Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shatu Garko: Hotunan Sarauniyar Kyau ta Najeriya
A ranar Juma'a ne aka zaɓi wata matashiya 'yar asalin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya a matsayin wadda ta zo ta ɗaya a Gasar Sarauniyar kyau ta kasar.
Ga wasu daga cikin ƙayatattun hotunan matashiyar mai suna Shatu Garko.
Shatu Garko, mai shekara 18, ta doke zaratan mata 18 a bikin da aka gudanar ranar Juma'a da dare a Landmark Centre da ke birnin Legas.
Shatu ce mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria a Turance.
Nicole Ikot ce ta zo ta biyu, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku.
Ta karɓe kambun ne daga hannun Etsanyi Tukura 'yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43 a 2019.
A cewar masu shirya gasar, wadda ta yi nasara za ta samu kyautar kuɗi naira miliyan 10, da zama a gidan alfarma na shekara ɗaya, da sabuwar mota, da kuma zama jakadiya ta musamman ga wasu kamfanoni.
A shafinta na Instagram, matashiyar ta yi godiya ga waɗanda suka shirya gasar da kuma waɗanda suka ɗauki nauyin wannan gasar.
Ta kuma gode wa jama'a bisa goyon baya da kuma soyayya da aka nuna mata