Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan zubar dusar kankara a Saharar Algeria
An samu zubar dusar kankara a Saharar da ke arewa maso yammacin Algeria a yayin da yanayin sanyi ya yi tsananin da hatta ruwa ma ya daskare.
Ga yara da ke garuruwa na kusa irin su Mekalis, ta kasance wata sa'ida daga tsananin zafin ranar da ake fuskanta a yankin.
Dusar kankarar ta yi wasu layuka, masu ban sha'awa a rairayin Sahara.
Dusar kankarar ta kuma dan rufe tarin rairayi - wanda mafi yawancin lokuta ake yin wasan zamiya.
Kankarar da ta zuba a garin Ain Sefra - wanda ake yi wa lakabi da mashigar Hamadar Sahara - ba ta yi yawa ba.
Yanayi a garin, wanda ke kewaye da tsaunuka Atlas, ya yi kasa da maki 2 a cikin dare uku amma hakan bai dara maki da yawa ba a yanayin sanyin da aka saba da shi a yankin a duk shekara, a cewar wakilin BBC kan yanayi Nicky Berry.
Ba a yi mamakin zubar dusar kankarar baki daya ba - akwai lokutan da hakan ya taba faruwa a shekarun 2021, 2018 da kuma 2017.
Sai dai dusar kankarar da ta sauka a kan jigayi a watan Disambar 2016 ta bai wa mutane mamaki matuka. Mazauna garin Ain Sefra su ce hakan ne karon farko da ta zuba tun daga 1979, lamari da ke nuna cewa yanzu dusar kankarar tana zuba akai-akai.
Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.