'Yan Kannywood na caccakar Buhari kan matsalar tsaro a Arewa

Lokacin karatu: Minti 3

Taurarin fina-finan Kannywood sun bi sahun sauran mutane wajen caccakar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari saboda zargin gazawarta wajen tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari kan fasinjojin da suka fito daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta'azzarar hare-haren 'yan bindiga a inda suke.

Bayanai sun nuna cewa 'yan bindigar sun banka wuta kan motar da mutanen akalla 40 suke ciki inda suka kone kurmus.

Wani ganau ya gaya wa BBC cewa: "Lokacin da abin ya faru ina Sabon Birni aka kira ni aka shaida min. Daga cikin matafiyan ma har da wani ƙanin mahaifiyata da matarsa da ƴaƴansu huɗu.

"Cikin ƴaƴan Allah Ya yi wa biyu rasuwa. Lokacin da muka isa wajen da ya faru mun je mun iske mutane sun mutu, kuma a ƙalla mun ƙirga gawarwaki sun kai 25".

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta ce mutum 21 ne suka kone a motar fasinjan lokacin da 'yan bindiga suka yi musu kwanton-bauna.

Lamarin ya yi matukar tayar da hankalin 'yan kasar musamman 'yan arewacin Najeriya.

Wani abu da ya kara jan hankalin 'yan arewacin kasar shi ne alwashin da Shugaba Buhari ya sha na gudanar da bincike kan kisan da wasu dalibai suka yi wa wani dalibi a makarantarsu da ke Lagos, amma kawo yanzu bai ambata daukar irin wannan mataki ba kan kisan mutanen na Sokoto, idan ban da jaje da ya yi.

'Bincike kan kisan ba gaira ba dalili'

Da yake tsokaci kan labarin da muka wallafa game da alkawarin da Shugaba Buhari ya yi na yin bincike kan mutuwar dalibin na Lagos, tauraron fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, ya ce ya dace gwamnati ta dauki irin wannan mataki kan mutanen da aka kashe a Sokoto.

"Ya kamata wadanda suka mutu a motar da aka kona a Sokoto su ma a yi wannan binciken a dauki mataki a kan daukar ransu da aka yi ba gaira ba dalili," in ji tauraron.

A nata bangaren, Hadiza Gabon, ta nuna takaicinta yadda 'yan Arewa suka kasa nemar wa 'yan uwansu hakki yayin da takwarorinsu na Kudu suke ta fafitikar nemar wa mutum daya 'yanci.

Shi kuwa Falalu Dorayi ya rubuta wani jawabi ne a shafinsa na Instagram wadda ya yi wa lakabi da "Gazawar Shugabanni" inda ya yi tir da irin rashin mayar da hankalin shugabanni kan ayukan da suka yi alkawuran aiwatarwa.

"Kuna zaune a gida a shigo a kashe ku, a far ma iyalanku mata. Kuna kan hanya a tare a debe ku a kashe na kashewa. Ku bar gari domin gudun tsira a tare ku a kone ku. Ku yi noma domin samun abinci, a kone gonar da amfanin cikinta... Idan kana so ka ga karfin ikonsu [shugabanni] to ka taba kujerarsu ko ku kuma jam'iyyarsu," in ji shi.