Yakin basasar Habasha: Yadda Fira Minista Abiy ya jagoranci yaki da 'yan tawaye

Abiy Ahmed

Asalin hoton, Ofishin Fira Ministan Habasha

Bayanan hoto, An dauki hoton Fira Ministan ya na bai wa kwamandoji umarni a fagen daga
    • Marubuci, Daga Farouk Chothia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Fira Minista Abiy ya shiga jerin shugabannin da suka gabata a Habasha da suka kafa tarihi wajen dannawa sahun gaba a yakin da kasar ke yi na karya laggon mayakan 'yan tawayen 'yankin Tigray, wadanda sukai barazanar hambarar da mulkinsa.

Mutumin da ya karbi kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekarar 2019, ya shayar da mutane mamaki bayan bullar bidiyo da hotunansa sanya da kakin soji da sauran dakaru, su na dannawa cikin surkukin daji da tsaunuka, da amfani da abin hangen nesa, tare da yi wa sojojin da suka kafa sansani cikin dazuka jawabi.

"Ina kira ga wadanda suke son zama 'ya'yan kasar Habasha, wadanda za a jin jinawa tarihgi kuma ba zai man ta da su ba, ku mike domin kasarku. Mu hadu a fagen daga" in ji Abiy.

Farfesa Kjetil Tronvoll, a sashen nazarin tashe-tashe hankula a kwalejin Oslow da ke Norway, ya ce babu tantama matakin da Mista Abiya ya dauka ya taimaka matuka wajen juyewar reshe kan mayakan TPLF.

"Duk da hotunan sun nuna ya na gab da isa sahun gaba a fagen daga, ba wai ainahin fagen yakin yakin ba, amma matakin ya yi, kwalliya ta biya kudin sabulu, " in ji shi.

"Hakan ya karawa sojoji karsashi, inda hakan ya sanya 'yan kasa suka yunkuro ciki har da fitattun mutane irinsu Haile Gebrselassie da ya fito ya nuna goyon baya ga yakin, kuma dubban mutane sukai layi domin shiga aikin da sojojin ke yi, hatta mayaka masu dauke da makamai na yankin Amhara sun shiga."

Hare da jirage marasa matuka

Koma bayan da mayakan TPLF suka fuskanta na da yawan gaske. A lokacin da mayakansu ke kusa da garin Debre Birhan town, kusan kilomita 130daga babban birnin Habasha, Addis Ababa, an tilasta musu komawa baya zuwa garin Weldiya mai nisan kilomita 400 daga Addis Ababa. Wannan na nufin 'yan tawayen sun rasa iko da manyan garuruwa masu muhimmanci a babbar hanyar da za ta sada ka da yankin Tigray zuwa fadar gwamnati.

Wurin da hari ta sama ya fada a Mekelle, yankin Tigray a Habasha - Nuwamba 2021

Asalin hoton, AC

Bayanan hoto, an kai hari da jirage marasa matuka a Mekelle, babban birnin yankin Tigray

Farfesa Tronvoll ya kara da cewa ya yin da Mista Abiy ya dogara da dakarun da ke kasa, jirage marassa matukan da aka samo daga kasashen Turkiyya da Iran da China sun taka rawar fatattakar 'yan tawayen TPLF: "An zargi jirgi maras matukin China samfurin Wing Loong II, shi ne mai karfi da ke iya dauke tankar yaki, da zubo makaman atilari, da jefa bama-bamai kan sojoji."

A bangare guda kuma, gwamnati ta yi kunnen shegu da kiraye-kirayen Amirka da tarayyar Turai da suka matsa lambar zama teburin sulhu ga bangarorin biyu da dakatar da bude wuta, da wani abu mai kama da goyon bayan kasashen yamma ga TPLF, wani mataki da Mista Gebrselassie, ke ganin bai dace ba.

"Mun ga yadda yaki ya karkare a kasashen Iraqi, da Syria, da Yemen da kuma Libya, yadda suka taru suka daidaita kasar. Amma Habasha kasa ce mai al'umma sama da miliyan 120. Dan haka yunkurin dagula lamura a kasar ka iya zama kaikayi koma kan mashekiya," ya shaidawa kafar yada labaran kasar.

"Na san 'yan uwana maza da mata na Afirka, su na mara mana baya, kuma mun dade karni da yawa mu na yaki da mulkin wariyar launin fata tare."

Tronvoll ya ce Abiy, ya bude hanya nunawa gwamnatocin kasashen Afirka goyon baya, da sauran kasashen da su ke kishi da kasashen yammacin duniya: "Da farkon fara yakin, Mista Abiy ya kira kungiyar TPLF da kungiyar da bata bin doka da oda.

"Daga baya sai ya rungumi tsarin nan na Afirka tare da kiran TPLF da mai neman durkusar wa da kokarin yaki da ci gaban Habasha, kamar dai yadda shugabannin da suka gaba ce suka yi."

Sunansa ya kara fice

A watan Nuwamba Mista Abiy ya ja layi tsakanin kokarin TPLF na kokarin hambarar da gwamnatinsa, kwatankwacin yadda sarki Menelik II, ya fatattaki wadanda suka mamayer Italiya a lokacin yakin Adwa a shekarar 1896, wanda shi ne sarkin da ya zo Habasha ya kafa kasar ta yanzu a yankin Amhara.

A 6 ga watan Satumba 2021, a lokacin da aka gudanar da wani biki na nuna goyon baya ga sojojin Habasha da ke yaki da 'yan tawayen Tigray a yankin Amhara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban 'yan Habasha sun cika titunan Addis Ababa don nuna goyon baya ga dakarun kasar

"'Yan uwana 'yan Habahsa a ciki da wajen kasarmu, mu na bukatar ku dinga bayyanawa duniya gaskiyar abin da ke faruwa. Kawunan mu a hade suke, za mu shawo kan matsalar nan idan muka hada karfi da karfe, mu magance masu yi wa kasarmu barazana. A matsayinmu na 'ya'yan #Adwa, za mu daukaka #Habasha #Lamarinmu babu karaya," wannan shi ne sakon da Abiya ya wallafa a shafin sa na tiwita.

