Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Christian Eriksen: Abin da ke jawo bugawar zuciya
- Marubuci, Daga Philippa Roxby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Lafiya
Dan wasan kwallon kasar Denmark Christian Eriksen ya shafe daren shi na uku a asibiti ana yi masa gwaje-gwaje, bayan wani ciwon bugun zuciya a lokacin gasar wasan kwallon kafa ta zakarun Turai ranar Asabar.
Amma har yanzu likitoci ba su da tabbas kan ko me ya sa babu zato babu tsammani zuciyarsa ta tsaya - kuma gano dalilan da suka sa shi ne abu mafi muhimmanci a yanzu.
"Mai shekaru 29 na kokarin ceton rayuwarsa,'' Farfesa Sanjay Sharma, likitan zuciya kuma shugaban kwamitin al'amuran da suka shafi zuciya na kungiyar kwararru a harkar wasan kwallon kafa ya shaida wa BBC.
"Yanzu muna bukatar kokarin gano ainihin abin da ya faru."
Daya daga cikin abubuwan da suka fi haifar da ciwon bugun zuciya shi ne bugawar zuciyar da ba a cika samu ba, kamar yadda kungiyar kula da masu ciwon zuciya ta Birtaniya (BHF) ta bayyana.
Sauran dalilan sun hada da cardiomyopathy - wata cuta da ke shafar tsokar zuciya da ke kuma shafar girman ta, wadda akan yi gado - da kuma acute myocarditis, ko kuma radadin tsokar zuciya.
Yanzu haka za a gudanar da aikin daukar hotunan kwakwaf mai cike da sarkakiya na zuciyar Mista Eriksen don gano duk wani tabo - wani abu da bai cika faruwa ba a gwajin da aka saba yi wa zuciyar 'yan wasan kwallon kafa, a cewar Farfesa Sharma.
Wadannan gwaje-gwaje wajibi ne a Birtaniya, ana yin su a ko wace shekara biyu daga shekaru 16 zuwa 25.
Sukan duba duk wani abu da ba a yarda da shi ba na yadda zuciya take aiki da kuma yanayin tsarin ta - amma duk da wannan namijin kokari na likitoci, wadannan gwaje-gwaje ba su da tabbacin nasara dari bisa dari cewa za a iya gano wasu boyayyun matsaloli.
"Wadannan matsaloli ba su cika nunawa ba a lokacin shekarun matasa ko daga masu shekarar 16 zuwa 25," in ji Farfesa Sharma.
"Ba lallai su nuna ba har sai sun kai shekara 20 zuwa 30."
Wani lokaci samun wasu alamu na daban kan faru a lokacin da 'yan kwallon suke tsakiyar buga wasa, ko kuma za a iya danganta shi da wata rashin lafiya da ba su dade da yi ba wacce ta sa zuciyar ta galabaita.
Idan aka gano matsaloli, wasu za a iya magancewa - amma wasu kan kasance babu waraka.
Ciwon bugun zuciya na faruwa ne idan cikin lokaci kankane zuciya ta daina kai jini jikin dan adam, tare da hana kwakwalwa samun iskar oxygen lamarin da ke sa mutum ya fadi ya suma kana ya daina numfashi.
Tana da bambanci da ciwon zuciya, wanda ke faruwa a lokacin da hanyoyin samun jini zuwa tsokar zuciya suka toshe, yawanci saboda daskarewar jini a daya daga cikin manyan jijiyoyin da ke kai jinin zuwa cikin zuciya.
'Abubuwan da ba su cika faruwa ba'
Ba Eriksen kadai ne dan wasan kwallon kafa da ya taba samun buguwar zuciya ba. A shekarar 2012, wani dan wasan kwallon kafar, Fabrice Muamba, ya yanke jiki ya fadi a filin wasan kuma zuciyarsa ta tsaya cik har na tsawon mintuna 78.
Marc-Vivien Foe ya mutu a lokacin da yake tsakiyar buga wasa ga kasar Kamaru yana da shekara 28, kana tsohon mai tsaron gid na Ingila Ugo Ehiogu, wanda kuma kocin kungiyar wasan kwallaon kafa na Spurs ne, ya mutu a shekarar 2017 yana da shekara 44.
"Tsananin motsa jiki kan saka rayuwar 'yan wasan motsa jikin cikin hadari saboda suna galabaitar da zuciyoyinsu - kana hakan ka iya haifar da babbar matsala," in ji Dakta Zafar Iqbal, shugaban bangaren kula da lafiyar 'yan wasa na kungiyar kwallon kafar Crystal Palace.
Ya kara da cewa: "Amma wadannan abubuwa ne da ba su cika faruwa ba."
Bugun zuciya kan faru ga kowa a kuma ko wane lokaci - ba sai 'yan kwallo ba.
A ko wane mako a Birtaniya, mutane 12 masu shekaru daga 12 zuwa kasa da 35 na mutuwa sakamakon bugun zuciya.
Kana a Birtaniyar a ko wace shekara, ana samun aukuwar bugun zuciya 30,000 a wajen asibitoci - duka masu bukatar taimakon gaggawa na farfadowa, inda akan samu mutane 10 kacal da ke rayuwa.
Zuciyoyin 'yan wasan kwallon kafa kan kasance da girma kana da yin aiki sosai fiye da na sauran mutane, wanda ke saka su zama mafi karanci cikin na masu hadarin kamuwa da sauran matsaloli na zuciya kamar na toshewar jijiyoyin da ke kai jini cikin zuciya, da galibi aka fi samu a tsakanin masu shan taba sigari ko masu cin abincin da babu kiwon lafiya.
Amma idan aka kara wa zuciya wata matsala daga rashin shan ruwa, da zafi da kuma wasu cututtuka za su iya yin mummunan tasiri.
'Ko wace dakika na da muhimmanci'
Dakta Iqbal ya ce yana da matukar muhimmanci cewa a fara yi wa Mista Eriksen aikin farfado da numfashi ta hanyar bubbuga gefen kirjinsa wato (CPR) ba tare da bata lokaci ba, daga nan sai a bi hanyar amfani da na'urar defibrillator mai wayoyin lantarki, wajen farfado da numfashin da ake kira (automated external defibrillator), kuma wata hanya ce da ya kamata kowa ya san yadda ake yi.
Yana so ya ga an kai irin wadannan wayoyi da ake amfani da wutar lantarki wajen zaburar da zuciyar ko wace makarantar sakandae.
Ya ce: "Bata lokaci na ko wane minti daya na rage damar samun rayuwa da kashi 10 bisa dari."
Aikin farfado da zuciyar na CPR ka iya ninka damar ceton rayuwar mutum a wasu lokuta.
"Ko wace dakika na da amfani idan mutum na fama da bugun zuciya - idan kowa ya san yadda ake yi za a iya ceton rayuka da dama," in ji Dakta Sonya Babu-Narayan, wata likitar zuciya kana daraktar cibiyar lura da masu ciwon zuciya ta Birtaniya.
Akan ajiye na'urori masu dauke da wayoyin lantarkin a wuraren aiki da filayen jiragen sama da kuma cibiyoyin taruwar al'umma.
Kowa zai iya amfani da su, kana kwararru sun jaddada cewa babu wata hanya da za a yi amfani da su kuma a yi kuskure.
Na'urar za ta zaburar da zuciya ne kawai idan bukatar hakan ta taso, bayan kai tsaye ta nuna yanayin bugawar zuciyar.