ECOWAS za ta kara matsa takunkumi a Mali da Guinea

Asalin hoton, BUHARI SALLAU
Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta bayyana matukar damuwarta a kan jinkirin da aka samu wajen mayar da kasashen Mali da Guinea kan mulkin dimukuradiya.
Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta ce zuwa yanzu babu wata alama da ta gani wadda ke nuna alamun mayar da kasashen kan turbar dimukuradiyya, bayan juyin mulkin da soji suka yi a kasashen biyu a farkon shekaran nan.
Saboda haka ta yi barazanar ci gaba da aiwatar da matakan ladabtarwa kan masu rike da iko a kasahen biyu ta hanyar takunkumi.
Kungiyar ta raya kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ko CEDEAO ta cimma wannan matsaya ne ta neman ci gaba da aiwatar da aniyarta ta ladabtar da masu rike da iko a wadannan kasashe biyu na Mali da Guinea, kamar yadda ta bayyana a takardar bayan taron kolin da ta gintse a Abuja, babban birnin Najeriya a jiya Lahadi.
Taron ya cimma wannan matsaya ne dalilin rashin ganin wata alama ta mayar da kasashen biyu kan mulkin dimukuradiyya kamar yadda sojojin kasashen suka yi alkawari, wanda a don haka ne kungiyar ta ce ba ta da wani zabi illa ta aiwatar da matakan da ta dauka tun farko a kan kasashen biyu, wanda ya hada da dakatar da kadarori da hana tafiye-tafiye a kan masu hannu a juyin mulkin da kuma iyalansu.
Tare kuma da neman kasashe da sauran hukumomin duniya kan su mara musu baya wajen aiwatar da wadannan matakai na takunkumi.

Asalin hoton, BUHARI SALLAU
A kan batun Guinea kungiyar ta kasashen Yammacin Afirka ta ce damuwarta ita ce, wata uku bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde, har yanzu babu wani jadawali da aka fitar na tsarin mayar da kasar kan mulkin dumukuradiyya, duk da alkawarin da sojoji suka yi na aiwatar da zabe cikin wata shida, bayan sun dare mulki.
Sai dai shugabannin na ECOWAS sun ce jagororin kasar sun ba su tabbacin cewa zuwa karshen watan nan na Disamba za su kafa majalisar kasa ta shirya mayar da kasar kan mulkin dimukuradiyya, wadda ita za ta fitar da jadawalin zaben.

Asalin hoton, AFP
Haka kuma kungiyar ta CEDEAO ta ce bisa ga dukkan alamu abu ne mai wuya a cimma wa 'adin da aka sa a Mali na aiwatar da zabe a kasar ranar 27 ga watan Fabrairu na sabuwar shekara 2022.
A don haka ta yi gargadin cewa dole ne a tabbatar da wannan alkawari, kuma idan ta ga babu wani muhimmin ci gaba da aka samu dangane da hakan nan da karshen watan nan na Disamba, to ba makawa za ta sanya wa masu rike da ikon Karin takunkumi na tattalin arziki da kudade daga ranar 1 ga wtan Janairun sabuwar shekara
Sojoji sun yi juyin Mulki biyu ne a Mali a cikin shekara daya kacal, inda na baya-bayan nan ya kasance a watan Mayu lokacin da suka hambarar da Shugaba Bah Ndaw da Firaminista Moctar.
Bayan batun dumukuradiyya a yankin na Yammacin Afirka, taron shugabannin kasashen, wanda Muhammadu Buhari na Najeriya ya karbi bakunci, ya kuma tattauna a kan yanayin tsaro da kusan a kullum yake kara tabarbarewa a yankin, inda kungiyoyi da ke dauke da makamai suke kara tayr da hankali da rikici a kasashe da dama da suka hada da Najeriya da Nijar da Mali da Burkina Faso.
Shugabannin sun ce wannan lamari na tabarbarewar tsaron ya dame su, inda suka yi alkawarin aiki tare domin fuskantar kalubalen.
Amma kuma sun nuna damuwarsu kan yadda aka shigo da wani kamfanin sojojin haya na kasar waje Mali domin yakar matalar.
Wanda wannan suna nufin kamfanin sojin haya Rasha ne wato Wagner Group, wanda rahotanni suka ce gwamnatin Mali ta dauko shi ne domin maye gurbin sojojin Faransa a yaki da 'yan bindiga da suka addabi kasar.
Shugabannin na kasashen Yammacin Afirka sun nana cewa matkin hadari ne ga tsaron yankin.
Harwayau wani batu da shugabannin na ECOWAS suka tattauna kuma shi ne na tasirin annobar korona a kan tattalin arzikinsu da kuma harkar kula da lafiya.
Ta wannan fanni shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya nuna damuwar da shugabannin kasashen Afirka da dama ke bayyanawa, inda suke suka kan matakin hana tafiye-tafiye a kan kasashen nahiyar da yawa da wasu kasashe ke yi saboda bullar sabon nau'in cutar korona na Omicron.
Shugaban na Ghana ya bayyana matakin da cewa abu ne da bai dace ba sam-sam wanda ba za su lamunta da shi ba, kuma abin takaici ne.











