Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama mutum 32 da hannu kan satar mutane a hanyar Kaduna-Abuja da harin masallacin Neja
Rundunar sashen 'yan sanda na musamman a Najeriya, ta ce sun kama wasu da ke zargin masu satar mutane don neman kudin fansa, da 'yan fashi, da masu safarar muggan makamai, da muggan ƙwayoyi, da satar motoci a iyakokin kasar, da fyaɗe da suransu.
Har wa yau, 'yan sandan su yi nasarar ƙwace bindiga samfurin AK47 guda 18, samfurin GPMG uku, da Ribalba biyu, da karamar bindiga guda, da alburusai 453 da kuma motoci 17 da suka yi fashinsu.
Hakan na ƙunshe ne a acikin wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ƙasar ta fitar a ranar Laraba da yamma.
Cikin wadanda aka kama akwai shahararrun 'yan fashin da ke satar motoci a jihohin Nasarawa da Abuja da Kebbi da Zamfara da Fatakwal.
Motocin da suka sata suna tsallakawa da su iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar domin sayar da su ga wani mutum Alhaji Garba da har yanzu ake nema.
Tuni 'yan sandan kasa da kasa ke aiki da takwarorinsu na Jamhuriyar Nijar domin gano mutumin da masu taimaka masa don gurfanar da su gaban shari'a.
Rundunar ta ce akwai wani matashi Dayyabu Muhammad mai shekara 27 dan karamar hukumar Soba da ke jihar Kaduna, da aka samu bindiga AK47 biyar da alburusai 250 a hannunsa.
An kama shi ne a samamen da suka kai wa ɓarayin daji a Saminaka da ke jihar Kaduna, kuma bincike ya nuna Dayyabu ne yake kai wa ɓarayin muggan makamai.
'Ɓarayin da suka daɗe suna addabar hanyar Abuja-Kaduna'
Sanarwar rundunar ƴan sanda ta kuma ce an kama masu satar mutanen da suka daɗe suna addabar hanyar Kaduna zuwa Abuja wato Yellow da Budderi.
Sannan an kama wadanda suka kai mummunan harin da ya rutsa da mutane da dama a Tafa da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna, inda suka yi awon gaba da wani mutum da matansa biyu, amma 'yan sandan sun yi nasarar kuɓutar da su tare da gano maɓoyar ɓata garin.
Rundunar ta kuma cafke mutum shida, Mohammed lawali da Suleiman Ibrahim da Mohammed Rebo da Bashir Audu da Monsoru Abubakar da Abubakar Hamidu, da alaƙa da harin da aka kai Masallacin Mazakuka da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja, inda mutum 18 suka mutu aka kuma yi awon gaba da mutum 30.
Binciken 'yan sanda ya gano Muhammad Lawali da wasu daga cikin ɓata garin sun tsere ne daga gidan kaso na birnin Lakwaja.
A karshe sanarwar ta ce, babban sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargi gaban shari'a domin fuskantar hukuncin da ya dace da su.