Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bulli Bai app: An kama mutumin da ya kirkiri manhajar yin gwanjon matan Musulmai a Indiya
Ƴan sanda a Indiya sun kama mutumin da ake zargin shi ya ƙirƙiri wata manhaja da ta yaɗa hotunan fiye da mata Musulmai 100 da sunan "gwanjonsu" ake yi.
Neeraj Bishnoi mai shekara 20, shi ne mutum na huɗu da aka kama kan wannan lamarin.
Manhajar mai suna "Bulli Bai" an ɗora ta ne a kan Github, wadda tuni kuma aka cire ta sakamakon fushi da tashin hankalin da hakan ya jawo.
Wannan ne karo na biyu da aka yi ƙoƙarin cin zarafin mata Musulamai cikin wata ɗaya, ta hanyar yaɗa hotunansu a gwanjon ƙarya.
A watan Yulin 2021, wata manhaja da wani shafin intanet "Sulli Deals" sun ƙirƙiri bayanai na fiye da mata Musulmai 80 - ta hanyar ɗora hotunansu a intanet - tare da bayyana su a matsayin "abin sayarwar ranar". Duk da cewa ƴan sanda sun fara bincike, har yanzu babu wanda aka gurfanar.
Ƴan sanda a aƙalla jihohi uku sun ƙaddamar da bincike a kan manhajar "Bulli Bai" kan ƙorafin da matan da ake yi wa wannan cin zarafi suka kai.
Wani sashen ƴan sanda na musamman a Delhi da ke kula da abubuwan da suka shafi laifukan intanet ya kama Mr Bishnoi a arewa maso gabashin jihar Assam a ranar Alhamis.
"Shi ne babban mai kitsa, kuma wanda ya ƙirƙiri manhajar," in ji KPS Malhotra, mataimakin kwamishinan ƴan sanda na tawagar laifukan intanet, kamar yadda ya shaida wa BBC.
Ƴan sanda sun kuma ce Mr Bishnoi ne ke kula da shafin Tuwitan da aka yaɗa hotunan matan daga manhajar.
A farkon wannan makon ne, ƴan sandan Mumbai suka kama wasu mutum ukun - Vishal Kumar mai shekara 21 ɗalibi mai karatun injiniya a birnin Bangalore da ke kudancin ƙasar, da kuma wasu ɗaliban biyu Shweta Singh mai shekara 18 da Mayank Rawat mai shekara 21 a jihar Uttarakhand da ke arewaci.
Wani mai magana da yawun kamfanin GitHub ya ce tuni kamfanin ya dakatar da shafin da ke amfani da manhajar "waɗanda dukka sun take dokokinmu."
"Bincikenmu yana kan matakin farko, don haka ba za mu iya cewa ko manhajar "Bulli Bai" da "Sulli Deals" suna da alaƙa ba," a cewar kwamishinan ƴan sandan Hemant Nagrale, a hirarsa da BBC Marathi.
A zahirin lamari, ba sayar da matan ake yi ba, kawai ana hakan ne saboda a muzanta da wulaƙanta mata Musulmai - waɗanda da yawansu suna nuna adawarsu kan yadda ake samun ƙaruwar irin wannan abu a ƙarƙashin mulkin Firaminista Narendra Modi.
"Sulli" kalma ce da masu tsaurin ra'ayi na addinin Hindu ke amfani da ita don cusgunawa mata Musulmai yayin da kalmar "bulli" ke nufin ɓata suna.
"An kuma kama wasu mutanen ma don amsa tambayoyi. Za mu binciki lamarin har zuwa ƙarshe, kamar yadda Satej Patel, ƙaramin ministan cikin gida na jihar Maharashtraya shaida wa BBC.
Jerin sunayen matan da ke kan manhajar sun haɗa da ƴan jarida da dama, da jarumin Bollywood da kuma wata mata mai shekera 65 mahaifiya wani ɗalibi da ya gudu.
Gwanjon matan ya kaɗa mutane tare da harzuƙa su bayan da hotunan mata da dama da aka sanya suka karaɗe shafukan sada zumunta.
Wani ɗan jarida ɗan yankin Kashmir Quratulain Rehbar, da ya kai koke kan shafin "Sulli Deals" a bara, ya ceabin takaici ne ka ga sunanka a kan manhajar.
Priyanka Chaturvedi, wata ƴar majalisa daga jam'iyyar Shiv Sena, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa an ƙirƙiri manhajarne saboda har yanzu ba a hukunta waɗanda suka fara ƙirƙirar shafin e "Sulli Deals"ba.
Sannan ta aika wasiƙun da ta rubuta zuwa ga Mr Vaishnav bayan da shafin intanet ɗin ya fara aiki a watan Yulin 2021.
A lokacin da labarin manhajar ya bayyana, wata mai waƙe Nabiya Khan wacce aka so kai wa hari a bara ta wallafa a tuwita cewa har a lokacin ƴan sandan Delhi ba su ɗauki mataki a kan ƙorafinta ba na 2021.
A 2018 ƙungiyar Amnesty International ta ruwaito cewa cin zarafi a intanet a Indiya ya nuna idan mace ta fiye magana kan ƴancinta to an fi kai mata hari.
Masu suka sun ce cin zarafin mata Musulmai ya yi muni a shekarun baya-bayan nan.