Bala Muhammad: 'Zan buga da duk wanda ya fito takarar shugaban Najeriya a 2023 ban da Jonathan'

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhamamd ya ce a shirye ya ke ya ƙalubalanci duk wanda ya fito takara a zaɓen shugabancin kasa na 2023.
Gwamnan wanda ke shaida hakan a lokacin tabbatarwa BBC da anniyarsa ta tsayawa takara ya ce baya shaƙƙun kowa kuma zai fafata da duk wanda ya fito neman kujerar shugabanci Najeriya.
Sanata Bala wanda ya kasance ɗaya daga cikin wadanda ake ganin suna hankoron wannan kujerar a inuwar babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, ya ce muddin jam'iyyar na son yin adalci to kamata ya yi ta tsaida ɗan takararta daga arewacin ƙasar.
Kalaman gwamnan na zuwa ne bayan wata ganawar sirri da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonthan kan batun takararsa, da ma rade-radin da ake yi cewa shi ma tsohon shugaban ka iya sake neman shugabancin kasar a zaben na gaba.
Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi, ya ce gwamnonin jihohin kudancin Najeriya na jam'iyyar PDP ba su da hujjar cewa sai jam'iyyar ta fitar da dantakararta daga kudu.
Ya kuma ci gaba da cewa wannan dalilin ne ma ya sanya ya je wurin tsohon maigidansa Goodluck Jonathan domin shaida ma sa halin da ake ciki ya kuma ba shi goyon baya dari bisa dari.
Sannan ya ce baya ga shi zai kuma je wurin tsofaffin shugabannin kasa da sarakuna da malamai da duk wanda ya dace, domin su bashi shawara kan wannan aniya ta shi.
'Tsakani na da tsohon shugaba Goodluck'
Gwamnan Bauchi ya ce babu shaka a tattaunawarsa da tsohon shugaba Goodluck ya shaida masa cewa ana tuntubarsa kan wannan aniya.
Sai dai ya shawarce shi cewa kar hakan ya sanya shi janyewa daga aniyar tsayawa takarar a zaben 2023, domin kuwa tamkar dan shi ne ya ke neman wannan kujera.
Sai dai kuma gwamnan ya ce ya mayarwa tsohon shugaban da martani cewa, mudin ya fito takarar to shi a matsayinsa na ɗa ba zai iya kalubalantarsa ba don haka zai ajiye matsayarsa ya yi masa biyayya.
''Amma na shaida ma sa matukar zai tsaya takara to ni ba zan tsaya ba, ko da a kowacce jam'iyya ce ba lallai sai APC ko PDP ba, girmamawa da kyautatawa da irin zaman lafiyar da muka yi da shi a lokacin yana shugaban kasa ba za su bar ni tsayawa takara ba matukar zai tsaya,'' in ji Sanata Bala.
Sai dai kuma Sanata Bala ya shaida cewa duk da cewa babu wanda zai hana shi tsayawa takara akwai wadanda ya ke jin nauyi a siyasa kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Asalin hoton, AFP
A cewar gwamnan "idan 'yan Najeriya suka ce shi (Atiku) suke so zan mara musu baya, amma sauran mutanen da za su fito to za mu kara har sai Allah ya ba mu nasara".
''Muma ina ganin mun kawo lokacin da zamu bada gudummawa da ikon Allah, mu nemi mutane a kuma ba mu damar da za mu magance matsalolin da ke addabar yankinmu ta tsaro, da talauci, da sauran abubuwan da suke addabar Najeriya.
Mu na da mutane, muna da sa ni, mun yi rawar gani dan haka yanzu ma zamu shiga a dama damu domin samun maslaha.''
Karin haske
Tun farkon wannan shekarar aka fara kada gangar siyasa a Najeriyar da kuma cece-kuce kan shiyyar da ya kamata dan takarar shugaban kasa ya fito.
Akwai masu ganin arewa ya dace arewa ta kara wani wa'adin, wasu kuma na ganin adalci ne a mika mulkin ga shiyyar kudu maso kudancin Najeriyar a wannan karo.
Gwamna Bala ya kasance mutum na baya-bayanan da ke bayyana aniyarsa ta tsayawa takara yayin da ake gabar tirka-tirkar siyasa gabanin manyan zabukan shekara mai zuwa.
Kafin wannan lokaci an samu mutane irinsu tsohon gwamnan Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da shi me ya ce a shirye yake ya shiga wannan fafatawar.











