine.

line

Kherson na cikin manyan birane na farko-farko da dakarun Rasha suka mamaye a makon farko da soma yaki kuma tun bayan nan mazauna birnin suke gudanar da zanga-zanga akai-akai.

Abin da ya faru cikin kwana 20 na yaƙin Ukraine
line