Kasashen Musulmi za su kafa asusun ceto Afghanistan

Kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta amince ta samar da wani asusu domin tallafa wa Afghanistan, inda miliyoyin mutane ke fuskantar hadarin yunwa.

Afghanistan ta fada mawuyacin hali ne tun bayan da 'yan Taliban suka karbe iko da kasar, sakamkon rike tallafin biliyoyin dala da aka yi.

Tun bayan da 'yan Taliban suka hambarar da gwamnatin Afganistan a watan Agusta kasashen duniya da ke ba wa kasar tallafi suka dakatar da dubban biliyoyin dala na wannan tallafi, abin da ya jefa jama'ar kasar cikin mawuyacin hali na rashi wanda ya sa suke fuskantar barazana ta yunwa, tare da gurgunta tattalin arzikin kasar.

Domin ceto al'ummar ne daga wannan hali na kaka-ni-ka-yi Kungiyar hadin kan kasashen Musulmin ta Duniya a taron na Islamabad, ta amince ta jagoranci samar da wannan asusu da zai taimaka wajen cetowa da kare al'ummar ta Afghanistan daga halin da suke fuskanta.

Haka kuma kungiyar ta OIC ta amince ta yi aiki tare da Amurka domin sakin kadarori na miliyoyin dala na Afghanistan din.

Kungiyar ta sanar da haka ne a wani taro na kasashen Musulmi 57 a babban birnin Pakistan Islamabad, inda Firaministan kasar Imran Khan ya bukaci Amurka da ta daina danganta gwamnatin Taliban da al'ummar Afghanistan.

Ya ce, '' dole ne in ce abu ne da ya wajaba mu yi, kuma na yi magana da Amurka musamman, dole ne su daina danganta gwamnatin Taliban da al'ummar Afghanistan miliyan 40.

" Ko da kuwa sun kasance suna rikici da Taliban tsawon shekara 40…. Shekara 20, saboda wannan Magana ce da ake yi da mutanen Afghanistan.

" Wannan ne ya sa yake da muhimmanci sosai a dauki mataki kai nan da nan. Tuni daman mun makara.'' In ji shi.

Baya ga wakilan kasashen Musulmin su kusan 60 da ke halartar taron, wakilai daga Amurka da Rasha da China da kuma Tarayyar Turai suma suna wurin taron.

Haka ita ma gwamnatin Taliban ta halarci taron, ko da yake ba za a barta ta shiga taron ba a hukumance.

Gwamnatin Pakistan ta ce an tashi tsaye ne wajen fadakarwa da nuna irin mawuycin halin da al'ummar Afghanistn ke fuskanta, wand dole a yi wani abu gagarumi a kai.

Ta ce ba wai ankararwar ba kadai, sai kuma an tashi tsaye cikin gaggawa idan ba haka ba to tattalin arzikin Afghanistan zai durkushe ba makawa.

Gwamnatin ta ce wadannan kudade da za a samar za su bayar da dama ga sauran kasashen duniya su bayar da taimakonsu ga kasar.

Ta kara da cewa akwai kasashe da yawa da suke son bayar da taimako amma ba sa son bayar wa kai tsaye ga gwamnatin Taliban.

Kasashen suna son ganin an samar da wata hanya da za su taimaka, wadda hankalinsu zai kasance kwance da ita.

Wannan ne ya sa aka samar da asusu ta Bankin Raya Kasashen Musulmi na Duniya, wanda ta nan ne yanzu kasashe za su rika tura timakonsu na Afganistan din.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa miliyoyin 'yan Afghanistan na fuskantar matsalar yunwa, muddin ba a dauki mataki ba lamarin zai kazanta.