Abu 10 da muka sani bayan rushewar gini mai hawa 21 a Legas

Adadin mutanen da suka mutu a rushewar ginin Ikoyi da ke Legas ya karu.

Gwamnatin Legas ta sanar da cewa ta gano gawa 14 kawo yanzu, kuma akwai fargabar a sake zakulo wasu gawarwakin.

Haka ma hukumomin sun yi nasarar ciro mutum tara daga baraguzan ginin a raye.

Dogon ginin da ke kan hanyar titin Gerrard a Ikoyi ya ruguzo ne ranar Litinin.

Kuma tun a ranar yan uwa da abokan arzikin wadanda ake sa ran ginin ya rufta da su suka yi cirko-cirko a inda lamarin ya faru, suna fatan a ceto 'yan uwan nasu da ginin ya danne.

Kazalika, tun ranar da bala'in ya faru ake samun sakonnin jaje har daga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Ganau sun ce da misalin karfe 2:25 na ranar Litinin ne suka fahimci cewa ginin yana rawa, kafin daga baya ya ruguje.

Ga abubuwa 10 da suka faru tun bayan rushewar dogon ginin na Ikoyi.

Masu aikin ceto na jin alamun masu rai da baraguzai suka danne.

Duk da cewa an samu karuwar yawan wadanda suka mutu tun bayan rushewar ginin, a ranar Talata masu aikin ceto sun ce suna jin motsin wasu a raye a karkashin ginin.

Wani ganau ma ya fada wa BBC cewa ya jiyo muryar wata mata a karkashin ginin ta neman ceto kuma suna ta kokarin ceto ta.

An rufe hanyar da ke zuwa inda ginin yake

Gwamnatin jihar Legas ta rufe hanyar da ke isa titin Gerard inda ginin yake.

Hukumomin sun yi haka ne da nufin bai wa masu aikin ceto damar isa wurin cikin sauki.

Ginin mai hawa 21 ya rushe ne kan babbar hanya

Sai dai manufar hukumomin ta bai wa masu aikin ceton damar isa wurin da bala'in ya faru ta hadu da cikas.

Dalili kuwa shine titin da ginin ya rushe wani bangare ne na babbar anguwar Ikoyi da ke da yawan ababen hawa.

Injiniyoyi sun ce aikin ceton gagarumi ne, da ke bukatar manyan kayan aiki da za su tono ginin tun daga tushe.

Shugaba Buhari ya umurci a agaza wa wadanda aka ciro daga ginin a raye

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci hukumomi da su kara kaimi wurin aikin ceto wadanda ake kan nema a baraguzan ginin.

Shugaban ya kuma yi kira ga hukumomin da ke bada agajin gaggawa da suka hada da asibitoci su bada taimakon duk da ya dace ga wadanda aka ceto.

Bayan haka kuma Shugaba Buhari ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu da ma wadanda yanzu haka ake kokarin ceto su.

Adadin wadanda suka mutu ya karu

A sanarwar da ta fitar tun da farko, gwamnatin Legas ta ce an gano gawa 10.

Amma kuma a ranar Talata wata sanarwar ta ce adadin ya kai mutum 14.

An sallami mutum uku daga asibiti

Mataimakin gwamnan jihar Legas Kadri Hamzat ya ce kawo yanzu an sallami mutum uku da lamarin ya rutsa dasu daga asibiti.

Kuma sauran shida da yanzu haka ke ci gaba da jinya na samun sauki.

Gwamnatin Legas ta dauki nauyin masu jinya a asibiti

Har wa yau, Mataimakin Gwamnan Legas Kadri Hamzat ya ce gwamnatin jihar ce za ta biya kudin jinyar wadanda aka ceto.

Ya fadi hakanne a lokacin da ya ziyarci inda ginin ya rushe yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Ba a san inda injiniyan da ke kula da ginin yake ba

Kamfanin Fourscore Homes Limited ya tabka babbar asara a dalilin rugujewar ginin nasa a ranar Litinin.

Olufemi Adegoke Osibona shi ne manajan kamfanin da ke kula da ginin mai hawa 21, kuma wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce yana inda ake ginin kafin ya zube.

Amma har zuwa yammacin Talata da ake ci gaba da aikin ceto ba a san inda ya shiga ba.

Gwamnatin Legas ta dakatar da shugaban hukumar kula da gine-gine

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da dakatar da shugaban hukumar da ke kula da gine-gine a jihar Gbolahan Oki.

Shine matakin farko a wani bangare na binciken da hukumomin za su gudanar don gano musabbabin rugujewar ginin.

Ana ci gaba da aikin ceto

Yanzu haka sojoji na ci gaba da jan ragamar yadda aikin ceton ke gudana.

A cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA aikin ya fi karfin fararen hula kawai.