Korona: WHO ta bayar da damar samar da riga-kafin korona na matalautan kasashe

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayar da dama ta gaggawa domin samar da wata karin allurar riga-kafin cutar korona, mai suna Covovox, domin amfanin musamman kasashe matalauta.

Cibiya mafi girma da ke samar da riga-kafi a duniya, Serum Institute da ke Indiya, ita ce za ta samar da maganin karkashin ikon kamfanin Amurka Novavax.

Yanayin da duniya ta tsinci kanta a ciki a wannan lokacin inda ake ta samun karuwar masu kamuwa da cutar korona a kasashen duniya masu arziki da yawa, a sanadiyyar sabon nau'in cutar, wato Omicron, shi ne ya sa duniya ta shiga taitayinta da cewa ba wanda zai tsira idan ba kowa da kowa ya tsira ba.

Daman tun kafin a zo wannan gaba, da jimawa Hukumar lafiya ta Duniya take ta jaddada bukatar ganin an samar da isasshen riga-kafin da za a yi wa mutane a kasashe matalauta domin a gudu tare a tsira tare,

To amma WHO ta damu da yadda kasashe masu arziki maimakon su tabbatar da samar da wadatacciyar allurar a kasashe matalautan, sai suka rika tarawa fiye da bukatarsu wai domin gaba.

A sanadiyyar halin da aka shiga yanzu ne za a samar da wannan sabon nau'in riga-kafin na Covovax, wanda za a raba a karkashin shirin samar da allurar a kasashen duniya Covax domin amfanin wadannan kasashe masu karamin karfi kawai.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce 41 daga cikin irin wadannan kasashe ba su yi wa ko da kashi 10 cikin 100 bisa dari na yawan al'ummarsu rika-kafin ba.

Wannan sabuwar allurar riga-kafin ta Covavax, wadda zagaye biyu ce ita ce allurar riga-kafin mai sinadarin furotin (protein) ta farko wadda hukumar ta lafiya ta duniya ta bayar da damar amfani da ita.

Har yanzu Hukumar kula da Magunguna ta Tarayyar Turai tana tantance ainahin samfurin allurar kafin kuma daga baya Hukumar Lafita ta Duniya ta yi nata nazarin a kanta, daga nan kuma sai a fara maganar ba da damar amfani da ita.