Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abdulrahman Muhammad Auwal: 'Wasiyyar da mahaifina Sheikh Albaniy ya bar mana'
Latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Abdulrahman Muhammad Auwal:
Babban dan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albaniy, ya ce babbar wasiyyar da mahaifinsu ya yi wa iyalansa ita ce su mayar da hankali wajen neman ilimi.
A wata hira ta musamman da BBC Hausa yayin da ake cika shekara takwas da kisan malamin, Abdulrahman Muhammad Auwal wanda aka fi sani da Abu Huraira, ya ce rayuwarsu ta "kasance cike da kalubale na rashin mahaifinmu".
"Abubuwan da na fi tunawa [game da shi] su ne kiran da yake yi mu mayar da hankali wajen karatu.
"Ina yawan tuna wadannan kalmomi musamman inda yake cewa ba mu da gatan da ya wuce mu yi karatu; kuma Alhamdulillahi, daidai bakin gwargwado muna kan yi, muna yi kuma," in ji Abu Huraira.
Ya kara da cewa abin da yake yi musu dadi shi ne ganin irin abubuwan alherin da mahaifinsu ya bari na ilimi da dalibai da har yanzu suna koyar da abubuwan da suka koya daga gare shi.
Abdulrahman Muhammad Auwal ya ce maganarsa ta karsher da mahafinsa ita ce lokacin da ya je wurinsa yin bankwana zai koma makaranta.
"Sati daya kafin rasuwarsa na je na same shi na ce masa gobe za mu koma makaranta, ya yi mini addu'o'i; daga nan ne kuma bayan mun rabu, washegari na koma makaranta ranar Asabar kawuna ya kira ni... ya ce ga abin da ya faru, an kashe malam.
"A lokacin na yi kokari na fito da tsakar dare na samu mota na dawo daga makaranta," a cewar Abu Huraira.
A shekarar 2014 wasu mahara suka harbe malamin da iyalinsa lokacin da suke cikin mota suna kan hanyarsu ta komawa gida daga makaranta a birnin Zaria na jihar Kaduna.
An bayyana cewa maharan suna cikin wata mota ne kuma bayan da suka harbe shi da iyalin nasa sai da suka sake janyo shi daga cikin motar suka kara harbinsa don su tabbatar ya mutu.
Sai dai wasu rahotanni sun ce anan take ne uwargidan nasa ta rasu, amma malamin da dan nasa sai bayan an kai su asibitin Wusasa da ke garin na Zaria ne rai ya yi halinsa.