DCP Abba Kyari: Me rahoton binciken dan sandan na Najeriya ya ƙunsa?

Babban sufeton ƴan sandan Najeriya ya miƙa wa hukumar kula da harkokin ƴan sanda rahoto a kan binciken da wani kwamiti ya yi a kan jami'in rundunar da aka dakatar, Abba Kyari.

Kyari ya kasance shugaban wata runduna ta musamman da ke yaki da miyagun laifuka, amma daga baya aka dakatar da shi domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi cewa yana da hannu a cikin wata damfara ta sama da dala miliyan ɗaya.

Damfarar ta shafi jami'in ɗan sandan Abba Kyari da kuma shahararren dan damfarar nan na intanet Abbas Ramon da aka fi sani Hushpuppi wanda yanzu haka ke hannun jami'an tsaro na kasar Amurka.

Babban sufetan ƴan sandan Najeriya, Usman Alkali ya miƙa rahoton binciken da aka yi game da baɗakalar da ta shafi Abba Kyari ga hukumar da ke kula da harkokin `yan sanda don ɗaukar mataki na gaba.

Sufoton ƴan sandan ya miƙa rahoton ne bayan wata shida da karbar kwatankwacin wannan rahoton daga wani kwamiti da ya kafa, wanda ya gudanar da nasa binciken sannan ya miƙa nasa rahoton.

Wata majiya a hukumar da ke kula da `yan sandan Najeriya ta tabbatar wa manema labarai cewa an miƙa wa hukumar rahoton, kuma jami`anta na shirin nazarinsa.

Kazalika majiyar ta bayyana cewa rahoton ya ƙunshi bayanai daga bangarori daban-daban na waɗanda lamarin ya shafa, ciki har da bahasin da aka ji daga ɓangaren Abba Kyari.

Abba Kyari, shi ne shugaban wata rundunar ta musamman da ke yaƙi da miyagun laifuka, wanda aka dakatar a watan Yuli don gudanar da bincike a kan zargin da ake yi cewa yana da hannu a cikin wata damfara ta dala miliyon ɗaya da dubu ɗari da Abbas Ramon, wanda aka fi sani Hushpuppi da wasu suka yi, ama ya musanta.

Mahukunta a Najeriya sun dukufa wajen gudanar da wannan binciken ne bayan wani bincike da hukumar da ke binciken manyan laifuka ta Amurka ta yi, wadda ta ce ta same shi da laifi, kuma ta ba da shawarar a kai shi Amurka domin a yi masa shara`a.

Sanarwar da rundunar ƴan sanda ta fitar lokacin da ta dakatar da Abba Kyari ta ce matakin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kammala binciken zargin da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka [FBI] ke yi masa.

Zargin da ake yi wa Abba Kyari

Jami'in ɗan sanda Najeriya, Abba Kyari ya musanta karba rashawa a hannun Raymond 'Hushpuppi' Abbas.

Sashen shari'a na Amurka ya ce ya kama wasu ƴan Najeriya mazauna Amurka uku da suka taimaka wa Raymond 'Hushpuppi' Abbas ya yi damfarar dalar Amurka miliyan 1.1.

Cikin wata sanarwa wadda sashen ya fitar a ranar 28 ga watan Yuli, ta ce Hushpuppi ya amsa laifin halasta kudaden haram da wasu laifukan masu alaka da kasuwancin intanet.

Kuma sun yi zargin cewa Hushpuppi ya bai wa mataimakin kwamishinan ƴan sandan Najeriya Abba Kyari cin hanci domin kama takwaransa Kelly Vicente mai shekara 40 da haihuwa.

Bayanin sashen shari'ar ya bayyana hakan ne bayan da Vicent ya yi kokarin tona asiri da kuma ba da bayanai kan zargin abin da suka yi masa.

"A cewar sanarwar, Abba kyari wanda babban mataimakin shugaban 'yan sandan Najeriya ne, shi ake zargi da kitsa kama Vicent tare da aike wa da shi gidan yari, ya kuma dauki hotonsa ya aika wa Abbas.

"Abba Kyari kuma an yi zargin ya aika wa Abbas bayanin asusunsa na banki wanda nan ne Abbas ya aika masa kuɗaɗen ladan kama Vicent tare da tusa keyarsa gidan yari,"kamar yadda bayanin kotun ya bayyana.

Amma Abba Kyari ya musanta zargin yana cewa bai karbi ko sisi ba daga Hushpuppi.