Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan ci-rani: 'Mamban cocinmu ne ya yaudare ni zuwa neman kuɗi Libya'
Hukumar yaƙi da bautarwa da fataucin bil adama a Najeriya ta NAPTIP ta ce ta ceto wasu mata da maza 'yan kasar 61 da aka yi yunƙurin safarar su zuwa Libya ta Jamhuriyar Nijar.
Ɗaya daga cikin matan da hukumar hana yaƙi da bautarwa da fataucin bil adam ta Najeriya ta kuɓutar a kan hanyar kai su kasar Libya, ta ce malamin cocinsu ne ya yaudare ta da zummar samar musu aiki mai inganci a Libya.
''Wani mamban cocinmu ne ya ce na zo zai mini hanyar aikin aikatau a ƙasar Libya, daga nan sai na hau motar zuwa Kano, ya kuma haɗa ni da wasu mutane da za mu yi tafiyar tare da su.
Da zan baro gida, ban faɗawa 'yar uwata inda za ni ba, na dai shaida ma ta zan je wurin wata ƙawata. Ban san tafiyar haka ta ke ba, cewa suka yi za mu wuce wata hanya babu damuwa, ina nadama, mun dauki kwanaki ba tare da mun yi wanka ba.
Ina son na ja hankalin matan da aka sanya su cikin kasada, su maida hankali su san inda za a nufa da su, babu abin da zai sanya na sake yin wannan kasadar," in ji ta.
Shi ma wani mutum da ke cikin maza 29 da aka kubutar, ya bayyana cewa da aka dauke su daga jihar Kano, sai aka nufi Katsina da su tun daga gidan da aka ajiyesu ya fara nadamar yin tafiyar.
''Hanyar da aka bi damu ban san haka ta ke ba, daga Katsina aka tsallaka da mu jamhuriyar Nijar, daga nan aka ajiyemu a wani wuri da ban ma san inda muke ba, jeji aka ajiye mu.
Na yi da-na-sani, duk wanda aka ce za a kai shi kasar waje, ya tabbatar an bi hanyoyin da suka dace, kama daga mallakar Fasfo din tafiya da sauransu," a cewarsa.
Aikin ceto
Hukumar ta NAPTIP ta sami nasarar ceto su ne bayan da jami'an 'yan sanda Jamhuriyar Nijar, suka gano su a lokacin da suke sintiri a cikin wani daji a ƙasar.
Mutanen da aka ceto 'yan shekaru 17 zuwa 50, sannan 29 daga cikinsu maza ne, sai kuma mata 32.
Jami'in hukumar NAPTIP shiyyar jihar Kano, Mista Yahona Haruna, ya shaidawa BBC cewa mutanen sun fito ne daga jihohin Kano da Edo da Imo, Ondo, Osun, Lagos, Delta, Kwara, Akwa Ibom, Ogun, da kuma Ebonyi.
Yohana ya ce, masu safarar mutanen su na samun makudan kudi a harkar, dan haka ne suke amfani da kalaman yaudara da romon baka, domin jan hakalin mutane, su kuma kwaɗaita musu irin kuɗin da tagomashin da za su samu idan sun isa ƙasar da aka nufa da su.
Sakamakon ƙaruwar fataucin bil adama a Najeriyar, tuni hukumar NAPTIP ta kafa da kuma kaddamar da wasu kwamitoci na kar ta kwana a wasu daga cikin jihohin kasar.
Ciki har da Kano da Jigawa da Kaduna da Katsina don shigar da al'umma cikin yaƙi da fataucin dan Adam da cin zarafin al'umma da ke kara hauhawa a yankin.