Jihar Kano: Manyan mutane bakwai da rasuwarsu ta girgiza jihar a ƙasa da wata biyu

    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya na ci gaba da alhinin rasuwar wasu fitattun mutane bakwai ƴan jihar da suka riga mu gidan gaskiya a ƙasa da watanni biyu da suka gabata.

Mutanen sun haɗar da ƴan kasuwa da sarakuna da malamai da ƴan siyasa da kuma tsoffin ƴan takarda, waɗanda aka daɗe ana gogayya da su a mu'amalar yau da kullum ta rayuwa.

Alhaji Sani Dangote

Marigayi Sani Dangote

Asalin hoton, ERIC PIERMONT

Bayanan hoto, Marigayi Sani Dangote

A ranar 15 ga watan Nuwamban da ya gabata ne Allah ya yi wa ƙanin mutumin da ya fi arziki a nahiyar Afrika, Aliko Dangote rasuwa.

An gudanar da jana'izar marigayin ne a Fadar mai martaba Sarkin Kano wacce ta cika makil.

Marigayin wanda hamshaƙin ɗan kasuwa ne, shi ne mataimakin shugaban kamfanin Dangote wanda ya yi fice wajen samar da kayan masarufi a nahiyar Afrika.

Ya rasu ne a wani asibiti da ke Amurka, daga bisani aka mayar da gawarsa jihar Kano bayan kwanaki kaɗan inda aka yi masa jana'iza.

An haife shi ne a shekarar 1959, kuma ya rasu ya bar iyali.

Alhaji Sani Buhari

Marigayi Alhaji Sani Buhari

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Marigayi Alhaji Sani Buhari

Gaba kaɗan a ranar 28 ga wannan wata na Nuwamba ne sai shi ma fitaccen ɗan kasuwar nan na jihar ta Kano Alhaji Sani Buhari ya koma ga mahaliccinsa, yana da shekaru ɗai-ɗai har 90 a duniya.

Bayanai sun ce ya rasu ne a Dubai, da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Kafin rasuwarsa dai shi ne mamallakin kamfanin kwangila na Bayajidda Nigerian Limited wanda ke aikin gine-gine da samar da hanyoyi da wasu manyan kamfanoni da dama.

Ɗaya daga cikin kamfanoninsa da ake kira The Standard Construction Limited ne ya samar da cibiyar jigilar kayayyaki ta ma'aikatar tsaron Najeriya da ke Abuja.

Dattijo ne wanda ake matuƙar girmamawa saboda irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban jihar ta Kano da kuma Najeriya baki ɗaya.

Sarkin Ban Kano

SARKIN BAI FAMILY

Asalin hoton, SARKIN BAI FAMILY

Bayanan hoto, Marigayi Sarkin Ban Kano

Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan na ɗaya daga cikin manyan masu riƙe da sarauta a Kano da suka rage a duniya kafin rasuwarsa a ranar 3 ga watan Disamba, na ƙarshen shekarar 2021.

Marigayi Alhaji Mukhtari Adnan ya rasu ne yana da shekaru 95 a duniya a wani asibiti mai zaman kansa da ke jihar ta Kano, inda ya yi jinya.

Alhaji Mukhtar Adnan yana daga cikin masu zaben Sarkin Kano wanda shi kadai ne ya zabi sarakunan Kano guda hudu da suka hada da Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Inuwa da Alhaji Ado Bayero a 1963, da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a 2014 da kuma Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a 2020.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ɗaya ne ya nada shi Sarkin Ban Kano kuma Hakimin Dambatta a shekarar 1954.

An haifi marigayin a watan Janairun 1926.

Ya rasu ya bar 'ya'ya da dama cikinsu har da Dakta Mansur Mukhtar, tsohon Ministan Kudi na Najeriya, wanda kuma a yanzu mataimakin shugaba ne a Bankin Musulunci na Duniya da ke da cibiya a kasar Saudiyya.

An zaɓe shi ɗan majalisar wakilai a jamhuriya ta farko ƙarƙashin jam'iyyar NPC daga 1959 har zuwa 1966 lokacin da sojoji suka yi juyin mulki na farko.

Ya zama mai tsawatarwa a Majalisar Wakilai ta Lagos a jamhuriya ta farko.

Alhaji Ado Gwaram

Marigayi Alhaji Ado Gwaram

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Marigayi Alhaji Ado Gwaram

Shi ma gogaggen ma'aikacin nan kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Malam Ado Gwaram ya rasu a ranar 24 ga watan Disamba

Gwaram ya rike mukamin sakataren gwamnatin mulkin soja a jihar Kano kuma bayan dawowar Najeriya tafarkin dimokuradiyya a tsakanin 1999 zuwa 2003 an sake nada shi a wannan matsayi.

