Fargabar korona ta hana taron kungiyar kasuwanci ta duniya

Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, WTO ta ɗage taron ministocin kasuwanci daga kasashe sama da 160 da ta shirya yi a birnin Geneva a mako mai zuwa, saboda matakan da ake ta dauka na dakile bazuwar sabon nau'in kwayar cutar korona.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne a wani taron jakadun kasashe a Geneva, bayan da ta tabbata cewa da dama daga cikin ministoci da jami'an cinikayya na kasashe ba za su halarci taron ba.

A shekarar da ta wuce ma an dage wannan taro saboda annobar ta korona.

Amurka da Australia sun bi sahun Karin kasashen da ke ta daukar mataki a kan matafiya daga kasashe tara a yankin kudancin Afirka, inda sabon nau'in cutar na yanzu ya fara bayyana.

In banda wannan sabon nau'in kwayar cutar ta korona, wanda aka yi lakabi da Omnicron, wanda ake gani mafi hadari da ya katse wa kungiyar kasuwancin ta duniya hanzari, ta dauki wannan mataki da taron zai kasance na farko cikin shekara hudu na ministoicin kasuwanci na duniya.

Kungiyar ta sake dage taron ne saboda Switzerland, kasar da ke zaman mazaunin kungiyar ta WTO ta haramta wa jiragen sama daga yankin kudancin Afirka zuwa can.

Sannan kuma ta sanya tsauraran matakan killacewa ga mutanen da suka fito daga kasashen da aka samu bayyanar sabon nau'in kwayar cutar.

Daya daga cikin muhimman batutuwa da ministocin suka shirya tattaunawa shi ne na kira ga galibin kasashe masu hali da su dage hakkin mallaka, su bayar da dama a rika yin magunguna da alluran rigakafin korona a sauran kasashe domin a raba su da sauri a fadin duniya.

Shugaba Biden na Amurka ya goyi bayan yin hakan yana mai cewa bullar wannan sabon nau'in kwayar cutar ya ma kara nuna muhimmancin bayar da wannan dama.

Abin da su kuma wasu kasashe wadanda suka hada da Birtaniya da kungiyar kasashen Turai suka ki yarda da shi.

Haka kuma a ci gaba da matakan da kasashe ke dauka domin dakile bazuwar sabon nau'in cutar kada ya kai gare su, Amurka ta bi sahun sauran kasashe wajen sanya matakai a kan matafiya daga da yawa daga cikin kasashen Kudancin Afirka.

Ita ma Australia ta sauya dokokinta na killacewa a kan matafiya daga sassan Kudancin Afirka, inda wadanda ba 'yan kasarta ba da suka je Afirka ta Kudu da Namibia da Zimbabwe da Botswana da Lesoto da Eswatini da Seychelles da Malawi da kuma Mozambique a cikin kwana 14 da suka gabata ta haramta musu shiga kasar.

Su kuwa 'yan kasarta da suka kasance a daya daga cikin wadannan kasashe tara za a kyale su su koma, amma kuma sai sun killace kansu, walau a otal ko a gida, ya danganta ga hukumomin jihar da suke.

Bayan zaman killacen na kwana 14 sannan za a yi wa mutum gwaji.