Nasir El-Rufai: Abin da ya sa za mu sayo jirage marasa matuka daga Turkiyya

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ya ce shi da wasu gwamnonin yankin suna shirin sayo jirage marasa matuka daga Turkiyya domin magance matsalar 'yan bindiga da ta addabi yankin.

Ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa.

Ya kara da cewa matsalar hare-haren 'yan fashin daji na dada kamari a shiyyar kuma kasar ba ta da isassun jami'an tsaron da ke iya magance ta.

Hakan ne ya sa, a cewarsa shi da wasu gwamnonin jihohi biyar na yankin suka yanke shawarar shigowa da jirage marasa matuka wadanda ake dora musu makamai da ake iya sarrafawa daga nesa daga kasar domin taimaka wa sojojin saman Najeriya wajen murkushe su.

"Gwamnatin Turkiyya tana da wasu drone [jirage marasa matuka] masu daukar bam da rokoki, kuma mu gwamnatocin wadannan jihohi guda shida dama mun yi shiri za mu je Turkiyya mu zauna da shugabannin kamfanonin kasar mu sayo su [jirage marasa matuka], mu bai wa sojojin saman Najeriya su yi amfani da su,"in ji Gwamna El-Rufai.

Gwamnan ya ce matsalar ta'addanci ta zarta duk yadda ake tunani kuma 'yan bindiga suna samun makudan kudade don haka akwai bukatar a yi musu kwaf daya domin kawar da matsalar.

Ya ce sun san inda 'yan bindigar suke zaune amma "abin da ya hana a kai musu farmaki shekarun nan shi ne rashin samun damar a kira su 'yan ta'adda kamar yadda aka yi wa Boko Haram...amma tun da yanzu kotun tarayya ta ce sojoji za su iya kashe su ba tare da an ce an kashe farar hula ba."