Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
IS ta fitar da wani bidiyo da ya nuna harin da ta yi iƙirarin kai wa a Buratai
Ƙungiyar IS a Najeriya ta saki wani bidiyo da hotuna wadanda ta yi ikirarin cewa suna nuna yadda ta kai hari a wata makarantar sojoji da ke Jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
A yayin harin, ana zargin mutum goma ne suka rasa rayukansu.
Kafafen yaɗa labarai na Najeriya sun ruwaito cewa makarantar da aka kai harin wata Kwaleji ce da ake kira Tukur Buratai Institute for War and Peace inda suka ruwaito cewa an kashe farar hula biyu.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai a kan harin ba kawo yanzu.
An buɗe cibiyar ce a watan Agustan 2020 a ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka na yaƙi da ta'addanci.
Ƙungiyar ta IS ta saki bidiyon ne a ranar 13 ga watan Janairu ta manhajar Telegram.
Wata kafar yaɗa labarai ta IS mai suna Amaq ce ta shirya bidiyon. A jiki, an yi masa take da "Mayaƙan IS a yayin da suka kai hari a Kwalejin yaƙi ta Najeriya da ke garin Buratai a Litinin din da ta gabata".
A bidiyon, an nuna mayaƙan a cikin motocin sojoji ƙirar a-kori-kura waɗanda ake kyautata zaton an ƙwace su ne daga hannun sojoji, inda suka shiga cibiyar sojojin tare da buɗe wuta ta hanyar amfani da manya da ƙananan makamai.
Manyan alluna da kuma ginin ya nuna cewa cibiyar ce ta nazarin yaƙi da zaman lafiya ta Buratai.
Haka kuma daga baya bidiyon ya nuna mayaƙan na IS a gaban ƙofar shiga harabar makarantar amma ba su shiga har cikin ƙuryar makarantar ba.
An nuna yadda mayaƙan suka rinƙa saukar da tutoci da kuma ƙona su. Haka kuma an nuna su a tsaye a gaban motocin sojoji waɗanda suka cinna wa wuta.
Sauran hotunan da aka saka guda takwas sun nuna motocin sojoji waɗanda da alamu ƙungiyar ke son nuna ko ta ƙwace ko kuma ta lalata su.
Duka hotunan an yi musu take da "Daya daga cikin yadda harin da aka kai a Kwalejin sojoji ta garin Buratai ya kasance".
Haka kuma wasu hotunan sun nuna yadda motoci suka ƙone da kuma lalata su, wasu hotunan kuma sun nuna manyan motoci masu sulke waɗanda lafiyarsu ƙalau waɗanda ake kyautata zaton mayaƙan suka tuƙa su.
Ƙungiyar IS ta sha iƙirarin cewa akasarin makamai da kayan aiki na soja da ƙawayen ƙasashen Afrika suka ba nahiyar na ƙarewa ne a hannun mayaƙan jihadin waɗanda suke amfani da su a hare-haren da suke kai wa.