Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta sauya manufa kan Mexico
Amurka ta ce ta daina daukar Mexico a matsayin wani yanki nata na bayan gida, wanda hakan ya sa shugaban Mexico sassauta wa a kan alaƙar ƙasashen biyu.
Shugaban Amurka Joe Biden ne ya jaddada wannan matsayi a ganawa da takwarorinsa na Mexico da Canada a taron ƙoli na farko na shugabannin kasashen nahiyar Amurka ta Arewa cikin shekara biyar.
Taron da batun shige da fice musamman na kwararar 'yan ci-rani da na tattalin arziki za su mamaye.
Ana sa ran Mista Biden zai tattauna da Shugaba Andres Manuel Lopez Obrador na Mexico kan yadda za a rage yawan 'yan ci-ranin yankin Amurka ta Tsakiya da ba a taba gani ba da ke ta tururuwa zuwa iyakar Amurka da Mexico.
Yayin da wannan taro na koli na shugabannin kasashen uku ke wakana a Washington, matsalar tuɗaɗar 'yan ci-ranin na kara haɓɓaka, inda dandazon wasu yan ci-ranin har dubu uku ya bar kudancin Mexico a jerin gwano, ya tasamma hanya da zummar kaiwa iyakar Amurka kafin ƙarshen wata mai zuwa.
Yawancin 'yan ci-ranin na kokarin tsira ne daga fatara da talauci da tashin hankali a Haiti da ƙasashen Amurka ta Tsakiya, wadanda suka kunshi Panama da Costa Rica da Nicaragua da Honduras da El Salvador da Guatemala da kuma Belize.
Shugaba Lopez Obrador na Mexico da sauran takwarorinsa sun amince bisa matsin lambar Amurka su tura jami'an tsaro domin hana gungungun 'yan ci-ranin da a ko da yaushe suke ratsawa ta yankunan kasar Mexico, wucewa.
Sai dai shugabannin sun bukaci gwamnatin Biden da ta yi kokarin magance ainihin matsalolin da ke janyo kaurar, ta zuba jari a yankin tare da kirkiro ayyuka a kasashen ta magance aikata miyagun laifuka da cin hanci da rashawa da kuma talauci.
A jawabinsa na bude taron shugaban Mexico ya ce yana godiya cewa Amurka ta daina daukar kasarsa a matsayin tamkar wani ɓangare nata, wato yankin bayan gidanta.
Ya ce, ''Kamar yadda Shugaba Biden ya ce, yana son dangantaka tsakanin kasashen biyu ta zama ta mutunta juna da kuma daukar juna a matsayin tsara.''
Ya kara da cewa, ''Ya gaya min wannan tun lokacin da muka fara magana ta waya, a matsayinsa na shugaban Amurka.''
''Ya gaya min cewa Amurka ba za ta rika kallonmu a matsayin bayan gidanta ba, wanda muna godiya a kai, domin ta wannan hanya ba ma bukatar mu jaddada manufofinmu na 'yancin kai da mulkin kanmu.''In ji shugaban na Mexico.
A yayin taron nasu ana sa ran Mista Biden zai kara matsa wa shugaban na Mexico a kan rage tuɗaɗar 'yan ci-ranin na yankin kasashen Tsakiyar Amurkawa da ke nufar iyakar Amurka
A fannin kasuwanci kuwa, Mexicon da Canada sun damu ne da manufar Mista Biden ta lalle sai a sayi hajojin Amurka, da kuma shirinsa na sanya haraji a motoci masu amfani da lantarki, wanda kamfanonin da ke Amurka ne za su fi cin gajiya.