Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Guinea-Bissau: Hukumomi sun ce mutum 11 aka kashe a yunƙurin juyin mulki
Hukumomi a Guinea Bissau sun ce zuwa yanzu mutum 11 aka tabbatar sun mutu a yunƙurin juyin mulkin da aka yi ranar Talata, wanda bai yi nasara ba.
Rahotanni sun ce wadanda suka rasun sun hada da sojoji da farar hula, yayin da kuma ake gudanar da wani gagarumin bincike na gano 'yan bindigar da suka yi shirin kifar da gwamnatin.
A halin da ake ciki dai al'amura sun koma yadda suke a babban birnin kasar ta yammacin Afirka, Bissau, inda aka bude shaguna da bankuna.
Sai dai sojoji na ci gaba da sintiri a titunan birnin, abin da ke zama wata matashiya ta alamar abin da ya faru na neman hambarar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissoco Embaló.
Haka kuma unguwannin da ke kusa da fadar gwamnatin kasar na ci gaba da kasancewa a rufe, inda a nan ne 'yan bindigar da ba a sansu ba suka kewaye ranar Talatar, aka rinka ba-ta-kashi tsakaninsu da jami'an tsaro tsawon sa'a biyar.
An ce shugaba da firaministansa Nuno Gomes Nabiam suna wani taro na majalisar zartarwa a lokacin da aka kai harin.
A wata sanarwa da ya fitar daga baya, Shugaba Umaro Sissoco Embaló ya ce maharan watakila masu hada-hadar miyagun kwayoyi ne, wadanda ya ce ba sa jin dadin irin matakan da gwamnatinsa ke dauka na murkushe harkar.
Ita dai kasar ta Guinea Bissau ta zama wata cibiya ta masu safarar hodar Iblis, inda suke bi ta nan su yi safararta tsakanin Amurka ta Kudu da Turai.
A ranar Alhamis din nan 03 ga watan Fabrairu, 2022 shugabannin kasashen yammacin Afirka za su gana a Ghana inda za su tattauna batun yawan juyin mulkin soja da ake samu yanzu a yankin.
A cikin shekara biyu da ta wuce sojoji sun karbe mulki a Mali da Guinea da Burkina Faso da kuma Chadi.
Bayan yunƙurin
Shugaban kasar ya fito ya ce ya tsira daga yaunƙurin juyin mulkin da sojoji suka yi bayan an yi ta harbe-harbe tsawon awa biyar.
Umaro Cissoko Embaló ya ce maharan sun yi yunƙurin kashe shi da kuma ministocinsa baki ɗaya a fadar gwamnati.
Shugaban ya ce an shawo kan matsalar, yana mai siffanta ta da "harin da bai yi nasara ba a kan dumukuraɗiyya".
Wata majiyar tsaro a lokacin harin da ba nemi a boye sunanta ta shaida wa BBC cewa 'yan bindiga sanye da kayan gida ne suka buɗe wuta kuma har an kashe wani ɗan sanda.
Ƙungiyoyin yankin Afirka ta Yamma sun bayyana yunƙurin a matsayin na juyin mulki sannan suka yi kira ga sojoji da su koma barikinsu.
Ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya talauci a duniya, Guinea-Bissau wadda Portugal ta yi wa mulkin mallaka a baya ta fuskanci yunƙuri ko kuma juyin mulki sau tara tun daga 1980.
Baya ga tarin bashi da take fama da shi da kuma tattalin arzikin da ya dogara sosai kan tallafin ƙasashen waje,
Bayan Mista Embalo ya yi nasara a zaɓen watan Disamban 2019, ya fuskanci turjiya daga majalisa kafin ya shiga ofis a Fabarairun da ya biyo baya.
Alamu na nuna cewa juyin mulki na dawowa
Daga Mayeni Jones, wakiliyar BBC a Afirka ta Yamma
Da alama juyin mulki na sake dawowa a Afirka ta Yamma da ta Tsakiya. Cikin shekara biyu da suka wuce, an samu juyin mulki a ƙasashen Mali da Chadi da Burkina Faso da Guinea, sai kuma Sudan.
Yayin da lamura ke fitowa fili a Guinea-Bissau, ƙungiyar sa ido a yankin ta Ecowas, da ma Amurka, sun yi Allah-wadai.
Sai dai abin da wannan juyin mulkin ke nunawa shi ne, ba wani abu da ƙasashen waje za su iya yi don hana faruwarsa.
Ecowas - ƙungiyar tattalin arziki ta Yammacin Afirka - ta saka wa Mali da Burkina Faso takunkumi, amma hakan bai hana juyin mulkin faruwa ba a yankin. Shekara 10 da ta gabata, ita ma Guinea-Bissau ta fuskanci takunkumi.
Cikin wata hira a baya-bayan nan, shugaban Ecowas ya ce takunkumin ya yi amfani a kan Guinea-Bissau saboda ya taimaka wajen dawowar zaman lafiya. Da alama wannan maganar a yanzu ta yi wuri.
Sojoji na amfani da cin hanci a matsayin dalilin da ya sa suke ƙwace mulki. A Burkina Faso da Mali, wasu 'yan ƙasar sun ji daɗi tare da yin murnar juyin mulkin da suka yi.
Sai dai masu sharhi na nuna damuwa kan ci-gaban da aka samu na dumukuraɗiyya cikin shekara biyu da ta gabata na taɓarɓarewa sannan ana fargabar Afirka za ta sake amsa sunanta na 'Magamar Juyin Mulki'.