Yana ɗaya daga cikin dattawan jihar Kano da ake jin maganarsu da shawarwarinsu a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Dakta Datti Ahmed

Dr Ibrahim Datti Ahmed

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Marigayi Dr Ibrahim Datti Ahmed

Kwatsam kuma a ranar 30 ga watan Disamba sai aka wayi gari da labarin rasuwar Dakta Datti Ahmed, tsohon shugaban majalisar ƙoli ta harkokin shari'ar musulunci ta Najeriya (SCSN).

Wasu bayanai sun ce ya shafe tsawon lokaci yana fama da wata rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

An sha gwagwarmaya da shi wajen yaɗa ilimin addinin musulunci da kuma bunƙasa harkokin addinin baki ɗaya a Najeriya.

Ya ɗan taɓa siyasa a lokacin da yake raye, don ya ma taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar SDP.

Bashir Othman Tofa

Bashir Othman Tofa

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Marigayi Bashir Othman Tofa

Ranar 3 ga watan Janairun 2022 ne jama'ar Kano suka tashi da mummunan labarin rasuwar tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya Alhaji Bashir Othman Tofa bayan shafe wasu ƴan kwanaki yana kwance a Asibitin Malam Aminu Kano da ke jihar ta Kano.

Wasu makusantansa sun tabbatar da cewa tsohon dan siyasar ya yi fama da jinya.

An haife shi a birnin Kano ranar 20 ga watan Yunin 1947 kuma ya yi karatunsa a Najeriya da Ingila.

Marigayin ya tsunduma harkokin siyasa a shekarar 1976 inda ya zama kansila a karamar hukumar Dawakin Tofa a 1977.

Tun daga lokacin ya rike mukamai da dama na siyasa ciki har da Sakataren jam'iyyar rusasshiyar jam'iyyar National Party of Nigeria, NPN reshen jihar Kano.

Bashir Othman Tofa ya tsaya takarar shugaban Najeriya a karkashin rusasshiyar jam'iyyar National Republican Convention, NRC, a zaben da aka gudanar ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 tsakaninsa da marigayi Chief Moshood Kashimawo Olawale Abiola ko MKO Abiola (a takaice) na rusasshiyar jam'iyyar Social Democratic Party, SDP.

Gwamnatin mulkin soji ta Ibrahim Badamasi Babangida ta rushe zaben wanda ya kasance da ce-ce-ku-ce da kuma wasu ke ganin marigayi Abiola ne ya yi nasara, wanda kuma a sanadiyyarsa aka samu ''June 12' wato 12 ga wata Yuni, ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da ita Ranar Dumokuradiyya a Najeriya.

Marigayin, wanda shi ne shugaban kungiyar dattawan jihar Kano, yana cikin dattijan arewacin Najeriya da suka dade suna kokawa kan matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin.

A wata hira da BBC Hausa, ya shaida mana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya daukar shawarar da suke ba shi domin shawo kan matsalar.

Sheikh Ahmad Bamba

Sheikh Ahmad Bamba

Asalin hoton, Sheikh Ahmad Bamba

Bayanan hoto, Sheikh Ahmad Bamba

Rasuwa ta baya bayan nan da ta girgiza jihar ta Kano ita ce rasuwar babban malamin addinin nan na jihar Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba, wanda aka fi sani da Ƙala Haddasana.

Wasu iyalansa ne suka tabbatar wa da BBC Hausa labarin rasuwar.

Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatun Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.

Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya inda ya kwana ɗaya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

Iyalan sun sanar da cewa za a yi jana'izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma'a.

Wani daga cikin ƴaƴansa Abdul ya shaida wa BBC cewa ya kusan shekara 82, don an haife shi ne a shekarar 1940.

Kala Haddasana kamar yadda aka fi saninsa da shi ɗan asalin ƙasar Ghana ne kuma a can aka haife shi.

"Ya dawo Najeriya ne bayan da ya yi karatun digirinsa a Saudiyya, sai ya koma Najeriya ya fara koyarwa a Jami'ar Bayero ta Kano har ya yi digirin-digirgir.

"Ya koyar a fannin Islamic Studies kuma ya jima yana koyarwar," a cewar ɗan na sa.

Malamin ya bar yara 28 zuwa 30 kamar yadda ɗan ya shaida mana.