Dokar zaɓen Najeriya: Mece ce makomar ministocin Buhari da ke son tsayawa takara?

Asalin hoton, State House
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Sakamakon watsi da buƙatar Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da 'yan majalisar dokokin ƙasar suka yi na cire wani sashe daga sabuwar dokar zaɓe, alamu na nuna cewa wasu daga cikin ƙusoshin gwamnatin tarayya da na jihohi na cikin ruɗani.
Dukkanin zaurukan majalisun tarayyar biyu - ta wakilai da ta dattawa - sun ƙi amincewa da gagarumin rinjaye su gyara sashe na 84(12) da ya tanadi cewa wajibi ne masu riƙe da muƙaman siyasa su ajiye aikinsu kafin su iya jefa ƙuri'a a zaɓen jam'iyyu ko kuma a zaɓe su.
Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci Buhari, da Babban Lauyan gwmnatin tarayya kuma Ministan Shari'a (Antoni Janar), Abubakar Malami, da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan kar su sauya sashen dokar.
Da yake bayar da umarnin a ƙarar da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta shigar, Mai Shari'a Inyang Ekwo ya ce dokar zaɓen ta zama cikakkiyar doka kuma ba za a iya sauya ta ba tare da bin tsarin doka ba. Sai dai Ahmad Lawan ya ce kotun ba za ta hana su yin aikinsu na majalisa ba.

Asalin hoton, State House
Yayin da suke jefa ƙuri'a a zaman majalisar na ranar Laraba, ba a ga bambancin siyasa a tsakaninsu ba kamar yadda aka saba gani idan ɓangaren zartarwa ya aike da wata buƙata, inda 'yan APC ke mara baya su kuma 'yan PDP su yi adawa.

Mece ce ma'anar sashen kuma su wa zai shafa?
Sabuwar dokar da aka yi wa laƙabi da Electoral Act 2022, ta sauya da kuma shigar da sabbin abubuwa da dama da za su sauya yadda ake gudanar da zaɓuka a Najeriya.
Daga cikin manyan tanade-tanaden akwai maganar masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara ko kuma jefa ƙuri'unsu a zaɓukan jam'iyyu a matsayinsu na wakilai ko kuma daliget a Turance.
Sashe na 84 (12) ya ce: "Babu wani mai riƙe da muƙamin siyasa a kowane mataki da zai zama wakili (daliget) ko kuma a zaɓe shi a wurin wani taron jam'iyyar siyasa domin fitar da wani ɗan takara."
Shige da ficen da wasu 'yan siyasa a gwamnatin Buhari ke yi na nuna cewa suna neman tsayawa takara a muƙamai daban-daban, ciki har da shugabancin ƙasa, waɗanda kuma tanadin dokar zai shafe su.
Daga cikin waɗanda rahotanni ke cewa suna shirin yin takarar kujeru daban-daban sun haɗa da Ministan Ayyuka da Gidaje Raji Fashola, da Ministan Shari'a Abubakar Malami, da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, da Ministan Ƙwadago Chris Ngige.
Kazalika tanadin dokar zai shafi 'yan siyasa a jihohin ƙasar 36 har da Abuja.
Sai dai wasu masu sharhi na cewa tanadin dokar ya ci karo da tanadin Kundin Tsarin Mulki na 1999 da ya umarci masu riƙe da muƙaman siyasa su ajiye muƙaman kwana 30 kafin zaɓe.
A gefe guda kuma, hukumar zaɓe ta INEC ta ce wajibi ne jam'iyyu su gudanar da zaɓukan fitar da gwani daga 4 ga watan Afrilu zuwa 3 ga watan Yuli na 2022.
Hakan na nufin saura wata tara ke nan kafin gudanar da babban zaɓen da za a fara a watan Fabarairun 2023. Ma'ana duk wani mai rƙe da muƙamin siyasa da ke son tsayawa takarar zai sauka daga muƙaminsa aƙalla wata tara ke nan kafin zaɓe.
Sai dai dokar zaɓen ba ta bayyana wani takamaiman lokaci ba da mai neman takara zai ajiye muƙamin nasa.

Me Buhari ya nemi 'yan majalisar su yi?

Asalin hoton, State House
Idan ba a manta ba, a ranar Juma'a 25 ga watan Fabarairu Buhari ya saka wa dokar hannu bayan shafe kusan kwana 25 a hannunsa "yana nazari".
Shugaban ya yi hakan ne da zimmar 'yan majalisar za su gyara sashen na 84 daga baya, kamar yadda ya buƙata.
Da yake magana yayin saka wa dokar hannu, Buhari ya ce "ya kamata a yayata cewa dokar ta tanadi abubuwa masu amfani da za su kawo a gyara a zaɓukan Najeriya," amma kuma "akwai abubuwan da ba za a yaba wa ba".
A cewarsa: "Sai dai ba za a yabi wani sashe ba a cikin dokar, wanda ya tanadi saɓanin abin da kundin tsarin mulki ya ƙunsa kuma suka ci karo.
"Sashe na 84 (12) ya tauye wa masu riƙe da muƙaman siyasa haƙƙinsu na jefa ƙuri'a ko kuma a zaɓe su a tarukan jam'iyya na zaɓen fitar da gwani, musamman a lokutan da za a yi tarukan fiye da kwana 30 kafin babban zaɓe.
"Abu ne mai muhimmanci mu sani cewa, abin da kundin tsarin mulki ya tanada game da masu muƙaman siyasa kawai shi ne waɗanda jam'iyyu suka zaɓa [a matsayin 'yan takara] ko dai su ajiye muƙaman nasu ko su janye [daga takarar] ko kuma su yi ritaya aƙalla kwana 30 kafin babban zaɓe."
Buhari ya ƙara da cewa "na saka hannu kan dokar nan tare da buƙatar majalisar tarayya ta sake yin gyara da zai dace da tsarin mulki ta hanyar goge sashe na 84(12)".

Wannan ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya - Masana
"Idan kika kula wannan ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya, saboda ko a lokacin Shugaban Ƙasa Shehu Shagari sai mutum ya sauka daga muƙaminsa kusan wata shida kafin zaɓe," a cewar Farfesa Abubakar Sadik Abba, malamin a sashen kimiyyar siyasa na jami'ar Abuja.
Farfesan ya ƙara da cewa sashe na 84 zai taimaka wajen gudanar da sahihin zaɓe a Najeriya.
"Ina goyon bayan wannan sashe ne saboda a lokacin ne za a bai wa dukkan 'yan takara dama iri ɗaya a lokacin zaɓen fitar da gwani. Idan mutum na takara zai ji cewa ba da mutumin da ke riƙe da kujerar yake yi ba.
"Kuma zai rage ɗaukar kuɗin gwamnati wajen yi wa wanda ke kan mulki hidima.
"Haka nan, 'yan adawa za su ji cewa suna da ƙwarin gwiwar cin zaɓe ba tare da wani ya murɗe musu ba."

Duk da cewa waɗannan manyan ministoci na gwamnatin Shugaba Buhari ba su bayyana aniyarsu ta yin takara ba, idan har ta tabbata hakan za a samu gagarumin sauyi a gwamnatin.
Akasarin ministocin gwamnatin sun fara ne tun wa'adin farko na gwamnatin a 2015, kuma Malami da Amaechi da Fashola da Ngige na cikinsu.











