Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Likitoci sun yi nasarar dasa wa mutum zuciyar alade
Likitoci a Amurka sun yi nasarar dasa wa wani mutum zuciyar alade, a irin wannan aiki da ke zaman na farko a duniya, inda mutumin yake murmurewa kwana uku bayan dashen.
Likitoci sun bayyana aikin da cewa gagarumin ci gaba ne da kuma nasara, domin ana ganin a karshe zai kai ga ana amfani da hanyar wajen yin amfani da sassan dabbobi domin yi wa mutane dashe.
Likitocin da suka jarraba wannan sa'a a asibitin Jami'ar Maryland sun ce zuciyar aladen wadda aka yi wa kwaskwarima ta yadda jikin dan adam zai iya karbarta, tana aiki a jikin mutumin kalau, bayan aikin na tsawon sama da sa'a bakwai.
Sun kuma ce zuwa wasu sa'o'i 24 za a iya cire wata na'urar da aka hada wa mutumin da aka yi wa aikin David Bennett, mai shekara 57, da ke taimaka masa.
Aikin ya nuna cewa zuciyar dabba za ta iya aiki a jikin dan adam ba tare da jikin ya ki ta ba a take.
An yi shekaru daruruwa ana bincike da nazarce-nazarce kan yadda za a iya yin irin wannan aiki, to amma a sanadiyyar fasahar da aka gano a baya bayan nan kan yadda za a iya jirkita kwayoyin halitta yadda ake so, ta kai ga samar da sassan jiki na dabbobi da za a iya jirkita halittarsu ta yadda za su iya dacewa da jikin dan adam, ba tare da jikin ya ki karbarsu ba.
Dashen ya kasance wata dama ko hanya ta karshe ta cetar rayuwar Mr Bennett ko da yake ba a san yadda zai karke ba a nan gaba ko zai tsira ko kuma zai rasu.
Likitan da ya jagoranci aikin a ranar Juma'a, Dr Bartley Griffith da ayarinsa sun ce suna da kwarin guiwa abu ne mai kyau ga maras lafiyar.
Ya ce, ''ba mu taba yin wannan a jikin mutum ba, kuma ina ganin mun ba shi zabin da ya fi, a kan ci gaba da maganinsa. To amma ban sani ba rana daya ce mako ne ko wata ko kuma shekara.''
Hukumar da ke sanya ido a kan ayyukan likitoci ta Amurka ce ta ba wa likitocin asibitin Jami'ar ta Maryland wannan dama ta jarraba aikin, bisa dalilin cewa ba makawa mutumin zai mutu, saboda haka aka yi wannan gwaji a kansa, wanda kuma ake ganin ga alama za a dace.
An zartar da cewa ba za a iya yi masa dashe da zuciyar dan adam ba, wanda wannan hukunci ne da likitoci ke yankewa idan jikin maras lafiya ya yi tsanani.
Ga likitocin da suka yi wannan aiki na dashen zuciyar aladen a jikin dan adam, wata babbar nasara ce a binciken shekara da shekaru da ake yi a fannin, wanda kuma zai iya sauya rayuwar mutane da yawa a fadin duniya.
Binciken farko-farko ya mayar da hankali ne kan samar da sashen jikin da ake bukata daga birrai.
A shekara ta 1984 an yi wa wata jaririya(Stephanie Fae Beauclair ko Baby Fae) da aka haifa a Amurka, wadda take da matsala ta zuciya dashen zuciyar gwaggon biri, sai dai bayan kwana 21 da aikin ta rasu.
Ita dai zuciyar da aka dasa wa wannan mutum a yanzu, an ciro ta ne daga alade, wanda aka sauya yanayin kwayoyin halittarsa inda aka cire sinadarin sukari a kwayoyin, sinadarin da zai iya sa jikin mutum ya ki karbar zuciyar idan aka dasa ta.
Yanzu dai idan wannan aiki ya yi nasara a karshe, zai sa likitoci su samu hanyar magance tsananin karancin sassan jiki da ake bukata na dashe.
A yanzu haka dai akwai sama da Amurkawa dubu dari daya da ke jiran a yi musu dashen wani sashe a cikinsu, kuma sama da mutum dubu shida daga cikinsu ke mutuwa a duk rana kafin a samu abin da za a yi musu dashen.