Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zamantakewa: Me ya sa wasu mazan ke muzgunawa ƴaƴa agola?
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 28 din, shirin ya yi duba ne kan zamantakewar agola da uban riƙonsa.
Agola, ka rasa laifin da ya yi wa uban riƙonsa da har zai sa ya dinga kyara da ƙyamatarsa a wasu lokutan.
Duk da ɗumbin lada da ake hasashen za a samu a riƙon ɗa, musamman mara cikakken gata ko maraya, sai ka ga riƙon agola na zamewa wasu tamkar an ba su riƙon dabba.
A da a kan yi tunanin mata ne kadai ke yi wa 'ya'yan mijinsu mugunta, amma a wasu lokutan da dama a kan samu maza ma masu yi wa 'ya'yan matansu irin wannan muguntar.
Ka auro uwarsa, wataƙila dama sharadin auren shi ne za ka riƙe mata ɗan, wataƙila don shi maraya ne kuma ta rasa mai riƙe shi a danginta ko na ubansa.
Mun sha jin labarin iyayen riƙon da ke muzgunawa agololinsu, sai ka ga ya ritsa ɗan maraya bawan Allah yana zazzare masa ido da nuna masa wuya wato alamar zan yanka ka, ko kuma ya yi ta harararsa babu gaira ba sabar.
Wani fa ɗan ma ba zaman dindindin yake yi ba, zuwa hutu kawai yake wajen uwarsa, amma a hakan ma wani ya ƙi jinin ya buɗe ido ya ga yaron nan.
To me ya sa maza ke wannan ɗabi'a ta ƙin agola ne saboda Allah?
Hajiya Asma'u Sani na daga cikin matan da suka samu kansu a irin wannan taskun na cin muzgunawa ƴaƴansu don kawai suna agola, kuma a cikin shirin na wannan makon ta ba mu labarin halin da ta samu kanta a ciki.
Wasu shirye-shiryen na baya da za ku so
Da yake kuma masu iya magana kan ce da muguwar rawa an ce gwamma ƙin tashi, ke mace ya kamata ki auna sosai kafin ki tafi da ɗanki agolanci wani gidan, don gudun abin da ka iya sosa maki zuciya ko kuma ya jawo matsala a zaman naki.
Idan kuma har tsautsayi ya sa kina cikin wannan yanayi, Hajiya Asma'u ta ba ki shawarar abin da ya dace ki yi.
Ɗa dai na kowa ne, bawa sai mai shi, idan har ka san kana son uwarsa tsakani da Allah, to ina ga in dai kana da hali, shi ma za ka iya riƙe shi.
Ba a ce dole sai ka so shi kamar ɗan cikinka ba, ba kuma a ce dole sai ka daidaita tsakaninsa da ƴaƴanka ba, amma dai ka nuna jin ƙai da ɗan adalci a riƙonsa ba tare da hantara ba ma abin a yaba ne.
Ba wanda ya san gobe sai Allah, ba ka san kai ma wata rana ko ɗanka ya yi agolancin a wani gidan ba, ka ga idan ka yi da kyau, ko bayan ranka zuri'arka ma za su ga da kyau.
Idan kuma ka san kawai ba za ka iya rike agola ba ne, to kar ka yaudari uwarsa ka aure ta. Kawai ka bar ta wanda ya ga zai iya sai ya aure ta.