Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Ukraine: Abubuwan da Macron da Putin suka tattauna
Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron ya ce kwanaki masu zuwa za su zama masu muhimmanci wajen yayyafa ruwan sanyi a kan rikicin Ukraine, bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Putin ya ce an samu ci gaba a yayin tattaunawarsa ta farko da wani shugaban yammacin duniya a Moscow tun bayan da aka girke dakarun a kan iyakokin Ukraine.
Rasha ta yi watsi da batun cewa tana shirin kutsa wa Ukraine.
Sai dai shugabannin ƙasashen yammacin duniya suna ƙara nuna damuwa kan yiwuwar ɓarkewar rikici.
Jami'an Amurka a ranar Lahadi sun ce Rasha ta girke kashi 70 cikin 100 na dakarun da ake buƙata don kutsawa.
A ranar Litinin, Shugaba Joe Biden ya yi barazanar rufe wani muhimmin bututun iskar gas na Rasha zuwa Jamus idan har Moscow ta kutsa Ukraine bayan wata ganawa da ya yi da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a Washington.
Shi ma Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya nuna alamar goyon bayansa kan sanya takunkuman. A wani rubutu a Jaridar The Times a ranar talata, ya ƙara da cewa Birtaniya na duba yiwuwar aike dakarun rundunar sojin sama da jiragen ruwan yaƙi zuwa yankin.
Ƙasashen yammacin duniya tuni suka yi watsi da buƙatun Rasha, da suka haɗa da cewa a cire Ukraine daga ƙawancen rundunar tsaro ta Nato, da kuma cewa za ta rage yawan sojojinta a gabashin Turai.
A maimakon haka sai suka bayar da shawarwari kan sauran batutuwan sasantawar, alal misali tattaunawa kan batun rage yawan makaman nukiliya.
Shugaba Macron, wanda ya yi magana da Shugaba Putin na tsawon sa'a biyar na cin abincin dare da ya haɗa da naman karkanda da dankalin Hausa da ƴaƴan itatuwa kamar blackberries, ya shaida wa manema labarai cewa kwanakin masu zuwa za su kasance na "yanke shawara" da "buƙatar tattaunawa mai zurfi da za mu yi a tare".
Shi ma Shugaba Putin na Rasha ya ce wasu daga cikin buƙatun Shugaba Macron "za su iya zama silar ɗaukar matakai na gaba", yana mai bayyana cewa "sai dai mai yiwuwa ya yi wuri a fara maganar".
Shugabannin biyu za su sake tattaunawa bayan shugaban Faransar ya je birnin Ƙib (Kyiv) a ranar Talata don tattaunawa da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine.
Daga baya Mista Putin ya sake nanata gargaɗinsa na farko cewa dole Ukraine ta shiga cikin ƙawancen Nato ta kuma sake ƙoƙarin ƙwace yankin Crimea - wanda Rasha ta ƙwace ikonsa shekara takwas da suka wuce da ƙarfi, abin da ka iya jefa ƙasashen Turai cikin wannan tarkon rikicin.
"Kuna son Faransa ta yi yaƙi da Rasha?" ya tambayi manema labarai. "To abin da zai faru kenan. Kuma ba za a samu wanda zai yi nasara ba."
A Washington kuwa, shugaban gwamnatin Jamus Scholz ya shaida wa manema labarai cewa yana da muhimmanci "Rasha ta gane cewa abubuwa da dama ka iya faruwa fiye da yadda suke tunani", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
A ziyararsa ta farko zuwa Washington tun hawansa mulki da kuma sukar da ake yi masa kan martaninsa kan rikicin Ukraine, Mr Scholz ya ƙara da cewa Amurka da Jamus "kansu a matuƙar haɗe yake" kan batun takunkuman da za a sa wa Rasha idanhar ta kusa Ukraine.
Ya ce "za mu bi waɗannan matakan kuma za su zama masu matuƙar, matuƙar tsauri ga Rasha".
Kazalika, ƙofarsa a buɗe take don tattaunawa kan batun bututun iskar gas na Nord Stream 2 fiye da Shugaba Biden, wanda ya ce Amurkan za ta kawo ƙarshen bututun iskar gas mai cike da ce-ce-ku-ce - wanda zai nunaka fitar da gas ɗin da Rasha ke yi zuwa Jamus - "idan har Rasha ta kutsa Ukraine".
Mr Biden bai ba da taƙamaimiyar amsa ba a lokacin da aka tambaye shi kan yadda zai yi hakan, sai ya ce: "Na muku alkawari za mu iya yin hakan."
An shafe shekara biyar ana gina bututun iskar gas na Nord Stream 2 mai tsawon kilomita 1,225 wanda ya lashe kuɗi har dala biliyan 11.
Sai dai har yanzu bai fara aiki ba, bayan da masu tsara dokoki suka a watan nuwamba suka ce hakan bai yi daidai da dokar Jamus ba suka kuma dakatar da amincewa da shi.