Asalin kungiyar TPLF dai ta 'yan sari ka noke ce, wadda ta yi mulki a shekarar 1991. Ta mamaye gwamnatin Habasha har zuwa shekarar 2018, lokacin da Fira Minista Abiya ya kama aiki, bayan wata zanga-zangar yadda suke mulki. Daga nan sai ta koma yankin Tigray ta yi bakam, wanda daga nan ne ta fara kaddamar da hare-haren kan sauye-sauyen da Abiya ya bullo da su a shekarar da ta gabata.

Wani mai sharhi kan lamuran da suka shafi kusurwar Africa, mazaunin Birtaniya Abdurahman Sayed, ya ce Abiy ya siyawa kan shi mutunci da kima a idanun 'yan kasar Habasha kan daukar matakin shiga sahun gaba a fagen daga, domin nunawa duniya aniyarsa ta magance tsagerancin 'yan tawayen.

"Matakin barin gidan shi, da hada kai cikin dakaru, Mista Abiy ya aike sakon cewa a shirye ya ke ya sadaukar da ran shi domin Habasha," in ji farfesan.

Zanen sarkin Habasha Menelik II GCB, da ya rayu daga 1844 - 1913, dan kabilar Negus Shewa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarki Menelik II ya yi nasara a yakin Adwa a shekarar 1896, ana kuma bikin tunawa da hakan a kowacce shekara

"Ya damu matuka da tarihin sarakunan Habasha, ya kuma taba fadawa dandazon masu saurarensa cewa mahaifiyarsa ta taba yin hasashen zai zama sarki na 7 a kasar. Sarakuna na jagorantar dakarunsu a fagen daga , ya kuma yi makamancin hakan."

Farfesa Tronvoll ya kara da cewa matakin da Mista Abiy ya dauka sun zo da mamaki ga wanda ya samu kyautar Nobel ta zaman lafiya, wadda aka karramashi da ita a shekarar 2019, bayan kawo karshen zaman tankiyar gwamman shekaru tsakanin kasar da makofciyarta Eritrea.

"Barack Obama ya lshe kyautar bayan zama shugaban Amirka, tare da kaddamar da yaki a Afghanistan, amma a dakin yaki na fadar White House ya zauna. Mista Abiy ne na farko da ya taba zuwa gab da fagen daga," in ji Farfesa Tronvoll.

Yaki a fitacciyar hanya

Mista Abiy ya tafi faggen daga da ke gabashin kasar a watan Nuwamba, inda dakarun Habasha na musamman da mayaka ma su dauke da makamai na yankin Afar suke wanda sukai nasarar janyowa mayakan TPLF.

Map
1px transparent line

"Kabilar Afar, makofciyar Tigray ce. Bisa al'ada, ana musu kallon mayaka. Kusan kowanne namijin Afar daga shekara 15 ya mallaki bindiga. Sun dade su na bai wa mayakan Tigray kashi , kuma a karon farko matan yankin Afar sun shiga yakin," in ji Mista Abdurahman.

"Ya nuna yadda suka fusata da 'yan TPLF, saboda irin muggan alkaba'in da mayakan Tigray suka yi wa al'ummar yankinsu a lokacin da sukai ballaewa daga yankin watanni 6 da suka gabata."

Mista Abdurahman na kallon hakan a matsayin wani abu da ya sanya dan ba a yakin, sakamakon yadda suka karya laggon TPLF na kokarin dannawa iyakar kasar da Djibouti: "Habasga kasa ce mai sa'a, ya yin da tashar ruwan Djibouti ita kasance ruhin tattalin arzikinta.

"Idan TPLF ta karbe iko da hanyar da za ta sada ka da iyakar, to kuwa tattalin arzikin Habasha zai durkushe ba ki daya, babu wasu kaya da za a iya shiga da su Addis Ababa, sannann mayakan Tigray za su kara samun damar dannawa da zarar sun karbe Addis shi kenan sun yi nasara a yakin."

Makwanni biyu da suka gabata, Mista Abiy, ya dawo daga fagen daga, mako guda bayan nan ofishin sa ya sanar da cewa ya sake komawa domin jagorantar sojoji domin kwace iko da yankin Amhara daya 'yan tawaye. A na su bangaren 'yan tawayen TPLF sun ce sun sake karbe iko da wata Majami'a mai da dadden tarihi da ke garin Lalibela.

Bayanan bidiyo, Exploring the churches carved from rock

Ga mutane irin farfesa Tronvoll, shugaban Habashar ka iya ci gaba da rike madafun iko, amma kash ya bata sunan shi a idanun duniya: "Muhimmin abin da ake dubawa wajen bada kyautar Nobel ta zaman lafiya shi ne wanzar da zaman lafiya, wanda shi ne abin da ya sanya aka bai wa Mista Abiy, amma a yanzu ya yi watsi da batun dakatar da bude wuta, ya yin da ake zargin dakarunsa da laifukan cin zarafin dan adam."

Amma Mista Abdurrahman ya kara da cewa Abiy, ba shi da wani zabi baya ga yaki da TPLF matukar ya na son ci gaba da rike madafun iko.

"Ba mu san tsahon lokacin da za a dauka ana wannan yaki ko ranar da zai zo karshe ba, sai dai Mista Abiy ya nuna shi ba kanwar lasa ba ne."

More on the Tigray crisis: