Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya: EFCC ta cafke Obi Cubana kan zargin halatta kudin haram
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, a Najeriya, EFCC ta cafke fitaccen dan kasar wanda ke facaka da dukiya, Obinna Iyiegbu, da aka fi sani da Obi Cubana, kan zargin halatta kudin haram.
Rahotanni da suka karade kafafen yada labarai a Najeriya na cew a ranar Litinin ne Obi haifaffen Anambra mai wani gidan rawa ya isa shalkwatar hukumar EFCC da ke unguwar Jabi a Abuja, babban birnin kasar, domin ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa.
Duk da cewa zarge-zargen da ake yi wa Obi ba su da yawa, amma wata majiya ta ce batun halatta kudin haram da kin biyan haraji na daga cikin abubuwan da ake tuhumarsa a kai.
Majiyar ta kara da cewa, "An kama Obi Cubana ne a ranar Litinin da rana, aka kuma tasa keyarsa zuwa shalkwatar hukumar EFCC, kan wadancan zarge-zarge da na bayyana. Yana can masu tuhuma suna ligwigwita shi da tambayoyi."
Sai dai mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, bai ce uffan kan batun ba.
A watan Yuli ne sunan Obi Cubana ya yi tambari a ciki da wajen Najeriya, lokacin da ya yi gagrumin bikin binne mahaifiyarsa da ta rasu a birnin Oba da ke jihar Anambra inda aka yanka shanu 200 a wannan lokacin.
Haka kuma yadda aka dinga holen dukiyarsa da yadda yake facaka da kudi, sun sa jama'a a na shakku kan hanyar da yake samun kudi.
Fitattun mutane da 'yan siyasa daga sassa daban-daban na Najeriya ne suka yi tururuwa a bikin binne mahaifiyar Obi a watan Yulin shekarar nan.