Yakin Ukraine: Yaya mutane ke rayuwa a garin da aka yi wa kawanya?

Wani mutum da raunika a yayin da yake kokarin tserewa daga Irpin a Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Fernando Duarte
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC

A daren watan Yulin 2019, abin da Zuhair el Karat ke fata shi ne mawuyacin halin da ya ke ciki, za a dakatar da hare-haren sojojin Rasha da na gwamnatin Syria suka yi a birnin Idlib ba tare da kakkautawa ba.

"Ba mu cika jin ƙarar bom ba a cikin dare, don haka muna fatan samun duk damar da muka samu," kamar yadda El Karat, likita a Syria ya shaida wa BBC.

Matarsa, tana buƙatar tiyata ta haihuwar ɗansu na uku na biyu kuma da aka haifa a yaƙin Syria.

Syria: Ba wuta, ba ruwa ba abinci'

Idlib, Syria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hare-haren Rasha da dakarun Syria a Idlib sun raba mutum miliyan 1.4

Yaƙin ƙwace ikon lardin Idlib, wanda har yanzu yana hannun ikon ƴan tawayen Syria, ya yi ajalin fararen hula sama da 1,600 tsakanin 2019 da 2020, kamar yadda alƙalumman Human Rights Watch suka bayyana.

Sama da mutum miliyan 1.4 rikicin ya raba da gidajensu a wannan lokacin.

A goyon bayanta ga sojin Syria, Rasha ta tura dakaru waɗanda yanzu ake gani bayan abkawa Ukraine.

Dr El Karat da matarsa sun haifi yaya biyu lokacin ƙawanyar Idlib

Asalin hoton, Zuhair el Karat

Bayanan hoto, Dr El Karat da matarsa sun haifi yaya biyu lokacin ƙawanyar Idlib

Birane kamar Kharkiv da Mariupol dukkaninsu na ƙarƙashin ƙawanyar dakarun Rasha, kuma da ke fuskantar barazanar hare-hare.

"Wannan yaƙi ne mummuna," a cewar El Karat. An yi wa matarsa aiki lafiya inda ta haifi yara biyu lokacin ƙawanyar da aka yi wa Idlib, amma ya ce ba ƙaramin tashin hankali ba ne.

"Ya shafe mu matuƙa. Babu wuta ba ruwa ba abinci," kamar yadda Dr El Karat ya bayyana.

"Yanzu Rasha na aikata haka ga ƴan Ukraine.

Ukraine: 'Kana fargabar bom da za a saki zai auka maka'

Roman ya nuna girman ɓarnar da aka yi a Kharkiv
Bayanan hoto, Roman ya nuna girman ɓarnar da aka yi a Kharkiv

Roman ɗan shekara 32 da ke Kharkiv, ɗaya daga cikin birnin da ke fuskantar mamayar Rasha.

Alƙalumman yaƙin na cin karo da juna tsakanin majiyoyin Ukraine da na Rasha. Daga 7 ga Maris, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fararen hula 474 da kuma mutum 801 da suka jikkata.

Ta kuma yi gargaɗin cewa adadin zai ƙaru.

A lokacin da yake magana da BBC ta WhatsApp, Roman ya ce akwai lokacin shi da matarsa sun shafe kwana biyu suna rayuwa a ƙasan wani bene kusa da gidansu, kuma suna tsoron fita domin samun kayan buƙata.

"Muna da shaguna inda mutane za su iya sayen abinci da ruwa, amma dole ka shafe sa'a biyu zuwa huɗu a layi," a cewar Roman.

"Akwai tsoro sosai ka tsaya kan layi yayin da kake jin ƙarar bama-bamai. Kana tsoron bom zai faɗa maka."

Smoke from shelling in Kharkiv

A birnin Mariupol, wanda ya jure luguden wutar Rasha, mazauna birnin sun ce an katse wutar lantarki.

"Babu wuta ba ruwa tsawon kwana biyu kuma ba wani abinci, kamar yadda mazauni yankin Maxim, masanin fasahar sadarwa wanda ke ɓuya a wani gidan kakanninsa ya shaida wa wakilin BBC Joel Gunter a 3 ga Maris.

"Abinci da magani ba a shigar da su a Mariupul a yanzu. Ƙaramar hukumar yankin ta yi ƙoƙarin raba burodi da ruwa amma sun ƙare," in ji shi.

Wahalar ƙarancin kayan buƙata wata babbar barazana ce ga rayuwar fararen hula da aka yi wa ƙawanya, Dr El Karat ya ce fama da raunikan yaki ya sha gaban agajin magaji da ake bukata a Idlib.

"Za mu ga mata da yara da cututtuka da dama kamar ciwon hanta da ƙarancin mai gina jiki," kamar yadda ya bayyana.

Mene ne kawanya a yaƙi?

