Sani Dangote: Jana'izar kanen Aliko Dangote da aka yi a Kano

Birnin Kano na ci gaba da daukar jama'a daga ko'ina a sassan Najeriya, don jana'iza da ta'aziyyar ƙanin mutumin da ya fi arziki a nahiyar Afrika, Aliko Dangote.
An gudanar da jana'izar marigayi Sani Dangote ne a Fadar mai martaba Sarkin Kano wacce ta cika makil.
Shi ne mataimakin shugaban kamfanin Dangote.
Kuma a ranar Litinin ne kamfanin ya fitar da sanarwar cewa Sani Dangote Allah Ya yi masa rasuwa, bayan ya yi fama da kansar hanji.
Da safiyar Laraba aka iso da gawar mamacin daga Amurka tare da rakiyar iyalansa, kuma an binne shi ne a maƙabartar Alasawa da ke unguwar Koki da ke cikin Kano.
Ga hotunan yadda aka yi jana'izar Sani Dangote a Kano











Ana karɓar ta'aziyya ne a gidan mahaifiyar Aliko da Sani Dangote wato Hajiya Mariya a gidanta da ke Koki.
Wani daga cikin ƴan uwansa ya fada wa BBC cewa marigayin ya mutu yana da shekaru 61 a duniya, ya kuma bar mata daya da 'ya'ya takwas.
Gwamnoni da ministoci a Najeriya da ma hamshakan yan kasuwa duka sun halarci jana'izar da aka yi a birnin Kano.
Wanene Sani Dangote?

Asalin hoton, ERIC PIERMONT
Duk da sunansa bai karaɗe duniya ba kamar na yayansa Aliko, Sani Dangote hamshakin ɗan kasuwa ne.
Kafin mutuwarsa, Sani Dangote na da hannayen jari a manyan kamfanoni da ke harkoki a kere-kere da noma da kuma hada-hadar kudade.
Haka ma yana shugabantar kamfanoni kamar kamfanin masaka na Nigerian Textile Mills Plc, da Nutra Sweet Limited da Gum Arabic Limited da kuma Dangote Textile Mills Limited.
Yana kuma jagorantar kwamitin gudanarwa na Alsan Insurance Brokers, da Dan-Hydro Company Limited, da Dansa Food Processing Company Limited da kuma Dangote Farms Limited.
Marigayi Sani Dangote haka ma shi ne mataimakin shugaban kungiyar masu samar da ƙaro ta Afrika, wato Gum Arabic Producers Association, kuma sau biyu yana zama shugaban masu buga kwallon Polo ta Legas, wato Lagos Polo Club.
Dama marigayin kwararre ne a kwallon ta Polo.
Saboda irin kwarewar da yake da ita ta iya shugabanci aka nada shi wakilin Najeriya a ofishin jekadanci Romania.
Bugu da kari Sani Dangote na jagorantar kungiyoyin yan kasuwa daban daban da suka hada da shugaban kungiyar masu samar da taki.











