Rikicin Ukraine: Russia ta bai wa dakarunta umarnin shiga gabashin Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bai wa dakarun kasar umarnin shiga yankuna biyu na gabashin Ukraine da ke hannun 'yan tawaye, bayan ya amince da su a matsayin kasashe masu zaman kansu.

Rasha ta ce dakarunta za su yi aikin wanzar da "zaman lafiya" a yankunan Donetsk da Luhansk da da suka ayyana samun 'yancin kansu.

Sai dai Amurka ta ce "shirme ne" a kira wannan aiki na wanzar da zaman lafiya, tana mai cewa Rasha tana neman takalar yaki ne kawai.

Ynakunan biyu suna hannun 'yan tawayen da Rasha ke goyon baya wadanda suka dade suna yakar dakarun Ukraine tun 2014.

Shugaban Ukraine ya ce kasarsa "ba ta tsoron komawa da kuma komai".

A wani jawabi da ya gabatar ta talbijin da talatainin dare, Shugaba Volodymyr Zelensky ya bukaci "tallafi na karara kuma mai amfani" daga kawayensu na duniya.

"Yana da matukar muhimmanci a yanzu mu san su wane ne abokanmu na hakika, da kuma wadanda suke magana ta fatar baki kawai," in ji shi.

Wasu bidiyo da aka fitar da tsakar dare sun nuna motocin sojin Rasha suna nufar yankunan.

A wani taron gaggawa da kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar, Jakadiyar Amurka a Majalisar, Ambassador Linda Thomas-Greenfield ta yi watsi da ikirarin Rasha cewa dakarunta za su yi aikin "wanzar da zaman lafiya", tana mai cewa: "Mun san abin da suke so".

Ta ce matakin Rasha na amincewa da Luhansk da kuma Donetsk a matsayin yankuna masu cin gashin kansu wani yunkuri ne na mamaye Ukraine.

Daga bisani wani ministan Birtaniya Sajid Javid ya ce: "Za mu iya cewa an soma mamaye Ukraine".

A shekarun baya bayan nan, an bai wa dimbin mazauna Donetsk da Luhansk fasfo din kasar Rasha.

Tun makon jiya ake kwashe mata da kananan yara da kuma tsofaffi mazauna yankunan da ke hannun 'yan tawaye zuwa Rasha.

A wani jawabi da ya kwashe awa daya yana gabatarwa ranar Litinin, Mr Putin ya ce Ukraine wani bangare ne na tarihin kasarsa, sannan ya bayyana gabashin Ukraine a matsayin "dadadden yankin Rasha".