An kiyasta fararen hula 400,000 suka mutu a birnin Leningrad na Rasha (St Petersburg) lokacin yakin duniya na biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kiyasta fararen hula 400,000 suka mutu a birnin Leningrad na Rasha (St Petersburg) lokacin yakin duniya na biyu

Kawanya na ɗaya daga cikin tsoffin dubarun yaƙi ta sojoji. An daɗe ana amfani da dubarar tsawon shekaru.

Rashawa sun shahara akansa lokacin yaƙin duniya na biyu - birnin Leningrad (yadda St. Petersburg ya kafu a shekarun tsohuwar ɗaular Soviet) ya jure kusan kwanaki 900 na ƙawanyar sojojin Jamus da Finland tsakanin 1941 da 1944, inda aka kashe kimanin fararen hula 400,000.

A 2004, dakarun Amurka sun yi amfani da dubarar yin ƙawanya a luguden wutar da suka yi a Fallujah na Iraƙi, inda mayaƙa ke adawa da kasancewar Amurka a ƙasar.

Amma ƙawanyar da ta fi shahara ita ce ta baya bayan nan da ta faru a Turai tsakanin 1992 da 1996, Saravejo shi ne aka yi wa mafi girma a wannan zamanin.

Lokacin yaƙin Yugoslavia, dakarun Serbia sun yi wa babban birnin Bosnia ƙawanya, waɗanda suka yi ta luguden wuta a ƙoƙarin mutrƙushe abokan gaba.

Tauraruwar fim Vedrana Seksan -tana shekara 16 lokacin da aka yi ƙawanyar kuma ta tuna fargaba da wahalar da suka shiga.

"Yaƙi ne na neman tsira. Mun dogara ne da taimakon agaji, yawanci taliya da shinkafa," kamar yadda ta shaida wa BBC a 2016 lokacin da aka cika shekara 20 da yin ƙawanyar.

Actor Vedrana Seksan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai fitowa a fim Vedrana Seksan ta tsira daga kawanyar a Sarajevo a Bosnia

"Wani lokaci muna samun taimakon abinci daga sojojin Amurka, abincin da ya kai yawan na sojan ɗaya. Amma mahaifiyata za ta raba muna da ni da ita da ɗan uwa na da kakarmu.

Sarajevo: ƙone takalmi don samun ɗumi

Sama da fararen hula 5,000 suka mutu a kawanyar Sarajevo tsakanin 1992-96

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sama da fararen hula 5,000 suka mutu a kawanyar Sarajevo tsakanin 1992-96

Yayin da rayuwa a Sarajevo ta dawo daidai a birnin da aka kai wa hari - mutane na zuwa aiki, misali - ana tunatarwa kan halin da yake ciki.

Sau biyu ana kai wa kasuwar birnin ta Markale hari a 1994 da 1995. Sama da mutum 100 suka mutu yayin da dama suka jikkata.

an ƙiyasta cewa sama da fararen hula 5,400 suka mutu a ƙawanyar da aka yi wa Sarajevo.

Mazana birinin na ƙona duk abin da suka gani domin samun dumi saboda tsananin sanyi, kamar takalmi da tufafi da kone tayun mota.

Kawanyar Sarajevo ita ce mafi girma a tarihi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kawanyar Sarajevo ita ce mafi girma a tarihi

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga ƙawanyar, ƴar jarida Aida Cerkez ta aika saƙo ga mutanen Ukraine a cikin wata buɗaɗɗiyar wasika da ta aika wa BBC.

"Za ku ji yunwa da ƙishirwa da sanyi da kuma ƙazanta. Za ku rasa gidajenku da abokai da kuma ƴan uwa. Za ku fita hayyacinku ku cire tsammani," kamar yadda Cerke ta rubuta.

"Amma ina faɗa maku: za ku jure kamar yadda muka yi. Ya kamata ace na mutu amma na tsira."

"Zan fita da jikoki mu motsa kafa a gobe," kamar yadda ƴar jaridar ta bayyana.

Faɗawa yara dalilin da ya sa mutane da dama suka mutu

A boy walks through rubble in the Iraqi city of Fallujah in 2004

Asalin hoton, Getty Images

Aida Cerkez ta tabo tasirin ƙawanya ga rayuwa.

Wahalar ta fi shafar yara ƙanana, in ji ta.

Bayan watanni na ruwan wuta a Idlib, Dr El Karat da matarsa sun koma suna ƙara yawan karar talabijin domin ɗauke hankalin yara daga ƙarar hare-haren bama-bamai.

Amma ya ce babu yadda za su iya faɗawa ƴaƴansu dalilin da ya sa ba za su iya ganin jida ba (kakarsu)

"Na rasa mahaifiyata, da ɗan uwana da ƴar uwata a yaƙin," in ji shi, muryarsa tana rawa.

"Amma muna son mu rayu don ƴaƴanmu."